
Bai taɓa sanin cewa ashe kullum ita din ce takeyin girki ba sabida najaha ta gama lura kamar hannun wasimen ya fi nata dadi,ta dawo bata tsinana ma wasime komi sai aukin comanding dinta daga tace suyi kaza saitace suyi kaza itadai master ce wajen kawo suggestion intayi ne ta dan tayata wanke wanke ko shara
Itako wasime abun baiya ko damunta sai da akaci kusan sati guda harda yan kwanaki snn ta soma shaƙar abubuwan da najaha take kullawa akanta
Gata da shegen rike abu acikin ranta,daga kan karyan da najaha takeyi agaban yayanta ta somajin haushi haushin ta musammn ma ayanzu dataga taheer ya dan soma sake fuskarshi kadan kadan da najaha har yana amsa maganarta,yana tambayan ta abubuwan da babu agidan ita kam abun nema ne ya samu nan danan ta soma fidda wasu makirtaccun halaye wa wasime
tsaban rawan kai Wasu maganganun ma bata sanin ta furta mata
Yau daga tace ita ce boss din gida,sai ta soma acting kamar itace ma matarsa, ga son bada oder akan abunda za’a masa kamar itace kadai mai iko dashi .ran wasime tuni ya soma baci da hakan…wani bin intana mata haka sai ta hade rai Tace mata ta tafi gida,tana ganin wasime ta hade rai Atake atake saita sauko tahau washe baki sai tace ai wasa ita take mata.Musamman ma akan kalman datake yawan furtawa nace wa itace uwargidan gidan lokaci ne kawai ake jira ta shigo,har wani ce ma wasime kanwata ta somayi, sosai wasime ta tsani wannan rahar ta ta kullum intanayi bata sake mata fuska sai ta hade ranta tace ita batason wannan wasar amma duk da haka najaha bata ko saka ranar denawa ba
Infact kowani rana tazo da sabuwar kisisinn datake zuwa dashi abun yabi ya ishe wasime sosai ta soma jin haushin ta.
hakan yasaka ta fara takurata dan tana koya mata abubuwan daya rage wanda bata iya ba, haka zasuyi ta girki ko bazasuci ba saita make sure takurata ta dan ta nuna mata yadda akeyi wasu ababen..
ahaka ahaka harta ta dan iya sarrafa abubuwa kala kala dakanta gashi yanzu hannunta ya soma mikewa sosai akan girka abinci dake abinma baiwace ajikiin maishi harta fi najhar iya sarrafa wasu abubuwan
Duk rintsi dai tanason kawancen ta da najaha
Amma karyan datakeyi agaban taheer yasa ta somajin tsanarta aranta,
ayanzu batada wani buri face taga ta gama koyan wasu abubuwan data saka agaba domin ta rabu da najaha
Sosai najaha take kkri wajen juya mind din taheer akan wasime
haka wata rana zaina gatsala mata magana aganinsa tafiye sakalcin da son jiki taki ta tsaya ta koyi komi awajen najaha.
Saida abun yafara zafanta,ya soma ci mata tuwo a kwarya sann ta zo ta dena ganin laifinsa ta fara kallon me najaha takeyi haryasa yayanta’
Yake yawan mata fada yana mata kallon sakaltaccya wanda bata iya komi ba…
Ranar haka ta shirya tsaf ta fito fuskanta ba a sake ba dan bata ko dariya
Samu tay har Najaha ta goga wasanta akan taheer ta amshe kudi mai yawa wai zasu sayi spices na abinci yana bata kuwa taje har kasuwa ita kadai ta sisisiyo abubuwan ta dawo
Yanzu kam ma direct take shiga kitchen tay abunda take so,sai in wasimen ta zago kawai saita ganta gatsau aciki tana abubuwan ta kamar wani gidan mijinta
,yauma kusan abinda ya faru kenan,najaha tana dawowa daga kasuwa bata tsaya neman wasime ba ta wuce kitchen tahau jejjera kayayyakin data siyo…
Daga kofar kitchen din ta tsaya tana kallon ta, wani uban tsawa ta daka mata tana cewa”………..
Na kudi ne,300₦ via 0152983148..GTB
08060712446.
7/25/22, 19:19 – Kawata: SURAYYAHMS#FR36.
Desperate13:busted
“me zan gani haka najaha?ubanme kikeyi min anan..
Arazane najaha ta juyo tare da miÆ™ewa tsaye adan daburce tana cewa..babu,babu,saikuma ta dan dakata taja numfashi “kai wasime meye zaki wani dakamin tsawa kamar wata yarki mtss ji harkin wani tsorata ni.
Fuska a matukar dore wasime ta hantsalo cikin kitchen din suka tsaya gaba da gaba suna kallon juna, wani dan uban harara takebin najaha dashi daga sama har kasa tanai musu kallon debar albarka daga ita har kayan girkin dataje ta sissiyo.
A dake cikin harara tace
“Yaushe kikaxo gidan nan bansani ba, kuma uban Meye wannan kika kawo nan?uban waye ya baki izini ?
Wani rolling idanu najaha tayi a makirce cikin kadadi da rigima shareta tay tanamai bata keya kamar ma bada ita takeyi ba,sai can acikin shan qamshi ta juyo,murya ciki ciki tace”As u can see,shoping najeyi na abunda zamuci yau agidan…”kinma san abunda zaki dafa kuwa?
Zonan ta jawo hannunta ta kawota har gaban ababen data siyo snn tace “look carefully,tana fadin haka ta jawo kayayyakin data siyo ta ajesu agabanta tahau nuna matasu one by one tana cewa wannan ledar kayan hada cole slaw ne,wann kuma nikakken nama zakiyi masa meat balls dinki mai shegen dadin nan,snn pasta italiano zakiyi shine as main meal da dan tuna fish sauce inkin gama gabaki daya saikiyi ganishing din abincin da meat balls din..
Dama so nake in shishhriya miki su kafin sai inje na kiraki kizo kifara yin aikin ki yanzu,And yes,lest i forget dan Allah wasime kidaure kina dan rage barkwano wallh Jiya bakiga yadda yaya na yakeyi da bakinsa ba ne wai Kashe shi zakiy ne?
Tana maganan ne with confidence irin ta samu wajen nan, tanawani kadadi da yanga tana giggila kai kamar itace oga madam din gidan gabaki daya.
wasime dake kallon ta da mamaki bata san lokacin da idanunta sukayi wani ja ba, ranta gabaki daya ya hargitsa ya baci,wani irin Runtse idanunta tay tare da dunkule hannayenta da suke mata kaikayi duk jikinta na rawa zuciyarta na mugun tafarfasa da kyar ma ta bude rikitattun idanunta ta saukesu akan najaha
Karkada kafafun ta tahauyi Cikin tsananin jin haushi snn ta daka mata tsawa”tace ke najaha wai intambayeki ni yar aikin ki ne…gwalo ido waje najaha tay ni yaushe nace miki haka..
bata gama rufe bakinta ba taji an wani cakomu wuyarta an shaketa cewa take amsa zaki bani jaka makaryaciya Yaushe kika dauke ni aiki a gidan nan da zakina bani dokoki??ko nan gidan ubanki ne da zaki wani xo kina mana mulki ga wani dan iskan karyan da kika samu sarar gundumawa wa yayana akaina najaya ashe ke babban munafuka ce kullum sai inyi girki kice inbaki zaki kai ashe karya kikeyi munafurta na kawai kikeyi..kinsa yaya na yanamin kallon wata shashasha.
matsiyaciya kawai ince kinayi ne don yana baki kudi?ai bantaɓa sanin bara da roko yakawo ki gidanmu ba,dan tsabar rashin kunya gida banaki ba harda karban kudin cefane waike gaki sarauniyar sanin hanyar kasuwa ko, hamshakiya me yimana jefanen gida.kin wani maidamu yan iska toh wallh baki isa ba,nafi karfin makircin ki,yau din nan karyan ki zai ƙare kuma saina tona miki asiri babban munafuka kawai.
Bude baki Najaha tay idanunta har sunyi jaa zatay magana wasime ta wani turmusa wuyanta yanayinta a mugun zafafe fixgo hannunta tayi a walakance tana mai tunkuduta kamar wata yar akuya takai ta har waje can bakin gate sann suka tsaya kowannen su na huci suna kallon juna.
“Wasime meyayi zafi?
Najaha ta furta hakan muryan ta na rawa idanunta cike taff da hawaye
A fusace wasime ta hau karkada kafafunta da sigar rashin mutunci da dabanci,bala’i da masiface zalla a cikin kwayar idanunta
tace ince dai waje na kikezuwa kuma dama ni na bukaci hakan,dan haka yau na sallameki karki Æ™ara zuwa wajena kije can gidanku kicigaba da makircin da karyanki anan,snn ki tarkata mulkinki kije kibaza ma tsohuwarki a gida amma ba anan ba…get out and dont ever come back…ta kara turata can waje a mugun fusace tunkan najaha ta bude baki tay wani magana har wasime ta hargitsa ta rufe kofar gate dinsu gararau ta danna masa lock ta ciki kamar wata mahaukaciya