GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Shi kuwa Sheykh kamar yadda ya saba, hakane baya amsa kiran kakan nashi, sai dai ya bari in tayi ta katse sai ya kira, shiyasa, yanzuma ya bari saida ta katsen sannan ya kira.

Gyara zamansa yayi tare da kara wayar a kunnensa na dama.

Imran kuwa yana ganin kiranshi yayi maza ya amsa,
cikin tarin girmamawa yace.
“Barka da hantsi, Hamma Jabeer”.
A can gefen Sheykh Jabeer ɗin kuwa, ido ya lumshe cikin yanayinshi da sun rigaya sun saba yayi shiru.
Da sauri Imran ya kuma ɗan rusunar da kanshi yace.
“Afwan Sheykh Assalamu alaikum “.
Murya can ƙasa yace.
“Wa alaikassalam”.
Cikin ɗan tura baki Imran ya kuma maimaita mgnarsa ta forko.
“Barka da safiya, Hamma Jabeer ya, Sitti?”.
A taƙaice yace.
“Alhamdulillah”.
Da sauri Imrana yace.
“Masha Allah, ga Lamiɗo”.
“Na’am”. Yace a takaice.
Shi kuwa Imran miƙawa kakansu wayar yayi.
A hankali Sheykh ya ɗan buɗa laɓɓansa cikin zazzaƙan sautin muryarsa yace.
“Assalamu alaikum”.
Murmushi mai cike da so da ƙaunar jikan, nasa yayi tare da amsa sallamar tasa. Gaisawa sukayi, bayan sun gaisa ya tambayi labarin su Sitti da ƙanennenta da kuma mahaifinta, sai kuma ya kora mishi jawabin abinda ke faruwa a jihar tasu.
Kana, ya ɗoro da cewa.
“Ka dawo, kayiwa lamarin tubkar hanci”. Cikin sanyi yace.
“In sha Allah. Ina nan tafe, nanda kwanaki uku. Ina jajanta musu, abinda ya faru, kuma in sha Allah.
hakan bazai kuma faruwa ba.

Da haka sukayi sallama.

A can garin Numan kuwa cikin Rugar Kikan.

Gaba ɗaya garin shiru yayi, dan wannan abunda ya faru yayi masifar shiga jikinsu.
Da dama maza matasanmu sun tafi kiwo, kamar yadda suka saba, rayuwar yau da kullum.
Saura sai irin dattawan da aka bari, da mata da yara maza da mata.

Cikin garin Bonon kuwa, gaba ɗaya, matasan garin dama ƙauyuka gefensu na ƙabulun Ɓachamawa, duk sun hallara wuri ɗaya, suna cike gaban dodon tsafinsu, wato Bonon ɗin, giyar burkutu mai ɗan karen tsami da wari, suketa sha, tamkar zasu fasa cikkunansu.
Yayinda gefe guda kuma, maƙerar dake gefe wasu matasa su ne maƙera keta wasa ababen faɗansu, kamarsu wuƙaƙe, Adda, sitaka, barandami, mashi, kibau, da dai sauran mugayen makamai, sai sheƙi sukeyi.

Suna cike a wurin, Ba’ana ya iso, cikin wata shigar rigar saƙi.
Hanya suka rinƙa buɗa mishi, hardai ya isa ga sarkinsu, dake zaune gefen dodo sun. Zama yayi kusa da sarkin nasu ya sasu a gaba,
Cikin harshen ɓacamancin yace.
“Ku hanzarta, ku shiga, duk matasansu majiya ƙarfi, sun tafi kiwo. Dottijan su kuma sun tafi, kai gulmarku, ga Sarkin su wannan karon basu tsaya ga sarkinku na nanba, ina da yaƙinin kuma za’a sauraresu a can.
Yanzu matansu da ƴaƴansu, ƙanana mata da mazane suka rage a garin.
Sai wasu dattawansu dake, dakon dawowar magulmatan can.
Kuyi maza, kushiha kafin su dawo, ku share garin kab.
Ku kashesu gaba ɗaya babba da yaro mace dana miji.”
Da sauri wani daga cikin su yace.
“Harda gidansu Shatu?”.
Cikin izaya yace.
“Harda su, domin Mata, bata nan, ku kashe kowa nata, ta hakane zata dogara dani kaɗai tunda bata da kowa nata a duniya, dole Ni zan zama mijinta ubanta yayunta ƙannenta uwarta, in zama Garkuwarta in zame mata duniyarta ta hakane zata yarda nine ɗaya gatanta kuma duniyarta, ba tare da ta zargeniba, a hankali wata rana in sata tayi ridda, musha giya, muyi tsafi tare da ita, bazatayi min musuba, mu haifi ɗanmu na forko mu bawa dodonmu yasha jininshi yasa mana al’barka a aurenmu”.
Wani irin ihu da sowa na tsantsar jin daɗin bayaninshi sukayi baki ɗayansu.
Hakama dodonsun, saida ihunshi ya firgitasu baki ɗayansu.
Dariya mai amo mara daɗin ji. Sarkin nasu yayi, kana ya busa ƙahon dodonsun, alamun ya basu izinin tafiya.

Nan fa duk suka rinƙa shiga, cikin maƙerarnan suna ɗaukan makamai, suna nufar garin Rugar Kikan (Rugar Bani) kenan a guje…

Cikin garin Shikan kuwa, Bani rana ta fara tasawa, mata masu zuwa tallan nono cikin garin Numan, suka fara ɗaukar ƙorarensu, suna fita garin.
Yara maza da mata kuwa, wasu na wasa wasu na ɗebo ruwa, wasu na ɗebo kayan lamɓu.
Yayinda wasu kuma suka dawo break dan tara tayi.

Cikinsu kuwa harda Junainah.

Tafe take da saurinta da ɗan tsalle-tsallenta tana rataye da yar jakarta,
da sauri ta tsaya ganin Junaidu a gabanta rike da kwanɗon zabari wanda yake cike da ƴaƴan itatuwa.
Murmushi ta ɗanyi tare da sunkuyar da kanta cikin surutunta tace.
“Har naji tsoro!”.
ta ƙarishe mgnar tana kallonshi,
Murmushi yayi mata shima cikin son ƴarinyar yace.
“Haba dai, tsoron me kuma zakiji, tunda gani, babu abinda zai sameki muddin ina raye, zan zame miki Garkuwa”.
Da sauri tasa hannu ta rufe bakinta tare da cewa.
“Kai! Kai! Ya Junaidu, sunan Babanmufa ka kira”.
Murmushi mai kama da dariya yayi kana yace.
“Au na manta ashe sunan surki nane”.
Kai ta gyaɗa mishi kana tasa hannu ta amshi, nonon inabin da yake miƙa mata,
baki ta buɗe da nufin sawa a baki,
sai kuma ta tsaya tare da tura baki jin yana ce mata.
“No kada kici ba’a wonke bafa.”
Sai kuma ya ajiye kondon, ya amshi inabin ya ɗan gangara, gefe kaɗan ya wonkeshi a bakin ruwan wutsiyar Kogin da yayiwa Rugar tasu ƙawanya.
Ya tahowa tana kallonshi.

Koda ya iso miƙa mata yayi,
kana ya ɗauki kondon, ganin still tanata kallonshi ne ya sashi cewa.
“Ya dai?”.
Kai ta kauda tare da fara tsinkar ƴaƴan inabin tana afawa a baki tana taunawa,
Murmushi ya kumayi ganin yadda ta lumshe idonta.
A hankali tace.
“Ya Junaidu kayi kyau sosai yau, har kamar ka fini kyau”.
Dariya ya ɗanyi kana yace.
“Yo dama ai na fiki kyau”.
Maƙe kafaɗa tayi tare da cewa.
“Uhum a a kam”.
A haka dai suna tafe suna hira.

Can cikin gida kuwa, Ummiy ce zaune bisa kujera ƴar tsuguno da buta a gabanta, alamun al’walan sallan walaha, zatayi.
Inna kuwa, da wasu maƙotansu uku Biba, Hari, da Innawuro. suna zaune bisa taburma a tsakar gidan. Suna amsar gaisuwa.

Can cikin garin kuwa su Alhamdulillah Manu dasu Siddine da dai sauran dattawan garin ne zaune a fada.
Sai yara daketa kai komo.

Da sauri su Siddi suka miƙe tsaye ganin, matasan mayaƙan ƙabilar ɓachama, sunata shigowa garin tako ina gabas da yamma kudu da Arewa, bisa dukkan alamu zobe sukayiwa garin
Kana ga zurma-zurman makamai masu tsawo tamkar raƙumai. Sai sheƙi sukeyi.

Cikin ɗaga murya, Alhaji Manu yace.
“Kai lfy? me haka?”.
Ganin sun nufosu gadan-gadan ne yasa, suka miƙe gaba ɗayansu, kowa ya fara, neman makari, to amman ina, basu da zato ko sanin za’a far musu, shiyasa basu da shirin komai na kare kai.
Ɗaya daga cikin sune, yace.
“Mu gudu kashemu sukeda shirin yi ba tare da laifin komaiba”.
Siddine ya kuma ɗaga murya tare da cewa.
“To in mun gudu matanmu da yaranmu fa”.
Ihun da sukajiyo tako wani sashi na garinne ya tambatar musu, ana karkashe su.
Gudu suka farayi kowa ya nufi hanyar gidanshi dan ɗaukar matakan kare kai.
Sai dai ina basu da hanya duk inda suka ɓullo sai sunci karo da, mayaƙan.

Lokaci ɗaya garin ya ruɗe ya birkice kota ina sai ife-ife da gudun ceton rai da makiyayan Rugar Kikan keyi.

Wani irin sauti mai baiyana azabar fitan rai Alhaji Manu yayi, lokacin da wani kafurin ya caka mushi sitaka a ƙahon zuciyarshi.
Siddine ne ya juyo da azaban razani, amman sai shima ya saki wani sauti mai gigitarwa jin azaban sara da sukan da akeyi mishi.
Garifa ya kacame,
Hadi ne babban ɗa ga Alhaji Haro mahaifinsu Junaidun Junainah, ya nufi cikin gidansu da azama,
Yana cike da fargaba, da tashin hankali domin wasu irin ihu da yake jiyowa a cikin gidan nasu.
Yana kusa kai ya samu, makasan suna cike a gidan.
Suna ta’addanci, sun kashe kowa na gidan.
Ganin haka ya juyo yana juyowa. Yayi kiciɓis da abokinshi Sale, yana tafe jini na zuba an farka mishi ciki.
Cikin magagin mutuwa yake cewa.
“Hadi sun kashe kowa na garin nan sai wanda baya nan.
Hadi na kira Hukumar yan sanda ta nan cikin Numan na shaida musu, amman kafuran nan maƙiya Allah da Manzonsa sai cewa sukayi,
A kashe mu mana, ai an rage musu aikine.
Na kira su Arɗo Bani, suna ɗagawa katin wayata ya ƙare.
Hadi sun kashe kowa na gidanmu.
Taroshi Hadi yayi suka faɗa nan suna kuka mai cike da taraddadin rabuwa.
Cikin ƙarfin hali Sale ya ture Hadi tare da cewa.
“Ka gudu Hadi ku gudu, Ni nasan bazan rayuba.
Ka gudu.
Sun kashe min Kowa har jariren tagwayen da aka haifa min shekaran jiya, sun kashesu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button