FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Faduwa gaban najaha ya dingayi tanajin wasime da wani irin tsinananen tsoro da fargaba,cike da karfin hali tace “yaya wallhy karya take min..

Ke wasime bakiga laifin kanki da kika munafurceni kika zubamin sugar a shayi na basa ya sha ba sai nawa ne ya tsole miki ido

Cikin harara Wasime tace
Eh eh naki zan gani makaryaciya..gwara ni ai nafada masa gaskiya amma kefa?haryanzun ma rantsuwa kike masa akan wani karyan..

Cikin katse su Taheer yace ya isa haka!!
Acikinsu kowacce taja tay shiru..daga can ya dubi najaha yace ke ki fadamin gaskiyar inba haka ba nasan inda zan kaiki a casamin ke yau…
Ashe ke munafukace?ni sa’arki da zakimun Æ™arya?

Take zuciyar najaha ya tsinke yana bada wani sauti mai tsananin bugawa idanunta sun cikka da ruwan hawaye

wani tsawa ya daka mata saida ta razana ta koma da baya,kallon shi take a razane yana cewa “bazaki fada min gaskiyar bako?wasime jeki dauko min bindigana…wasime ta juya fuuuu kamar dagaske zataje ta dauko bindigar,aikuwa da mugun gudu kuma a birkice najaha ta taho taa capketa,wani irin matsanancin kuka ta fashe dashi,wasime ta hankadeta cikin fusata tanacewa nikan ki dena taÉ“ani wallh sai in sharara miki mari anan wajen.

Najaha data gama tsorata kuka ta fashe dashi tana cewa toh kibari karki je wallahy zan fadi gaskiya…

Jawota baya taheer yay a walakance ya dangwala ta cikin zare mata ido yace “Ke ina wasa dake ne?…shiru tay ya watsa mata wata mari wanda yasata kaiwa kasa a mugun daburce ta shiga girgiza kanta tana cewa a’ah a’ah zan fadi gaskiya

harÉ—e ransa yay yace toh me kike jira,kifada karki boyemin komi …

Kuka ta dingayi cikin rasa yadda zata soma tona asirin kanta kawai saita soma bashi hakuri cikin matsanacin kuka tana marairace masa fuska sosai..

Yayan wasime kay hakuri bazan kara ba…

…”ganin zata kara bata masa lokaci ya juya yace ma wasime je ki kawo min bulala…nan da nan wasime ta juya tana barin wajen najaha ta rikirkito kan kafarsa ta kama tana kuka mai rikitarwa

Yaya yaya dan Allah karka bugeni ka tsaya kaji wallahy zan fada maka gaskiya.

Nan ta soma gaya masa irin son datake mishi da duk wani makircin data dinga kullawa akan wasime tana cewa sharrin shedan ne..

Mamaki ne ya dada rufe fuskan taheer jin tana cewa mamanta ne take kitsa mata hakan dan kawai ya kulata..

Tana cikin confessing saiga wasimé ta sauko da wani zugegen wayar wuta ta ja tsaya tace yaya wani karya ta karayi maka ainasan duka gaskiyarta in karya ta maka ni zangane …kafin taher ya amsa caraf najaha ta amshe maganan abakinsa cikin yanayin jin mummunan tsoro da firgita,a daburce tace “ke nifa ban masa wani karya ba duka gaskiyar na gaya masa kinji na rantse miki da Allah…yaya na wallhy ina sonka…dama ina son muyi aure ne…sai mamana tace wai kana da kudi kuma zaka kula damu sosai.Wasime dan Allah kiy hakri ki fahimce ni,nifa ban munafurce ki dan na cutar dake ba mamana ta dinga sakani,kuma dagayau nayi maka alkwari bazan kara daukar huduban mamana danna cutar da kanwarka wasime ba.

Yaya Nasan nayi kuskure dan Allah kayafemin..ka dubi girman Allah ka dubi girman son da nake maka yaya.

Atake Wasime tafarajin kamar zata mutu tsabar kishi da haushin jin wayannan kalaman soyayayyar da ke futa a bakin najaha,tsaki taja ta kauda kai tana huci.

Ajiyar zuciya taheer yay cikin nazarin maganan da najaha ta furta akan mamanta,a hnkli cikin ranshi yace toh Allah ya kyauta..snn ya juyo
Najaha or what eva ur name is kin bani mamaki kuma kin cuce kanki.
Ni bawai na kyaleki kina zuwa gidan nan Haka kawai bane,na barki ne sabida kwanciyar hanklin matata.

But with all these wat ure saying akan mamanki i think is best if u stay away from my wife,jan kunnenta yay yace “ke daga yau saiyau kar na kara ganinki a inda take inba haka ba zan kulleku a caji office daga ke har maman naki..dungurinta yay yana mai jefata baya “dat was so stupid of u.

Najaha ta fara wani sabon kuka mai ban
tausayi cikin shesheka
Tace yaya kenan baka sona?nifa ina sonka
Sai cewa kake wai matarka matarka waye kuma matarka…cikin matsanancin kuka ta karashe.

Takaitaccen dariya taheer yay yace Stop dreaming young girl! Ki bude idonki ki kalleni da kyau ni ba abokin wasanki bane and also extend this information to ur sensenless mother datake kkrin turaki hanyar da zai lalata rayuwarki ya cutar dake

I just dont knw why wasu matan sai ahankli Wato Mahaifya ce ma zata nuna ma yarta hanyar bibiyar maza at this ur tender age?no wonder u alwys sound too desperate nd stupid with me.

tsumammen Kuka ne ya kara kufce mata tana cewa Yaya Wallh kuskure ne yaya harcikin zuciyata nake son ka.. bani na kawo idean cutar da kanwarka ba wallhy mama na take gayamin..

Yace okay wayene kuma kanwata anan?ina kiranta mata ta kinace mata kanwa ta ke kinsan me kike fadamin kuwa to maza ki iye bakinki…

A rikirkice Najaha ta harzuko cikin matsancin kuka duk da bata gama dago meyake son gaya mata a hatgitse ta mike zatay magana ya daga mata hannu cikin datse ta da daurarriyar Fuskan sa

Yace hey hey just shut up nd listen to me,wani jawo wasime yay ta fado a jikinshi ya dan rungume ta sosai ta gefen shi hannunsu sakale da juna,kallon tsakar idon ta yake yana sakar mata murmushi mai sanyi dan tayi cool off dan yaga bakaramin baci ranta yakeyi ba,nan take najaha tasoma jin kamar jiri jiri ne yake son zubar da ita awajen kwakwalnta baya son ya fahimce abunda take son gani agabanta yanzu.. ya cigaba da maganan sa ahaka yana ce ma wasime”bazamu yafe ma mamanta ba amma kin yarda inyafe mata?..
Acikin wata salon rigima wasime tay Rolling idanunta tana mai kara narkewa ajikinshi tuno da cewa duk abunda ya afku ba najaha ce ta shirya ba yasatace “toh ai shikenan kayafe amma banason ta kara zuwa nan..”.wani kiss ya dora mata a saman goshinta ta mayar masa da faffadan murmushi
Hannunsu sakale da juna ya juyo ya kalle najaha dake sama sama da numfashinta tanaji kamar mafarki takeyi
Ba yabo ba fallasa aheer yace ‘its okay najaha,..
What eva u nd ur mum did is none of our business…u just have to abide by my rules nd stay away from me nd my wife tunda dama kince sabida ni kike zuwa gidan nan,..”Wasimé matata ce,and she doesnt like u anymore. Har baki da kunya agabanta kike cewa kina son mijinta!Yay yar dariya toh Ke ya zakiji in aka miki haka uhm?wani kiss din ya dora ma wasime a goshi cikin wani salo mai Æ™ayartawa yaja hancinta ahankli yace my jelous wife…
Lumshe ido wasime tay fuskrta a sakalce tana mai turo mai baki
Yace “Toh zan barki da kawarki ki rakata waje.

Wani irin narke mishi wuya wasime tayi cikin maƙe kafada tace yaya da can nina kawotane ?itafa tazo dakanta dan haka kafafunta ya maidata gidansu.Yaya ka harbesu in suka kara kulani kaji?wani tantame kugunsa tay snn ta juya tana watsa ma najahar wani matsayicin kallo
Tace…”Nide wallhy nagayamiki ni ba kawarki bace tunda yaya ya yafe miki kuma kinsan ni matarsa ce saiki kama hanyarki ki tafi gidanku aini zan masa komi ba keba,wallh karki kuma kara dawowa Naganki kusa da yayana saina miki shegen duka..

A kasa najaha ta zube ta balla wani asararren ihu..
Wayyo Allah na..
Wasime dan Allah dagaske kuke min?.
Yaya,taheer wasimé fa kanwarka ce dan Allah kudemin wannan wasan .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button