FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kallon yadda ta birkice numfashinta yakeyin sama sama kawai yakei

Kan yace zaiyi wani abu jikin wasime har ya fara ragwabewa, kamar wacce dama jiransa take ya dan taba ta..yana kawo hannunsa jikinta ta firgita ta dauke numfashin ta,wani irin jan zuciyarta sama tay atake tayi luiii tay colapsing, with full force ciwon asthmanta ya tashi tafara numfashi mai matukar karfi da gigitarwa……
Na kudine 300₦ via 0152983148 GTB 08060712446….
7/25/22, 19:19 – Kawata: #SURAYYAHMSFR39.
Better path:my first nd last decison!.

Na kudine 08060712446…

Jin sauÆ™ar marinta akan fuskan sa yasashi yay wani irin runtse idanun sa,atake kuma ya budesu ya zuba raunatacun kwayar idanun sa akanta yanata kallonta da fuskar mamaki ayayin da ta sunkuyar da kanta can Æ™asa tana famar fidda wani sassanyar kuka marar kara…

Wani mummunan tsoro ne ya dabaibayeta duk jikinta na rawa kar kar kamar mazari duk sai ta rasa yadda zata aje kanta tsabar yadda kirjinta yake bugu

magana yay mata acikin tausashiyar murya mai sanyi sabida baison ya mata tsawa balle ya Æ™ara jefata acikin wani mummunan halin irinta dazu Yace “wasimé marina fa kikayi..?

A tsorace ta dago ta kalleshi hawaye taf idanunta jikinta na rawa sosai ta kara fashewa da wani matsanancin kuka.

Bata iya amsa shi ba
Gudun karta amsashin yace zai rama marinsa
Tsoron dukansa takeyi itakanta ayanzu bazata iya tantace abunda yasata ta mareshin ba

Batasan daga ina ta samu wann karfin gwiwar ba,data mareshin saitaji kamar an dawo da itane cikin hayyacinta.

shanyewa yay cikin karkada kansa bainuna yawani damu ba.

matsowa yay kusa da ita yazauka daf da niyyar kara lallanshin ta,yana taɓata ta firgita tafara kai masa hatsallen duka akan kirjinshi shiru yay ya barta harta gaji ta dena dukanshi tayi shiru
A sulale ta koma baya ta sauke kanta ajikin kujera
Gameda kife fuskrta awajen tanata kuka sosai.

Yanata kallonta shide baisan wani irin zazzafar zuciya da kishin tsiya Allah ya bawa wasime ba…shiduk a tsorace yake da yanayin jikinta shiyasa bazai taÉ“a iya mata komi ba face yabita da lallami da lallashi.

kukan ma da yasan yadda zaiyi ta dena da tuni yay mata hakan dan harynzu baimanta da kalar wahalan datasha da ciwonta ya tashi dazu ba…

Hannunshi ya ziraro ta bayanta abaxata,firgita tay dan Bata san sanda zuciyarta ya daka wani tsalle zaiyo waje ba ayayin da taji ya tabata a hankli cikin tattausar yanayi mai kashe lakar jiki yana shafa mata gadon bayanta acikin sigar lallami da rarrashi

Ji tayi kamar ma ta rude
,magana yake mata da wani irin sassanyar murya wanda daga ita sai shi kawai suke iyajin meyake furtawa abakin nashi,kwayar idanunta yake kalla Yace “I knw i was wrong to slap u nd send u away a cikin ruwan nan But am sorry”!…yadda yay maganan yasa taji wani sanyi na ziyartan zuciyan ta,tana ta kallon kwayar idanun nasa koda zataga wani alaman karya aciki sai bataga alaman hakan ba, duk da haka batafasa kukanta ba dan duk sanda ta tuno da maganganun najaha akanshi saitaji kamar wuta a ke hurawa akan kirjinta, daf da ita ya zauna a Æ™asa game da nannade kafafuwan sa snn ya dafa kafaduna kadan cike da kulawa yace
“kinga baki da lpya yanzu
Muje ciki man ki kwanta
I promise you inkin tashi a baccinki zamuyi magana ko?…

sassanyar muryan nashi dayasa yana bala’in ratsa mata zuciya,Gaba daya saita ji ta firgita dan tay tunanin data mareshin hala zai mata mummunan duka ne ya ya tattaka ta.

ganin duk abunda tay masa bai mata komi ba yasata ta dingajin rudani acikin kwakwalwanta

Wani abu ta dingaji acikin ranta mai kama da tausayi tausayin shi, jin yadda yake mata magana da tausashiyar muryansa da yadda ya saukar mata da kanshi yana lallabata,hakan yasata ta dingajin wani kasalar na dirar mata tanajin kamar ba ita bace take aikata masa dukkan wayannan rashin da’ar.

..hanun sa ya kawo kusa da ita kamar zaijawota jikinshi, firgita tay ta dago kanta tana kall’lon fuskarshi a tsorace.

Hawaye tafara sauke masa mai sanyi

Acikin rudani muryanta ma rawa tace yaya dan Allah Ka kyaleni nayi tafiyata ta,nifa babu ruwanka dani yo mai ruwanka dani?Yaya baka so na..ni inda ake sona zan koma acan kauyen mu…yo Akan najaha saika dinga marina?yaa banfa taba maka karya ba, ai kasan ba halina bane,. kuma Nima banso na mata haka ba ai itace take munafurta ta kuma kaima kaki ka fahimci hakan sai bin bayanta kakeyi,hmmm ai yanzu na ganoka..kaima ai
Sonta kakeyi ba har tace min wai zaka aureta ba?kara fashewa da kuka tay ta rufe idonta tanajin tsananin kishinsa a zuciyartaa musamman ma data furta masa hakan,acikin kukan tace “Toh ai sai Kaje ka same najaharka kuzauna tare amma ba dani ba,ai ni ba matarka bace ai itace matarka..Gaskiya ni tafiyata kawai zanyi bazan iya zama da munafuka irinta ba..
Kaima ai watarana saita maka munafurcin kuma ni wallhy babu ruwana.
..bakana bin bayanta ba?
Maganan nata cike da yaranta takarashe shi.

shiru kawai yay ya nitsu yana jinta har tagama fadar duk abunda zata faÉ—a cikin shagwababben kuka..
Hmmm kawai yace ya karkada kansa yay shiru nadan wani sekanni..
daga bisani Ajiyar zuciya ya sauƙe Baice mata komi akan zancentan ba,can saiya miƙe tsaye game da miƙa mata hannu yana jira ta taho gareshi.

Kallonshi ta tsayayi with mixed feelings akan fuskanta,gabaki daya idanunta ya kumbura ya sauya mata kamanni sabida tsabar kukan dataci..da wani sexy voice ya kanne ido akanta yace comon zo mana, ni babu abunda zan miki daki kawai zamu tafi kinga babu wani kaya ajikinki ko so kike wani wanda ba muharraminki ba yazo ya kalleki ahakan?

..shiru tay batace cemishi komi ba,ajiyar zuciya ta sauke kamar wata maijin tsoro tsoron sa,a hakan dai ta daure ta mika masa hannun nata ahankli ya dagota ta mike tsaye,gaba da gaba suka tsaya suna kallon juna,a hnkli ya shafa gefen fuskrta ta lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya mai sanyi, jawota yy jikinshi ya dan lafar da kanta akan kirjinshi nashi tay wani lamooo,kansa yay resting kadan ata gefen wuyarta yana sauÆ™e mata numfashin sa mai dumi da kuma nakasarwa,da muryansa dake fita da wani irin kasala yace mata “kinyi sallah?..kafin ta amsa ya jawo hannunta yana kallonta yace c’mon muje ciki kiyi sallanki kinga lokaci yaja sosai bakyau yin sallah a makare.
Koyau bazakiy salla bane dan kawai kina fushi na mareki?turo bakinta tay gaba Batace mishi
Komi ba ta sunkiyar da kanta kasa,janta yay suka haura sama dakinta

Yana tsaye hartaje tay alwala tazo ta gabatar da sallan azahar…tana idarwa lkcin bata tashi awajen ba tana kan zaune akan Sallayarta can taji kirjinta na mata zafi zafi numfashin ta yana kkkrin daukewa…

Kamar da wasa ta Riƙe wajen tanajin wani iri wani iri,sai kuma ta fara gasping ahankli kan kace kobo har tafara tari mai tsananin karfi da kara..

Kamar yadda yay dazu haka yanzuma yay,da gaggawa ya karaso wajenta ya sunkuceta suka koma dakinshi ya ajeta akan gadonsa yajuya ya dauko inhaler ta ya bata ta zuƙa.
Daga haka ta bingire da wani wahalliyar bacci….

Time to time haka sai yaga ta firgita ta tashi,haka asthman zai sake dawowa ya kuma kwantar mata dashi
Daga ta runtsa kadan sai ciwon ya kara dawowa haka suka dingayi gabaki daya ta daga masa hanklin sa sosai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button