GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Yah Jafar ne ya gyara zamanshi tare da cewa.
“Tabbas kuwa Hajia Mama da Baba Kamal da Baba Nasiru da Hashim sune manyan Magautan mu”.

Da sauri Sheykh ya miƙa tare da kamo hannun Hajia Mama da taketa son kwaɓe kayanta.
Da sauri ya nufi Side ɗinsa.
A wannan ɗaya ɗakin yasata ya rufeta bayan yayi mata allurar bacci.
Kana ya fito.
Nan ya samu Lamiɗo yasa Fadawan shi sun fita da Baba Kamal dake ta ihun hauka.
Sannan Jalal kuma ya miƙa ya damƙi Baba Nasiru dake son guduwa.
Ya miƙashi hannun abokanshi sojojin daya kira bisa laifin kisan kai.

Shi kuwa Yah Sheykh a hankali ya kalli Yah Hashim a hankali yace.
“Ashe harda kai a cikin magautana Yah Hashim. Kai lallai ɗan Adam darene babu mai saninsa sai Allah”.
Lamiɗo ne ya kamo hannunshi ya zaunar dashi kana yace.
“Kai Hashim fice mana daga nan bama buƙatar mai muguwar zuciya ko ɗaya a nan”.
Ai kuwa da gudu ya fice cike da kunya.

Shi kuwa Lamiɗo gyara zamanshi yayi tare da cewa.
“Jafar bamu lbrin meya faru da kai da mahaifiyarku a dare ɗaya ta sauya halitta daga mutun zuwa tsuntsuwar Boleru kai kuma ka dena mgn”.

Gyara zamansu sukayi baki ɗayansu dan wannan itace tambayar da take cinsu a rai tsawon shekaru goma sha uku kenan gaba ɗayansu.

Cikin gyara zamanshi ya ya fuskancesu kana a hankali yace.
“A ranar…!

Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300 babbancinsu a posting ne 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Ta wannan ac no zaku tura kuɗin sai kiyi screenshort na Debit Alert ɗin ki turo min shaidar biyan ki ta whatsApp 09097853276 ku yan 300 in baku da damar biya ta Account zaki iya sayan katin mtn na ɗari uku kacal sai ki copy numbers ɗin ki turo min ta whatsApp 09097853276.

                   By
        *GARKUWAR FULANI*

[4/2, 7:41 AM] +234 806 559 0880: “Aranar wata jumma da da wanna Zazzafar ƙaddara ta rufta damu shekaru goma sha uku baya.”
Sai kuma ya ɗan tsakaita
tare da jan
sassayan numfashi ya gyara
zamansa tare dasa tafin hannunshi ya share hawayensa.
Yayin da gaba
ɗayansu kacokam
suka mai da hankalin su kansa,
Duk sun ƙagu suji yadda a kayi a wannan ranar da basu manceba.
Shi kuwa Yah Jafar wani numfashin yakuma.
Saukewa kana yaci gaba da cewa.
“Ranar da dare bayan anyi sallan isha’i duk muna falon Mamey dani dasu Jalal Jamil Affan da Ummi da Imran yana ɗan sheksru takwas lokacin.
Anan mukaci abinci kana muka zauna muna hira.
Kasan cewar akwai shaƙuwa mai tarin yawa tsakanin Mamey da Affan da yake tana da son yara.
Amman son Affan da banne a wurinta har su Jamil kance wa Affan na hannun daman Mamey.
Takanyi Dariya tace.
“Eh ɗin ai ya fiku nitsuwa”.
Muna zaune sai hamma Mamey keyi tare da miƙa da lumshe idonta hakane yasa tace mana.
Duk ta sallamemu saida safe tanajin bacci.
Ummi tace.
To.
Still Kuma sai mukaci gaba da hira.
Da ido muka bita ganin ta miƙa cikin sanyi tace.
“Kai zanje inyi bacci wlh wani irin bacci mai nauyi nakeji yana fuzgata tamkar zan faɗi.
Ni na shiga saida safenku”.
Allah ya bamu al’khairi mukace dukanmu kana ta shiga.
Tana shiga kwanta ko second uku batayi da kwanciya ba tayi bacci.
Mu kuwa muna gama hira muka watse.
To su Jalal ne ƙarshen fita ashe basu tasheta ta rufe ƙofarta ba a famintata kenan fa?”.
Ya ƙare mgnar yana kallon su Jamil.
Da sauri Jamil yace.
Eh.
Cikin sanyi ya kalli su Lamiɗo kana yaci gaba da cewa.
“Ina komawa ɗaki na kira Juwairiyya muka fara hira a waya kamar kullum.
To bayan mun gama
waya da Juwairiyya
har na kwanta sai na mike na nufi
ɗakin Mamey dan
inaso nayi mata magana a kan Juwairiyya fa tasanar wa mahaifin su maganar auren mu da ita, tun da lokacin takammala
karatun ta dan haka itama ta gayawa Abba na ayi batun aurenmu dan nima tuni lokacin na gama karatuna har na fara aiki.
Kuma a kwanakin ne aka bani sarautar Galadima wanda da mijin Gimbiya Saudatu ce mai matsayin to daya rasune Lamiɗo ya maida mulkin kaina.
A zatonshi ta hakane zaisa yaranshi bazasuyi faɗa da junaba tunda bazasuce ya baiwa wane ya hana waneba.
Ni a lokacin dagani har Mamey da Jabeer da baya ƙasar ma ba son wannan mulkin mukayiba bisa dole aka bani ita.
Sai kuma ya jingina bayanshi da kujera kana yaci gaba da cewa.

Ina isa bakin kofar
Mamey natura kofar da sallama nashiga ɗakinta.

Da sauri naja natsaya nan bakin kofar.
Can na hangi Mamey na kwance.
Bisa gado tana bacci da alamun baccin mai nauyi ne.
Hajiya mama kuwa na tsaye a kanta da wata iriyar shiga da tafi kama data bokaye ko ince matsafa.
Da mamaki nake kallon
Hajia Mama dake tsaye bakin gadon sanye da wasu irin jajayen kaya tun daga samanta har ƙasa,
kanta babu ko ɗan kwali
hannunta rike da wani ƙwarya.
Tana yayyafawa Mamey
wani ruwa dake cikin ƙwaryar tare da yin wasu surutai da sukafi kama da surkullen matsafa.

“Innalillahi wa’inanna ilaihirraji’un, nafurta da karfi.
Da sauri nanufo in da Hajia Mama’n ke tsaye cikin ruɗani da kiɗima ina faɗin.
Meye hakan Hajia Mama? me kike mata? me kike zuba mata a jiki haka?.
Dasauri tajuyo kaina tasaka hannunta cikin ƙwaryar taɗibo ruwan tashiga watsamin tana ƙara matsoni,
kaucewa nashiga yi ina matsowa in da Mamey take kwance kamar gawa ko matsi batayi,
itako Hajia Mama masoni tarikayi tana watsamin ruwan,
Baki na buɗe da karfi sabida wani irin masifeffen suka da naji duk inda ruwan ya taɓa a jikina yanayi.
Ƙara watsomin tayi wanda yasa na ƙara kaucewa da sauri tare da buɗe baki da nufin yin ihun zafin da nakeji da kuma fargabar halin da Mamey na ke ciki.
Sai kawai naji harshena yafurta Innalillahi wa’inanna ilaihirraji’un,wannan kalmar narika nanawata da karfi madadin inyi ihu.”

Ita kuwa Hajia Mama da sauri tajuya cikin alamun tsoron tonuwar asirinta.
dan lokacin dare baiyi nisa sosai ba misalin ƙarfe goma ne,
da gudu tafita a ɗaki dan jin yadda na kara sautin salatin da nake.

Ita kuwa Hajia Mama tana fita part ɗinta ta nufa direct bathroom ɗinta ta shiga gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi number’n bokan ta takira yana ɗagawa cikin haki da fargabar a bin da zaije ya da wo tace.
“Boka yanzu nafito daga ɗakin matarnan na samu tayi bacci kamar yadda kace, kuma na watsa mata ruwan bata farka a sai daifa wani yaganni lokacin danake yayyafa mata ruwan maganin nan babban ɗanta Galadiman Masarautar Joɗa kenan ya ganni”.
Wani irin dariya irin nasu na hatsabibai bokan yayi kana yace.
“Toh daya ganki me yakeyi? me kuma yake cewa?”.
cikin rawar baki da soron da ya ziyarce ta gudun kada ai kin ya ɓaci tace.
“Sunan Allah yaketa ambata salati yaketayi babu ko kakkautawa da wasu addu’o’i”.
Cikin ɗan tsagaita dariyar mugayen bokan yace
“To aiki kam zaici amma dai akwai nakasu aciki, amma kada kidamu yanzu shi yaron zamu rufemasa baki zai dauwama kurma ba mgna a bakinsa bazai iya yin maganaba bazai iya furta komai ba haka zai dauwama ba mgn saidai yayi ta mai-mai-ta abinda yake cewa.
Sannan daga nan tagwayen kuma zamu haɗa ɗaya da bin mata ɗaya shaye-shaye shi kuma babban kinga zai zama kamar Mahaukaci, shi kuma wancan Jabeer ɗin na gaya miki tun yana ƙaramin akwai sihirin da wani yayi mishi kada ki damu dashi bazai taɓa yin aureba har gaban abadan ko an mishi bazai zauna da matarba, kinga kenan duk sun zama suna da matsalar da dole baza’a basu mulkiba sai dai a bawa ɗanki Affan tunda kinga shi Imran ɗan ɗaya kishiyar taki shine ƙarami kan Affan.”
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Yauwa boka na gode ni dama fatana ɗana yayi mulki dan bana son mulkin ya bar ɗakina tunda dai kace min tabbas cikin yaran Habibullah ne mijin wani zai gaji kakansa sarauta.
Dariya yayi tare da cewa.
“Kada ki damu mulki na gareki da ɗanki”.
Wa iyazubillah kaɗan kenan daga sharrin tsinannun shaiɗanu maƙiya Allah da Manzonsa bokaye taɓaɓɓu masu sa mai binsu ya taɓe ya gaza sauri a ranar da muminai ke sauri a bisa siraɗi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button