
Tashi yayi a hankali yake taku cikin kamala da nitsuwa irinta manyan limamai a hankali yake manna farar tattausar fatar ƙafarshi da in ya taka sai kaga kamar jini zai tsallo.
Yana shiga cikin ɗakin nashi, al’kyabbarsa ya cire tare da buɗe wani sashi na durowarsa ya sanƙala a masanƙalinta.
Da tattausan farar jallabiyar dake ƙasanta ya shiga bedroom da ita,
Wannan lokacin wonkansa ne, babu abin da zai katse mishi uzurin domin ya kasance mutun mai mutunta lokacin rayuwarsa ko wani lokacin da abinda yakeyi.
Wonka yayi cikin tamfatsen bathroom ɗin nashi.
Yana fitowa, ya wuce gaban dreesing mirror, kimtsawa yayi a gaggauce dan lokacin tafiya aikinshi ya karato.
Koda ya gama kimtsawa cikin wasu tattausan manyan kaya riga da wondone da kuma babbar gariyarsa, kayan sun kasance farare ƙal-ƙal ne, sai zazzafan aikin kufta da akayi mishi mai blue color, kana sai hular zanna bukar daya murza bisa kanshi da yake wadace da tattausan suma baƙiƙƙirin mai sulɓi da sheƙi,
hular itama farace sai ratsin blue, hakama takalman sawunshi da suka kasance irin na sarakuna ne,
Agogon Daimond dake hannunshi shima yanada yanayin ɗigon blue mai garai-garai,
Sai kuma ya sunkuyo ya ɗauƙi biyu daga cikin woyoyinshi yasasu a al’jihun babbar rigar tasa,
jakar system ɗinshi ya ɗauka da hannunsa na dama, kana hannunshi na hagu kuma sajenshi yake shafawa a hankali har zuwa kan madai-madaicin tsabtaceccen gemunshi mai ɗan karen kyau da burgewa.
A haka ya fito daga cikin ɗakin nashi.
Yana fitowa cikin tamfatsen falon nashi da ya kasance yanada iyaka da bayi da hadimai duk iya karsu can bakin ƙofar babban falo bai yarda da wai bayi su shigo suyi mishi hidima har cikiba,
Jamil shike kula da tsabtan sashin sirrin ɗan uwan nashi.
Ido ya lumshe jin wani irin sassanyan ƙwamshi da sanyi mai ratsa zuciya daya ziyarci jiki da zuciyarshi.
A hankali yake taku, har zuwa dinnin area, a hankali ya ɗan juyo, jin an jamishi kujerar.
Jamil kenan.
Zama yayi bisa kujerar, kana, ya miƙawa Jamil jakar system ɗin nashi.
Amsa yayi ya rataya a kafaɗarshi,
sannan ya matso gab kusa da ɗan uwan nashi,
baƙin Tea ya haɗa mishi da zuma sai bredy wanda shima da zuma a jikinshi ,
wanda yasan iya abinda zai ci ya sha kenan duk da tarin. Abinci da hadiman Aunty Juwairiyya, suke kawowa dominshi ga kuma na Hadiman Hajia Mama, wanda duk Umminshi Jakadiyace ke kawosu, domin ita tana shiga har cikin falonshi ɗakin konciyarshi ne dai bata shiga, amman falo ukun nan duk tana shigarsu da kitchin da sauran ɗakunan sashin.
Suna zama babu jimawa, wayar Jamil ta fara tsuwa, da sauri ya ɗauka tare da karawa a kunne,
sai kuma yayi zuru-zuru da idanu ganin yadda Hammanshi ya tsareshi da fitinannun idanunshi masu sa hanjin cikinsu kaɗawa, cikin yin ƙasa da murya yace.
“My love Sheykh yana kusa”.
Ya ƙarishe mgnar da murmushi a fuskarshi, shi kuwa Sheykh kauda idonshi yayi yaci gaba da zuƙan tea ɗin a hankali a hankali.
Shi kuwa Jamil cin abinci yai haninƙan kana.
Shi kuwa Sheykh ido kawai yake zubawa ƙanin nashi bai tashiba har saida yaga ɗan uwan nashi ya gama cin abincin.
Sannan suka jero suka fito falo,
A can bakin ƙofar shigowa babban falon suka samu sarkin ƙofa da kuma hadimai na jere a wurin suna hangosu duk suka rusuna har ƙasa har suna haɗa baki wurin cewa.
“Takawarka lfy ɗan Babban Yaya jikan mai martaba sarkin Nuruddeen jika ga mai Alfarma Sarkin Musulmai Jalaluddin.
Malam ɗan Malam Habibullah jinin Limamen Saudia malamai magada annabawa, jika ga ƙabilar da tafi ko wacce ƙabilar duniya d…”.
Hannun shi biyu ya ɗaga musu alamar amsawa gaisuwar da sukayi mishi, da kuma dakatar dasu da kirarin da sukeyin.
Kana yaci gaba da taku Jamil na biye dashi a baya, Sarkin ƙofane yayi saurin rusunawa tare da cewa.
“Hajia Mama ta turo jakadiya a sanar maka cewa tana buƙatar ganinka”.
Kanshi ya gyaɗa kana yaci gaba da tafiya,
Gefen dama ya nufa, inda wani tamfatsetsen part mai tarin girma yake, a hankali hadiman dake tsaron wannan ƙofar suka fara rusunawa tare da bashi hanya da gaidashi.
Tafe suke har cikin part ɗin, wani babban falo suka fara ratsawa kana suka wuce zuwa cikin wani corridor sai gasu a wani fitinenne falo mai wadatar tsabta da ƙamshi.
Wasu ƴan yarane guda biyu duka mata,
Suna ganinsu suka ruga a guje jikin Sheykh Jabeer suka faɗa tare da cewa.
“Sabahul khair Uncle MJ”.
Sunkuyowa yayi ya ɗan shafa kansu tare da cewa.
“Sabahul noor ya Habittey”.
murmushi sukayi kana suka sakeshi suka isa gaban Jamil sunkuyowa yayi ya ɗauki ƙaramar bayan sun gaidashi ne babbar ta juya da gudu tana cewa.
“Ummi ga Uncle MJ”.
tsayawa tayi tare da kamo hannun wata kekyawar mace matashiya yar duma-duma, tayi shiga irin ta larabawa, kamo hanunta tayi suka fito falon.
Murmushi ta ɗanyi tare da cewa.
“Barka da safiya GARKUWAN FULANI, GARKUWAN ahlin Sitti”.
Fuska ya ɗan sake still bawai yayi murmushi bane, a hankali yace.
“Barka da safiya”.
“Barka dai Sheykh Dr Garkuwa”.
Babbar rigarshi ya ɗan gyara tare da cewa.
“Ya jikin Ya Jafar?”.
Kai ta ɗan ranƙwafar tare da yin rau-rau da idanunta murya na rawa tace.
“Jiya kwana yayi baiyi bacciba, Sheykh, hankalina yana tashi, sabida duk randa baiyi bacciba, to kwana yake karatu yanayi yana kuka, kukan da yakeyi ɗin ne yake sashi zazzaɓi da ciwon kai, gashi ba cikin zuciyarsa yake karatunba ya wuni karatu a baiyane ya kwana karatu a baiyane babu bacci”.
Kanshi ya ɗan jujjuya tare da nufar kofar wani ɗaki.
Jamil da Juwairiyya na biye dashi a baya.
Suna shiga cikin ɗakin, da sauri Sheykh ya karisa gaban wani kekyawan mutun fari ƙal mai tarin tsabta wanda yake tsananin kama da Jamil duk da duk suna kama da juna amman Jalaluddin yafi kama da Jabeer, Jamil kuma yafi kama da Jafar.
Zaune yake bisa sallaya, ya jingina kanshi da jikin gado, karatun al’ƙur’ani yakeyi cikin nitsuwa da da cikar tajwid, babu ɓata ko na ɗigo, yana karatun ne hawaye na kwaranya daga kwayar idanunshi,
A hankali Sheykh Jabir yasa Hannu ya kamo hannun ɗan uwan nashi,
A hankali Ya Jafar ya buɗe idanunshi ganin mutumin da shi kaɗai ke sashi yin abu yayi ko ya hanashi ya hanune ya sashi gyara zama still yana karatu.
A tausashe Sheykh Jabir ya ɗan ranƙwafar da kanshi cikin salon tausayawa da muryar larabawa yace.
“Sadakallahul Azeeeeeem”.
Jin hakane yasa wannan bawan Allah’n ya ɗago tafin hannunshi addu’o’in ya, fara karantawa kusan tsawon 3 minute sannan suka shafa a tare,
Cikin wani zafi da ƙuna Sheykh Jabeer ya taune lips ɗin shi na ƙasa hannunshin yasa ya kamo na Ya Jafar ɗin,
ba musu ya miƙar dashi,
kan gadonshi ya zaunar dashi,
A hankali ya juyo ya kalli Juwairiyya cikin sanyi yace.
“Yaci abinci kuwa?”.
A hankali tace,
“Tunda asuba daya dawo masallaci na bashi yaci abinci, kuma yanzuma na bashi ya ɗan ci”.
Kanshi ya rausayar kana yace.
“Maganin shi fa kin bashi”.
Kai ta jinjina tare da cewa.
“Eh na bashi maganin yasha”.
Jin hakane yasa Sheykh ya kamo hannun kekyawan Yayan nashi ya kontar dashi bisa gadon blanket yaja ya rufe mishi rabin jikinshi a hankali yace.
“Ya Jafar kayi bacci, kaji jikinka zafi”.
Shiru bai kulashiba sai dai, ya lumshe idonshi.
A hankali ya juyo ya kalli Matar ɗan uwan nashi kuma ƴar kawunsu yayan Mamansu yace.
“Juwairiyya Nagode”.
Hawayen dake zubo mata ta sharce tare da kamo yaranta ta ruggumesu,
Jamil kuwa tuni yaketa zubda hawaye.
Cikin rawan murya Juwairiyya tace.
“Sheykh ka dena gode min nimafa Ya Jafar ɗan uwanane kuma mijinane, uban ƴaƴana, to in ban kula dashiba da waye zan kula a duniya?.”
Kanshi ya kauda kana ya juya ya nufi hanyar fita a ranshi yanajin ko sai yaushe manyan burukan rayuwar da fatanshi da addu’o’in shi zasu ƙarɓu yana ganin daraja da girman Juwairiyya domin tayi musu tsantsar halacci ta zauna da ɗan uwanshi a matsayin majanuni, a haka suke tafiya yana zancen zuciya.
Jamil na biye dashi a baya.