NOVELSUncategorized

NAJEEB 4

DEDICATED TO…..

MY LOVELY MUM
        PAGE 4

Lokaci d’aya ibtisam ta d’auki ruwan ta fita, Granny na tsakar gida ita da ummi, sai murmushi Granny take kaman ance an bata kyautar kujeran makka.

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9704, ‘t’: ‘160 by 600’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());

Koda ibtisam ta k’arasa falon da sallama ta shiga, kabir ya amsa,  ajiye ruwan tayi da drinks tare da fad’in bismillah 

Murmushi yayi yace ngd ibti 

Kanta na k’asa Tana wasa da yatsun hannunta, tana tunani mai yasa nake jin nauyin shi?  Kai gaskiya da sake, koda yake inna tafi makaranta ai shikenan k….

Katse mata tunani yayi da fad’in ibti, nazo ne muyi magana ta fahimta, kaman yanda na Fara fad’a miki jiya, akan ni auranki zanyi dagaske, bada wasa nazo ba, sai dai baki ce komai ba, ina fatan yanzu zan samu amsa daka gareki? 

D’an murmushi tayi tare da cewa naji abunda kace, sai dai…..  Shuru tayi ta kasa fad’in abunda take son cewa 

Ganin haka yasa Kabir yace Ina sauraranki ibti 

Kanta na k’asa tace banki magananka ba, amma sai dai ni yanzu karatu ne a gabana, shi nake burin inyi 

Kabir yayi murmushi tare da fad’in, ibti karatu ai baya hana aure, sannan Nima namiji ne mai burin ace iyalina tayi karatu, so inaga wannan ba matsala bace, kawai yardanki nake nema 

Shuru tayi tana nazari, toh inta amince Mai cewa zaiyi zai turo? Ko ya?  Ita dai gaskiya bata shirya aure ba, dan bata son abunda zai kawo mata tsaiko cikin karatun ta, yanzu Idan tayi aure tana karatu lokaci kad’an ace ta samu ciki, ga karatu ga ciki, haka inta haiyu ga raino ga ciki, gaskiya a’ah bazan yarda ba, ko kuma wasu mazan in ba’ayi Sa’a ba suce su basa son karatun Bayan da farko sunce sun amince mace tayi karatu ga…. 

Katse mata tunani yayi da fad’in ibti, plz say something 

Murmushi tayi wanda bata san tayi ba, tace kana nufin zaka jirani har shekara hud’u? 

Kabir yace ibti shekara hud’u yayi yawa, ki kalleni ki gani ya kamata ace na ajiye iyali, mutun kaman ni bai kamata ace banda iyali ba, duk da aure lokaci ne, amma ibti Idan kika amince na turo manya, ni a Abuja nake aiki sai weekend nake samun hutu shima bako yaushe ba, gobe zan koma Abuja da safe, a ina kike son zuwa karatun? 

A hankali tace ABU zaria.

Yace toh kin gani, zaki samu lokacin karatu tunda ba gari d’aya muke ba, kina kaduna Ina abuja, sai inna samu time inzo, ko in kunyi hutu ki dawo inda nake.

Ibtisam shuru tayi tana nazari, lallai maganan Kabir gaskiya ne, toh amma abun dubawa da tsoro shine inta samu ciki fah? Anya wannan auren zaiyu kuwa? Koda yake ai nasan ba lallai wani abu ya shiga tsakaninmu ba, kai any….

Kabir yace ibti kiyi tunani akai ki gani I…. 

Babu wani tunanin da zatayi, Kabiru ka turo iyayenka kaji, Granny ce Mai wannan maganan wanda tun d’azu take labe take jinsu.

Gaida Granny yayi cikin girmamawa, amsawa tayi cikin fara’a tare da fad’in karka damu ka turo iyayenka, a tsaida magana, Kaga a hankali kwa fahimci juna 

Ibtisam ji tayi kaman ta saki ihu saboda takaici 

Kabir yace Granny zan turo su, amma nafi son mu fara fahitan juna Kafin manya su shiga cikin batun

Tace a’ah Kabiru, ka turo kawai 

Yace toh Granny insha Allah zan turo.

Tace Allah yayi albarka, tare da kallon ibtisam ta galla mata harara sannan ta fita. 

Kabir murmushi yayi tare da fad’in Granny akwai ban dariya, kallon ibtisam yayi wacce yaga ta had’e rai, alaman ranta ya baci, murmushi yayi tare da fad’in ibti kiyi hakuri na fahimce ki ko bakiyi min bayani ba na gane abunda kike nufi, kina da burin kiyi aure Bayan kin kammala karatu, babu damuwa zan iya jiranki, amma ki bani dama manya su shiga cikin lamarin asan da maganan. 

Ibtisam jin haka yasa taji dad’i Sosai, ta kuma yarda Kabir yana Sonta tunda har zai jirata ta kammala karatu,  a hankali tace babu damuwa, dama ni babban burina in kammala karatun sai inyi aure ta yanda hankalina zai nutsu waje d’aya. 

Kabir yayi murmushi tare da fad’in kice dai ta yanda zaki kula dani .

Hannunta tasa ta rufe fuska tana murmushi alaman taji kunyan maganan da yayi. 

Yace yanzu dai kin amince in turo koh? 

Kai ta d’aga mishi alaman eh 

Wani irin ajiyan zuciya ya sauke Wanda har Tana jiyowa, tare da furta Kalman Alhamdullilah, gaskiya ina cikin farin ciki, ibti na tabbata idan manya suka shiga cikin maganan koda Kinje karatu babu Mai kwace min ke.

Murmushi tayi ba tare da tace komai ba, mamaki take yanda harta amince akan ya turo magabatanshi, tunda take bata taba jin wani abu akan namiji ba sai yau, kodan kabir shine namiji na Farko data taba doguwar fira dashi haka? Eh tabbas hakane saboda bana magana da maza irin haka, toh mai yasa nake jin nauyin shi? Kai Mai yake damuna ne haka, daka had’uwa da mutum jiya jiya yana son saka min tunani lokaci d’aya ta cire tunanin tare da k’ago murmushi tace baka sha ruwa ba. 

Yace Alhmdlh ibti nagode, am Okey, tashi yayi tare da fad’in zan tafi zadai muyi waya, cuz gobe zan koma office. 

Tace Allah ya taimaka ya bada Sa’a. 

Kabir yaji dad’in addu’anta Sosai ya amsa da Ameen ibti, muje in baki sa’ko. 

Binshi tayi har waje inda ya bud’e motarshi ya d’auko Leda guda d’aya babba, yace gashi. 

K’in amsa tayi tare da fad’in wannan fah? 

Yace ki Fara amsa first.

Mi’ka hannu tayi ta amsa Tana kallon shi ta gefen ido, gskya Kabir ya had’u ta furta cikin ranta 

Yace na tafi sai munyi waya 

Tace nagode tare da shiga gida.





              London
Najeeb ne ya fito daka toilet towel yasa ya d’aura a dai dai kugun shi, sannan wani towel din ri’ke da hannunshi yana goge ruwan dake kanshi, yana abun ne cikin sauri daka gani zai fita ne yanda yake sauri. 

Janet dake kwance tana kallonshi, lokaci d’aya ta taso babu komai a jikinta, ta rungume shi ta baya, tare da fad’in nagit naga kana sauri kaman zaka fita, ina zaka? 

Bai ko kalleta ba balle ya bata amsa, ganin haka yasa ta sakeshi tare da d’aukan kayanta ta Fara sawa, Bayan ta gama ta koma kan gadon d’akin ta zauna tana kallonshi tana murmushi, komai na nagit yana burgeta ya iya love da sarrafa mace, gashi ya had’u ga kyau ga kud’i, sai dai ta kasa gane halinshi, yanzu ya sake maka anjima ya d’aure maka, sai yayi abu kaga kaman bashi ba. 

Najeeb ya shirya cikin uniform Wanda yake k’ara mishi kyau da kwarjini, d’aukan wata jaka yayi lokaci d’aya ya bud’e ya cire kud’i ya watsa ma Janet tare da fad’in zaki iya tafiya, yana fad’in haka yayi gaba abunsa 

Janet kam da ido ta bishi tana mamakin wannan wani irin mutum ne haka, taga sunyi sex taji dad’i shima yaji dad’i, kodan wannan ai ya mutunta ta, d’an shuru tayi tana nazari tare da tambayan kanta Mai yasa tun ranan data had’u dashi baya komai da ita sai yasha alcohol?  Koda wasa ya fara mata zai barta sai yasha alcohol yake sex, kodai saboda alcohol dinne da yake sha baya cikin hayyacinshi yake sex da ita shi yasa baya ganin darajanta, kai ta girgiza tare da fad’in next time zanyi k’okari in tabbatar bai shaba, muyi sex haka inga miye matsalan, daukan kud’in daya watsa mata tayi masu uban yawa, tace nagit has alot of money, I love you nagit, tana maganan tana murmushi.

Najeeb direct airport aka kaishi, kai tsaye ciki ya shiga inda ya amsa wasu takardu ya cika, sannan ya nufi cikin jirgi, inda mutane suka fara shiga,Najeeb shida wani bature ne a wajan tukin jirgin, kaman dai ko wani jirgi matuka biyu, lokaci d’aya jirgin ya d’aga zuwa America 


             America

Koda jirgin ya sauka mutane suka fara fita, Najeeb kam, wayarshi ya kunna, sannan ya tashi ya fita daka cikin jirgin shima, wasu takardu ya cika sannan ya fita daka airport din inda ya tsaida taxi ya shiga tare da fad’ama Mai taxi din inda zai kaishi. 

Kofar wani Gida aka kaishi wanda ya fito yaba ma Mai taxi din kud’i sannan yayi nocking, wata baturiya cikin uniform Wanda zai tabbatar maka cewa Mai aiki ce ta bud’e nashi kofar tare da gaidashi cikin girmama, wanda wannan ne yasa na gane gidan Najeeb dinne. 

Shiga yayi tare da nufa bedroom dinshi wanda yake a gyare kamshi na tashi tako Ina, cire uniform d’in jikinshi yayi, ya rage daka shi sai boxer kwanciya yayi akan gadon d’akin sai juyi yakeyi, lokaci d’aya yayi tsaki tare da d’aukan wayarshi yayi rubutu alaman message ya tura, bayan ya gama ya ajiye wayar. 

Baiyi ko 30mnt ba sai ga wata kyakyawan yarinya baturiya ce amma tana da kyau Sosai, tasa dogon wando tare da wata top mara hannu, gashin kanta Brown, ganin Najeeb a kwance yasa tayi murmushi tare da fad’in sannu da hutawa cikin harshen turanci, kayan jikinta ta Fara tubewa, saida ta cire komai dake jikinta sannan tahau gadon domin massage yace yazo tayi mishi, hannuna tasa a bayanshi ta Fara mishi tausa tun daka kan wuyanshi har k’asan ‘kugunshi, Najeeb har ido yake lumshewa alaman yana jin dad’in tausan da take mishi, lokaci kad’an bacci ya D’aukeshi, ganin haka itama yasa ta manneshi a jikinta tare da kwanciya tana kallonshi, Najeeb yana dakyau duk wasu abubuwa da ake bukata a samesu a wajan namiji Najeeb yana dasu, sai dai abu d’aya yana da wulakanci Sosai, mai mu’amala dashi sai yayi hakuri, inma mutum baida hakuri Toh bazai iya hulda da Najeeb ba.

Koda Najeeb ya farka baiga Angelina ba, toilet ya fad’a yayi wanka domin yana jin jikinshi wani iri, Bayan ya fito yasa singlet da boxer yayi falo inda yaga Angelina Tana zaune tana kallo.

Ganin Najeeb yasa ta tashi da sauri tayi hugging dinshi tare da fad’in zo muci abinci nasa anyi maka abinci, baice komai ba sai dinning daya nufa ya fara cin abinci tare da alcohol d’inshi, sai dai bada yawa yasha ba, dan haka bai bugar dashi ba, bayan ya kammala ya dawo kujeran falon ya zauna, itama Angelina Bayan ta gama tashi tayi ta nufeshi tare da zama akan cinyarshi tasa hannunta ta rungumoshi tace yau zamu club?

Murmushi yayi tare da fad’in may be.

Tace plz muje mana, kasan a club muka fara had’uwa, tun daka lokacin ka hanani zuwa, kace sai dai muje tare plz muje yau nayi missing abubuwa 

Tureta yayi daka jikinshi tare da fad’in tashi ki tafi, karki k’ara nunamin face d’inki 

Cikin tashin hankali tace najit maiya faru? 

Yace How dare you, to say that in front of me?  You are a cheater only god knows what you are doing when am not around,  you even have the courage to say you miss something?  Kina fad’in kinyi missing abubuwa miye babu a nan?  Alcohol?  Food?  Kome?  Kawai kice kina son zuwa kiga wani yana fad’in haka yayi d’akinshi Jim kad’an sai gashi da kud’i ya kamo hannunta ya bata tare da fad’in fita tun Kafin in fitar dake, bana hulda da macen da take hulda da wasu mazan.

Jiki a sanyaye ta Fara fad’in najit plz listen to me….. 

Daka mata tsawa yayi tare da fad’in I said leave from here

Tsugunnawa tayi a k’asa tana ro’kanshi akan yayi hakuri, ba haka take nufi ba, amma najeeb yaki sauraranta, daka karshe ma falon yabar mata, ganin haka yasa ta tashi ta fita cikin takaici, ta tabbata ya barta kenan har abada, dama ya gaya Mata tun farkon haduwansu ta guji abunda zaisa yayi zarginta, daka ranan daya Fara zarginta ya barta kenan, ya kuma ja mata warning akan karya ganta da wani namiji, kuma tun daka lokacin ta kiyaye amma gashi bata tsira ba 

Najeeb kam ranshi ya baci Sosai, tare da takaici kenan yanzu bayan yayi sex da ita ta kuma bama wani shima yayi, tsaki yaja tare da tashi ya d’auko kwalban alcohol ya bud’e tare dasa baki ya fara Kwan kwad’a dan yasan shine kawai zaisa ya manta komai in yasha, Hmmm Allah ya kyauta





          Nigeria

Koda ibtisam ta shiga gida ta tarar da ummi a falo tana shirin fita, tace ummi Ina zaki? 

Tace zan shiga gidan Hjy fati ne d’anta ya kone ban shiga ba, hjy fati makwabciyar  suce.

Ibtisam tace Allah sarki, wanne a ciki? kai kuna akwai azaba Wlh 

Ummi tace Sosai dan karamin yaronta Jamil, ibtisam tace Kai Allah sarki Allah ya sawake, ummi tace bari in dawo Ina son ganinki, ibtisam tace toh, fita Ummi tayi ibtisam tayi d’aki tare da ledan hannunta 

Koda ta shiga taji kamshin sabulu alaman Granny tana toilet Tana wanka, ajiye ledan tayi akan gadon d’akin, cire hijab din jikinta tayi tare da bud’e ledan, su chocolate ne Kala Kala dasu biscuits masu tsada duk kuma na waje. 

Granny ce ta fito daka wanka d’aure da towel Hhhhh, ganin kayan ciye ciye yasa tace ah Kinga d’an arziki. 

Ibtisam tashi tayi tace Granny Wlh abunda kike min ya isheni, miye haka sai kace an gaji dani, baki San kina zubar min da kima bane 

Tsaki Granny tayi tare da fad’in, kimar banza da hofi, ai babban Kima shine kiyi aure, kuma Wlh Bari kiga Kabiru ya turo zaki sha mamaki, gwara tun yanzu ki Fara kallon kanki a matsayin amarya, maganan karatu kuma saiki daina ja’ira, wannan rashin kunyar da fitsaran da kikeyi duk saboda Kinga kin ri’ka ne a gaban mu, inda anyi miki aure tun tuni da yaushe, yarinya kaman Mai iska kin dage ke boko, muda bamuyi bokon ba mun fasa rayuwa ne, wannan yaran dai na masu jajayen Fata munaji kad’an kad’an toh mai za’a nuna mana?..  Tsaki ta saki tare da fad’in wannan kayan kabirun ne ya baki 

Ibtisam tace ban sani ba sai ki kirashi ki tambaya

Granny tace uwarki aysha kike fad’ama haka bani ba, aure ne dai sai kinyi ko zaki mutu, mutuniyar banza 

Ibtisam tace kaman yanda zaki mutu, kowa ya huta ba 

Granny tace oho dai, ko yanzu na mutu na taba aure kefa?  Ai gwara ni amma ke babu aure 

Ibtisam tace ni Wlh Granny ki koma Abuja da zama ki barni in huta

Granny tace gidan d’ana nake, dan haka ke zance ma ki tafi gidan miji kowa ya huta, ke in kika kalli madubi baki ganin tsufanki ace har yanzu kina gida 

Ibtisam tace Kedai kika Sani, aure ne dai Banyi sai lokaci yayi. 

Granny tace zanga karshen kafiya, naga dagaske kike, saina gama dake zan koma kan miskili shima, naga abun naku iskanci ne,  musamman ma miskili da in ana magana ya dinga wani kallon mutane Wai shi bature baya jin Hausa, wannan karan ashar zan dura ma d’an banza Nasan zai gane, ta k’arasa maganan tare da tsuke baki alaman bada wasa za tayi mishi ba 

Ibitsam kam babu abunda take sai dariya tare da fad’in tunda mutum baya jin turanci basai kayi hakuri ba, ko dole sai kinyi magana dashi 

Granny tace ai zanyi maganin d’an banza Wlh, kauye zani in samo mishi Mata, insa a d’aura Mai, zanga karshen miskilanci da rashin jin Hausa ta k’arasa maganan cikin jin haushin jikanta baya jin fulatanci baya jin Hausa, Hhhhhhhhhh su Granny manya muje zuwa 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button