FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SURAYYAHMSFR41
Better path saga:bygones

Na Kudine 08060712446

Ahankli wasimê ta fito tana tafiyarta da sanyin jiki kirjinta na bugawa fat fat kamar zai fito waje.

takawa take kamar wacce batada jini a jikinta tana jajjan kafafun ta akasa tana saiɓi saiɓi kamar wata wacce bazata iya isa gareshi ba haka tadinga ji acikin zuciyarta.

Langwame wuyarta tay data hango sa acan shikadai yana zaune,waje idanuwanta suka firfito wanda ahalin yanzu har sunyi ciki ciki kwayar idanun nata sunyi wani sanyi da kuma alaman bugun zucya atattare da ita..

Sassanyar tafiya take tanata sake sake acikin ranta ayayin da kanta yafara mata juyi tanajin brain dinta a rude tsabar tunanin abubuwan da zataje gabanshi ta fada mishi wanda haryanzu bata sansu ba.

A Cikin sanÉ—a da sanyin jiki har ta iso cikin falon ta tsaya tay shiru ata bayansa tana ta kallon bayan keyarsa batace komi ba,wani wuri wuri takeyi da idanunta dan ko numfashinta batason yaji bare motsinta dan har iyanzu bata san me zata fara cemasa ba.

Rawa rawa jikinta ya dingayi hawayen fargaba cike da kwayar idanunta
Wanda basu samu daman saukowa ba tukuna,maganganun biltine suka dinga dawo mata cikin zcyarta ta tuna masifar data mata akan dolenta ne saita bashi hkri, dadin karawa da tace mata in batayi hakan ba taheer zaije ya karo aure halama ya auro mata najaha suna zaman gidan tare…

Lumshe idanunta tay cikin zuciyarta tace Allah ya kiyaye mini in zauna da makaryaciya kamar najaha..wallh bata isa ba ainice kadai matarsa..
Tagama masifarta tasss acikin zuciyarta ita kadai sai huci takeyi tana tumbatsa dan bakaramin saka damuwar najaha tay aranta ba,har bata sani ba garin sauke bala’in datakeyi acikin ranta wani tukikin tsaki ne ya kufce mata mai dan Æ™arfi wanda ya saka taheer saurin juyowa ta baya saiya kalleta tana tsaye

Suna hade ido yaga ta toshe bakinta ta da mugun sauri,kallonshi takey da fargaba ayanayinta gaba daya taga ya sauya mata ya zamo tamkar bashi ba, a iya saninta dai dazu da safe jallabiya tagansa yanzu kuma sai taganshi da wani kayan nadaban.

Ganin yanata kallonta yasa ta sauƙe kanta kasa ahankli tafara fidgeting fingers dinta tana wani sum sum uwa warce aka kamata da cikin shege haka tay da yanayin expression din fuskarta

Taheer Baice mata komi ba banda kada kansa dayay ganin ta sakamai riga,saiyaga kamar ma rigar yafita mata kyau ajikinta cos she looks sexy bana wasa ba,dan kyabe bakinsa yayy snn ya dauƙe kansa akanta ya juya ya cigaba da danne dannen sa a laptop dinsa bai kara kulata ba.

Wasime dakejin tsananin fargaba, tsaye tay awajen batayin ko motsi.,ahaka saida taci kusan mintina uku tana tsaye akansa kanta kallon kasa tana kuma murmurda yatsun hannayenta cikin juna,gaba daya yanayin ta ya sauya ya koma na tsoro,ga uban tunani data dora ma zcyarta na abubuwan dazata fada masa wanda suke sakama zuciyarta jin nauyi da kuma damuwa,

kanta a sunkuye sosai tana famar kallon kasar tiles din falon,gabaki daya bata san sanda idonta ya ciko da hawaye ba gani kawai tayi har ya fara zilalowa kasa…ita ganin hawayen kawai tayi suna diddiga akan tiles amma bawai danta shiryayin kuka ba,tursasa kanta tashigayi don ta samu ta nitsu koda zata samu kwarin gwiwar fuskntar sa..tasan dai Yanzu lokc bazai wuce karfe 7:30 ba ai gwara tay marmaza taje gabanshin tunkan yace zai tafi makaranta ya kyaleta.

data raya hakan acikin ranta sai kuma shedan yy sauri ya fara kitsa mata mugayen tunani yana cewa inhar tabari taheer yaje schl hala daga nan kuma shikenan zai biya ta gidansu najaha yasameta harta bashi hakri suyi soyayyarsu sai ita yabarta anan a tutar babu, kamar lkcin da bilti tagayamata cewa in bata bashi hrkri ba za’a kwace mata shi awani wajen haka ma yanzu taji dirar wani mummunan tashin hankli yana neman mamayeta,….

Bugawa zuciyarta yafarayi da tsananin karfi numfashinta ya soma sauya salonshi izuwa zallan madaran ruwan kishi,jan ajiyar zuciya tay cikin dauriya ta taho ta gabansa tana takawa a hankli harta iso ta gabansa taja ta tsaya

Taheer na kallon screen din system dinshi bai dago kansa ba, da gefen idonshi ya kalleta a sace snn ya harde fuskansa yy kamar baiji tahowartan ba.

Sunkuyar da kanta tay cikin sarÆ™ewar murya tace ” yaya…shiru tay jin bai amsata ba..

Sulalewa tay har kasa ahnkli Tace “yaya ina kwana?..”lpya” yace mata atakaice batare da ya kalleta ba idanunshi stiff akan abunda yakeyi.

Sai can da yadan numfasa cikin yanayin ko inkula yace “ya jikin ki…yunwa kikeji ko?Bata amsashi ba tana ta kallon yanayin sa ganin ko kallon inda take baiyayi maganan sa kawai yake kamar da iska ba da mutum ba.

muryansa kasa kasa yace”im busy right now pls try nd make tea for urself kafin infita zanje na siyo miki abinci.

shiru tay bata amsa shi ba,shima sai yay shiru, kanta tadan sauke a kasa yanayin jikinta ya sauya gaba daya ta rasa mema zata soma cewa..”hawayen bazata ne ya sauko mata ta saka hannunta ta share snn ta tashi tsaye jiknta a sanyeye,binta da kallo harta wuce kitchen ta hada musu shayinsu a tare snn ta kawo masa nashi gaban sa…still taga ko daga kai ya kalla baiyi ba bare yace zai sha, gaba daya sai taji tafara rasa nitsuwarta awajen..

Zama tay dirshan a ƙasa da cup din shayin nata a hannu, yanata danne dannen sa har kusan mintina goma taga baiko kalle tea dinta ba barema ya dauƙa ya sha.

A lokcin sabbin hawaye ne suka harzuko suka cikke kwayar idanunta haka kawai gabanta ya dinga fadi ta riƙe nata shayin a hannu tsawon mintinan nan itama bata iya kaiwa kofin bakinta ba, Gabadaya yanayinta ya sauya ya zamto na kunci da damuwa.

Hmm kawai taheer yace acikin ransa yana lura da ita Tare da rufe system dinsa ya firzan da iska ta bakin shi yana mai danne rashin jin dadinsa saboda ya fahimci danyen kan yarinta na debarta uwa uba ga kuma tauron kai da shegen son fitina data dasawa ranta.

Yana kallo ta ajiye nata shayin a hankli idanunta cike da sauƙe boyayyr hawaye.,kasan ransa yanajin duk babu wani dadi, acikin son boye yar damuwarsa ta da haifar masa arai ya juya kadan ya tambayeta yace
“Meke damunki?
Cikin dauriya idanunta na kallon kasa saida danja lokaci snn Tace mishi babu komi,tana furta hakan muryan ta ya fara rawa rawa, cikin sautin kuka ahankli cikin sanyin murya tace yaya yaa naga bakasha tea din ba?Wani takaitacciyar amsa ya bata cikin sautin da kai kace dole aka masa ya amsa yace “no na koshi ne..jin hakan yasa ta daga rikitattun idanunta ta kallesa zuciyarta a mugun dagule da baÆ™ar kishi.

Tashi tay cikin fushi tay kamar zata bar wajen ya jawo hannunta ya dawo da ita baya,Kaman jiran hakan take suna hade ta saka hannu akan fuskarta ta rufe tare da fashewa mishi da kuka.

Sake mata hannunta yy yana kallonta da mamakin yadda kukan banza sam baiya mata wuya..

Lokcin wani zuciyace yake tunzirata akan tay abunda ya kawota,a Cikin hanzari da sanyin jiki ta sulale kasa daidai kan kafarsa tay kneeling kanta na ƙasa cikin kuka
Mai ban tausayi tace

“yaya toh mesa bazaka sha shayin ba?ko dan nay maka laifi ne…yaya dan Allah kaya hakuri na tuba bazan kara ba…”ta karashe maganan cikin matsanancin kuka..

Shikam Gabansa ma yake kalla baice mata komi ba..
kara marairacewa tay cikin kuka tana cewa “nasan nay kuskure dayawa Dan Allah kayafemini saboda Allah..inka yafemini kaima Allah zai yafe maka abubuwan da kamini akan najaha.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button