FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Zuciyarta cike yake da son ganinshi,amma tasan kota sauko ma is of no use he seems very busy da karatunsa,bai wuce ta gaishesa ya amsata ciki ciki batare da ya kalleta bama, kuma yau batajin ma zata iya yin wani magana dashi.
Kwanciyarta kawai tayi da tunanin sa acikin ranta Kafin kace wani abu bacci mai dadi ya kwasheta,yanayin garin da iska iska yasaka ta rungume pillow a kirjinta tana kwasar minshari.

At around 11 pm taher ya sauko kasa daga shi sai vest da gajeren wandon sa white colour very clean kamar yanzu ya saka,hanyar kitchen ya nufa sabida yunwar dayake damun cikinshi altho not dat much sabida yaci abincinsa a restaurant tun dazu kafin yashigo gida,kunna wutan kitchen din yay ya wuce direct wajen coffe maker ya hada yummy coffe mai dan karan qamshi,da coffe powder kawai yay amfani dan bai iya yin komi ba,idanuwan sa ne suka sauka akan sink yanata kallon dirty dishes da wasime ta bari akan sink din wani sabon mamaki na dabaibaye shi he began to wonder how comes?ubanwa ya kunna mata gas hartay girki can sai ya lura da empty park din taliyar a dust bin snn ya fahimce cewa abincin daya siyo mata ne ta dumamashi kafadun sa ya daga ciki kyabe baki Yana kammala abunda yake yasa kai yay waje.

Dakinsa ya wuce da cup din coffen dinshi a hannun sa,harya kammala shanyewa bai dena mamakin wasime aranshi ba,he find it hard to assimilate the fact dat ta iya wasu abubuwan duba da yagama sanin dabi’ar yarintarta wani bangaren zuciyarsa kuwa yanata daubting din ko itace tay, but wani bangaren kuma yasan babu wanda zai zo ya taimaka sabida a kulle take acikin gida.

Around 12 na dare ya jawo laptop dinsa ya soma karatun sa na papr gobe which is a very important practical wanda zasuyi akan how the brain works ya kumshe cikakken ilimin sanin kowanni jijiya da hanyar jini dayake tuamali da cikin kwakwala…he needs his full concentration to study tonight.

Hakan kuwa ya faru dan karatunsa yakei babuji babu gani har wajen karfe uku na dare sann ya farajin gajiya da tsananin yunwa yanajin kamar an yashe hanjin cikinshi.
kitchen ya shiga ya dinga bude drawers yana neman abin ci yaga babu wani abu awajen da zai iya sarrafawa.
Bai iya ko kunna gas ba sai abokinsa dake hostel ya kira sukayi video call ya koyamai yadda akeyi ahaka yay kkrin tafasa farar indomie ya zuba mai da yaji ya zauna yana ci yanda kasan ya dade baici abinci ba,
Takaici ya dingaji aransa yana cewa wannan wani irin masifa ne?

Tsaki ya dingaja kafin nan ya tarkata abubuwan daya lalata ya aje matasu akan sink ya taho palo da laptop dinsa yay zamanshi yana lallatsawa nauyi yaji jikinshi na masa ya dan kwantar da kansa akan cushion yadan huta,after like 30 minutes aka fara ruwan sama kamar da bakin kwarya wata malalaciyar baccine ta sunkuce shi batare da yyi aune ba..

Sai wajajen 5:40 dot ya bude idanunshi yana kallon waje a kasale.
Sanyi sosai yake addabar sa ya rasa abunda yake masa dadi worst with all this morning erections dabaison rigimarsa inya tashi mishi dan nashi erection din da wuya yake saukowa.

Haka yay addua ya mike dashi tsaye yana jajjan guntun wandon sa kasa kasa waidan ya dena yakushin shi,a cikin sauri kamar wanda ya tsargu ya nufi dakinshi ya fada wanka,yana fitowa ya shimfida sallaya ya gabatar da fajr he cudnt make it to masjid sabida lattin da yay ga wani tsananin sanyin dake kadawa ata waje sakamakon ruwan saman da akayi cikin dare.

A fannin wasimé ma da kyar ta farka ta finciko kanta tayi kasa ta nufi toilet cikin gaggawa domin gabatar da ibadunta.

Da kyar tay sallah jikinta na rawa rawa,sanyi gaba daya yahanata sakat waje guda ta nema ta takure kanta acikin bargo tanajin dumi,ahaka ta dinga sharban baccinta kamar wanda bata da damuwar komi.

Acikin sauri taheer ya shirya kansa ya fita agidan batare da ya dubata ba,yau ko abincin ma bai samu ya siya mata ba sabida lattin dayayi,by 6:15am zasu fara exams din nd he gots only 10 min to drive to schl right now..babu bata lokaci ya isa bakin hall knowing that zuwa karfe goma haka zasu iya gamawa su fito,anan ya qudira akan zai iya satar jiki kafin su shiga paper na biyu yajeshi kasuwa yanemo mata abunda zataci yakaivnata gida snn ya dawo mkranta akan lokaci.

Wasime kuwa tun karfe takwas ta farka kuma da tsananin yunwa ta tashi ko cire nitynta batayi ba, idanunta a rufe ta nufo kasa ta shiga kitchen neman abincin da zataci.

Yau bata tsaya jin wani fargaba ba ta dauko tuwon sakwaranta na jiya
Ta kunna gas da kyar tahau dumamawa,as usual bai wani dumu ba ta sauke ta faraci ham ham bataji tsamin da miyar yay ba harsaida taci kusan rabi snn tafarajin ta koshi,tun daga nan cikinta ya soma mata ciwo ahaka dai ta mike cikin basar da shi ta danyi wanke wanke ta tsaftace kitchen din tsaf.

Mopper ta dauko tana kkrin goge kasan tiles tafarajin zuciyanta na tashi tanajin tashin hankli kamar wanda zai tayi amai..

Dakatawa tayi nadan wani lokaci kafin nan ta soma jin tsananin murdawan ciki atake takai hannunta wajen ta damke shi tana fidda numfashinta da kyar

Kan kace kobo cikin ya hargitsata yana kara murdata sosai Har kasa ta sulale ta zube kan gwiwarta batare da tayi aune ba ta kara damke ruwan cikinta..

Wani kuuuuuu cikin nata ya bada sauti Da dan banzan gudu ta mike ta haura sama tawuce toilet ta cire pants dinta a girguje ta dinga kwara zawo mai ruwa ruwa.
Kan tagama gabaki daya karfin jikinta yay kasa Koda tay kkrin mikewa tsaye awajen ta zube kan gwiwarta sabida yadda koina ajikinta yay sanyi cikinta yanakan mata ciwo sosai.

Sau biyu tana yin zawo can sann ya tsaya sai kuma Amai data dinga kwazawa kamar hanjin cikinta zasu tsiyaye.

Jikinta a mugun kasale ta fito ta kwanta sharrr akasa akan floor din dakinta tana sauke makudan numfashi idanunta suna juyawa kamar wanda ta shawu,hawayenta ne ya shiga saukowa sosai yana gangarowa daga cikin kwayar idanuwanta.
Lumshe idanunta tayi
Cikin juye juye daga nan bata kara sanin inda hanklinta yayi ba.
Na kudine kanemi naka a 300# via 0152983148 mohd sule surayya GTB 08060712446
7/25/22, 19:19 – Kawata: FR26.

Mr/mrs chef saga

Ƙarfe goma da kusan minti sha biyar taheer ya iso bakin gate, gyara parking dinsa kawai yay tundaga waje snn ya bude karamar ƙofa ya shigo cikin gida,sauri yakeyi da wani babban leda a hannun sa ya tarkato mata kayan cime cime.

Ganin koina a gidan yadau shiru yasa ya haura sama direct ya wuce dakinta, da sallama abakinsa ya turo kofar ya leƙo ciki ganinta a rigingine a kasa yasa ya aje ledan tundaga nan ya karaso kanta a hanzarce.

Tattabata yay yaga alaman kamar Babu wani kwakkwaran motsin datake iyayi,jikin ta ya mutu murus kamar wanda ta suma hatta idanuwanta batada guzarin budesu,kamshin turarensa ne kawai ya sanar da ita cewa shine akanta,tattaba kirjinta yahauyi jin tana jan numfashi ciki ciki ya sauke boyayyar ajiyar zuciya.

Yunkurin dagota yake son yi yaga ta miƙe a susuce ta soma kwaza masa amai,harta gama aman yana kallonta baice komi ba yanata lura da yanayin ta.

Batare da yace mata komai ba ya sa hannu ya sunkuce ta gaba daya ya ajeta akan gado atake ta jingina kanta da jikin bangon gadon tana fidda nishi kada kadan.

Cikin gaggawa ya juya ya shiga tattara wajen datay aman yana kimtsawa bayan ya kammala ya dauketa a hannun shi Daga nan Bai tsaya ko ina da ita ba sai dakin sa..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button