FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Adan tsorace ta dago ta kallesa,muryanta na rawa tace “yaya Nifa ban mata kome ba.

Jin yay shiru yasa itama tay shiru abunta,,tagama lura dashi,da alaman kamar ransa na É“acine da yanayin yadda take bashi amsa,hakan yasa ta dan saki muryanta dake rawa rawa tana turo baki tace'”toh ba itace ta kawo shayin, shine kawai nace mata taje gidansu bafa wani abinda ya faru..

ciza labbansa yay yana kallonta yanajin kamar ya shaketa,daurewa yay..’yace toh Akan me zaki koreta?saboda kawai ta kawomin shayin ne ko akwai wani abunda ya hada ku?

Tace “A’a ai sugar ta zuba maka mai yawa kuma saida nagaya mata bakashan sugar sosai mesa zata saka

Idanunshi ya rintse yana jin haushin karyan datake masa,ransa a bace yace “kimin shiru ure lying,ba abinda ya faru ba kenan,
Kigayamin gaskiya in ba haka ba zangane cewa kece kika zubamin sugar a shayina ba najaha ba

Shiru tayi tana kallon kasa..zucyarta kamr zai ballo yay tsalle ya fice waje tsabar tsoro.

A dan tsawace yace mata “Answear me,kece kika saka min sugar ko a’a?

Wani Tsorataccen Kuka ta fashe mishi da shi tanayinsa ahankli cikin muryan kuka Tace yaya Nifa,nifa, nifa….
yaya ai duk itace ta jawo

Yace Oh wow, ashe kece kika munafurceta kika zuba sugar danki koreta agidan nan kenan ko?are u stupid?wato danayi miki fada jiya shine bari yau kinunamin cewa ban isa dake ba right,wasime wannan wani irin bakin hali ne,ashe ke munafukace waye ya koyamiki wannn
Banzar dabi’ar?

Ji tay maganan tasa ya cakketa a zuciya Cikin kuka tace Yaya dan Allah ka tsaya kaji zan fadama gaskiya

Ransa abace Yace Bazan tsaya injiki ba..ive head enough of ur nonsense wasimé,kinbani mamaki
Wallh.im highly dissapointed in you kika kara memeta makamancin wannan halin arayuwarki ki rubuta ki aje saina miki shegen duka na kakkaryaki…

Kanta na kasa tanata kuka har cikin zcyarta tanajin bata kyauta datay hakan ba sam,kuka take at same time feeling disgusted about her action, ita kanta tasan zuciyace kawai ya debeta ta zuba sugar nan amma badan son rantaba…bata san meye munafurci ba,bata taba karya ma wani ba,najahr ce kawai ta Æ™ureta harta tunzira takejin saita rama kafin nan zata samu kwancyar hankli amma bawai dan hakan datay halayyarta bane

Kanta na kasa tana kuka cikin rasa me zata ce can ta dago ta kallesa tace

“Yaya mesa bazaka saurareni in fada ma gaskiya ba, yanzu saika bugeni akan najaha?ai ita din ma babbar munafuka ce..ba ita bace kullum inta zo sai ta rinka munafirta na tana gilla maka karya akaina.
Ai cewa take wai zaka aureta ita ma matarka ce.Innayi abincina saita daukemin ta kawo maka kuma ai bata fadama gaskiya kullum,najaha babbar makaryaciya sai tace maka wai ita takeyi dan kawai ta munafurci ni ta shafamin kashin kaza awajen ka.

yaya wallahi karya take yi maka bata aikin komi Ai abinci nane duka take kawo maka kanaci..jiya nace mata ta rabu dani kartazo… shine yau zatazo bansani ba hartaje tayi maka tea ta kawo ?yaya najaha babbar makira ce munafuka itama ai saika mata shegen duka indagske kakeyi.

Tsawa ya daka mata yana cewa kimin shuru
Not another words frm u
Shirun tay tanajinshi
Yace makaryaciya kawai
Harke kinsan ki lalata ma wani abunsa a makirce sabida wuyarki ya riƙa yay kauri ko,To kenan wata rana haka zaki kasheni da haukar munafurcinki
…datake miki hakan meyasa baki zo kingaya mun ba tun farko ai duk abunda ya faru dake laifinki ne..

Cikin kuka tace yaya ai kaine baka saurarata
Saunawa nake son ingaya maka kullum sai fada kake min wai ban iya komi ba…

Yace toh aisai kiyi hkri,da ubanwaye ya kawota gidan nan inba ke ba..Wasimé I wll not tolerate lies nd deceit from u ..tun muna shaida juna dake ki canza wannan hali,snn ki wuce kije yanzun ki gaya mata cewa kece kikayi abun nan kafin na tattaki anan wajen..Bazaki taba kawomin wannan halin gidana ba kinaji na ko?
Get up nd go bfore i sound u,Da ihu ya karasa
Mata maganan

Kuka ta fashe da shi na fitan hankli tanajin zafin sunayen daya kikkirata dashi musamman ma munafuka makaryaciya dayace..ji take badadan shi yayanta bane da wallahy saita rafka masa cizo da yakushi mai zafi

Gani take ai ba laifinta bane ita kadai,kullum najaha tana nata munafurcin ba’a mata komi dan yau kawai
Itama tay nata sau daya shikenan sai akwashe duka laifukana dora mata?acikin zcyarta tace,gaskiya hakan bazai taba yuwa ba..inde zata bawa najaha hakri toh saidai in itama najahar zata toni asirin kanta sann ta fadi gaskiyar me take mata kowama yaji snn abata hkri.

A zuciye ta mike tana share hawayenta,duk dama tana matukar jin tsoro amma hakan bai hanata tsayawa agaban da ba,tana kuka tace ni fa ba inda zanje..ni banzanje ko ina ba…ai itace mai laifi bani ba..in bazata ban hakuri ba nima baza taÉ“a bata ba.

Idanunsa ya kankance akanta snn Yace wht?
Kikace mene?

Tsuke bakinta tay tana turoshi gaba hawaye na kin dena tsilalo mata acikin idanunta
Cikin muryan kuka tace “yaa fa wannan ba adalci bane,mesa zakace nice zanje na bawa najaha hakuri,ai ita ta fara munafurta ta,da batamin ba da nima bazan mata.
Dan kawai tana kawo maka abinci shine zaka wani bi bayanta..nide wallh babu inda zanje saidai a kasheni amma wallhy bazan ba najaha hakuri ba

Kafin tagama rufe bakinta taji saukar Wani wawan mari akan fuskanta, xubewa kasa tay arazane ta fasa wani irin rikitaccen ihu dafe da kuncinta tace wayyo Allah na na higga uku,a take Yahau kanta da masifa har yana diri dan bakaramin baci ransa yay akan taurin kan datake nuna masa ba, cikin ihu da tsawa yake cewa “Are u stupid… ina wasa dake ne da zakicemin haka wato ban isa ince miki kiyi abu kiyi bako? to maza kiwuce yanzun nan kije gidansu ki aikata abunda na fada miki yanzun nan, ya fatattake

Kin motsawa tay ta kife kanta akasa tanata kuka game da turjewa, sam taki ta tashi ta aikata abunda ya umarcetan

Kuka kawai takeyi kamar wanda ranta zai fita

hannunta ta ya ja zai mikar da ita cikin bori ta firgita ta turesa ta fizge hannunta cikin zuciya da taurin kai

Zai sake fizgota tay sauri taja da baya,yabita ya capko hannunta,kokawa ta somayi dashi tafara cewa”Nika sakeni ni kasakeni,yaya baka gani ne,aruwan sama fa za’ayi aruwan ne zanje inbata hkri yanzu,.. ni wallh bazanje ba…ni tsoro nakeji ai gidan su nada nisa nide bazan ce gidansu munafukan can ruwa ya daka ni ba,Ai itama babbar munafukace mesa toh baxaka ce taban hakuri ba saika mareni kuma kace inje inbata hkri…fincike hannunta anashi tay da karfi taja can nesa ta rakube da jikin bango tana kuka arikice, daga can yake kallonta muryan sa a hatsale yace “innazo wajen nakamaki Zan kara wnka miki wani marin, dont allow me to get der.. Kifiita nace miki kije kibata hakuri

Tsawar daya daka mata yasata ficewa a dakin agigice tana rusa kuka ihunta duk ya karade gidan.

Tsaye yay turus a tsakiyar dakin Yanajin kukan nata wani Lumshe idanunsa yay yana daga tsaye,shi kwata kwara ba lamarin najaha bane ya addabesa aransa,abunda ta aikata ne na makirci ya tunzirashi ya bakanta masa ransa sosai.

He love her soo much shiyasa baiy tsammanin ganin wani faults a halayyrta ba.

Ya zabi ya runtse idanunsa ne akan laifukan najaha just so dat he can purnish her akan abunda ta aikata
Cos He doesnt want his beloveth wife to posses this evil quality.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button