GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Cikin rauni da azabar raɗaɗi murya na rawa yace.
“Mata! Mata zasu kasheni!”.
Cikin wani irin rauni da tsananin tausayi wani irin masifeffen kuka mai ƙarfi yan kwacewa Shatu.

Da sauri ta zame har ƙasa ta durƙusa.
Sabida wani irin azabebben tokara da guiwa da Jalal yayi mishi bisa tsakiyar bayanshi.
A take sai ga jini ta hancinsa da bakinsa.

Murya na rawa cike da rauni Shatu ta ɗago kanta.
Ta kalli Jalal dasu Khalid kana ta kalli jinin bakinshi daya ɗan tsallo ya taɓa farin gyalen jikinta.
Wani irin kukane mai cike da tsananin tausayi rauni ta fashe dashi tare da cewa.
“Ayyah Jalal dan Allah ku barshi kada ku kasheshi ku barshi dan Allah”.

A hankali Jalal ya ɗan tsaya yana maida wani irin azabebben numfashin haƙi.

Sheykh kuwa wani irin kallo mai cike da azabebben kishi ya watsawa Shatu.
Tare da sa tafin hannunshi ya tallabe haɓarshi.
Kana ya jingina kanshi da jikin bishiyar yana mai kallonsu.

Mamey kuwa itama zamewa tayi tanamai sakin kuka.
Ummi, Inna Amarya, Aunty Juwairiyya, Sara, dama duk sauran matan dake wurin wasu irin hawaye ne masu zafi suka tsastsafo musu.

Junainah kuwa zuwa tayi ta durƙushe gaban Ba’ana gefen Shatu cikin wani irin azabebben kuka mai cike da rauni tace.
“Wayyo Yah Ba’ana Dan Allah Adda Shatu ki hanasu dukanshi.”

Da ƙarfi Junainah ta faɗa jikin Shatu lokacin da Jalal yayi wani irin juyi ya kifawa Ba’ana wani irin masifeffen mari da tafin ƙafarsa.
Tare da cewa.
“Wato kai gaka shege har zaka sa hannu ka daki jamin soja”.
Wani irin azabebben karkarwa jikin Ba’ana ya farayi tamkar mazari.

Wani irin kuka mai azabar ciwo da cin rai Bukar da Bugulu suka saki sabida ganin yadda hukuma ke azabtar da Ba’ana tamkar zasu ɗauke ransa.

Cikin rauni murya na rawa ido na zubda hawaye Mamey tace.
“Jalaluddin ku bar dukanshi”.
A hankali Jalal ya koma baya ya zauna bisa dakalin ƙofar ɗakinsu Giɗi.
Sabida yasan muddin Mamey ta kirashi da sunanshi kai tsaye to abu ya ta’azzara gareta.
Domin Babana take kiranshi, sai gashi yau full name ɗinshi ta kira bama Jalal kawai ba.

Sai kuma ta kalli su Khalid kana ta juyo ta kalli Sheykh murya na rawa tace.
“Muhammad ka hanasu dukanshi”.
Cikin wani irin yanayi Sheykh ya ɗagawa su Khalid hannu.
Haka yasa suma suka koma gefen Jalal suka zauna suna haki da maida numfashi.

Shi kuwa Sheykh ido ya zubawa Shatu dake kuka tamkar ranta zai fita.

Gaba ɗaya wurin babu wanda rauni bai darsu bisa zuciyarsa ba.

Yah Jafar da Bappa kuwa tuni hawaye suke zubdawa.

Bukar da Bugulu kuwa da rarrafe suka iso gareshi.

Shi kuwa Ba’ana wani irin dogon numfashi mai cike da azaba rauni nadama ya fesar a wahalce kana a hankali ya fara yunƙurin tashi zaune.
Amman Ina ya kasa ganin hakane yasa Bukar yin sauri yasa hannunshin ya tallaboshi ya ɗagoshi.
Ya jingina bayan Ba’ana nan da kirjinsa.
Ya zama suna fuskantar Shatu dake kuka tamkar ranta zai bar gangar jikinta gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi.
Cikin wani irin rauni murya na rawa yace.
“Mata!”.
Da sauri ta ɗago jajayen idanunta ta ɗaurasu kanshi.
Wanda haka yasa ta saki wani sabon kuka, Junainah ma kukan ta saki da ƙarfi.
Shi kuwa Ba’ana hawaye na kwarya yana ƙore jinin hancinsa da bakinsa murya can ƙasan maƙoshi yace.
“Mata”.
Murya na rawa kuka na kumbe mata tace.
“Na’am Yah Ba’ana”.
Wani irin murmushi mai rauni yayi kana a hankali yace.
“Mata Ranar da nake tsoro tazo, ranar da na gaya miki zata iya ɓaci zata zo, gata yau tazo”.
Sai kuma ya ɗago ɗaya hannun nashi mai lafiyar ya sharce hawayensa, cikin sanyi ya jujjuya kanshi dake masifar mishi ciwo.
Ido ya zuba mata ganin yadda take kuka har numfashin ta na fizga.
A hankali yace.
“Shatu kin san son da nake miki gsky ne?”.
Cikin kuka tace.
“Na sani Yah Ba’ana na sani son da kake min gsky ne”.
Wani dogon ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe tare da cewa.
“Alhamdulillah”.
Sai kuma ga hawaye shar-shar bisa fuskarshi.

Cikin rauni yace.
“Ke kuma kin taɓa sona a ranki da gsky?”.
Kanta ta fara ɗan bugawa da ƙafar Sheykh dake gefenta.
Tare da cewa.
“Eh eh eh Yah Ba’ana na soka so na gsky na soka so irin wanda naso mu gudu tare mu tsira tare nasoka irin son da nake yiwa Yah Al’ameen sabida bana son irin wannan ranar tazo mana”.
Kanshi ya jujjuya kana cikin rauni yace.
“Shatu haka ƙaddarar rayuwata take.”

Sai kuma ya kalli Junainah a hankali yace.
“Junnu me yasa kike kuka, bakya son a kashenine”.
Cikin kuka tace.
“Bana son a kasheka Yah Ba’ana. Ina sonka kamar yadda nake son sun Yah Giɗi”.
A hankali ya sunkuyar da kanshi tare da sakin wani irin raunataccen kuka wanda saida Affan ya zubda hawaye.

Cikin sanyi yace.
“Mata ina ƴarmu?”.
Cikin wani irin rawan jiki hawaye na kwarya.
A hankali tasa hannunta ta amshi Afreen dake hannun Ummi.
Kana ta juyo da rarrafe tamkar ƙaramar yarinya ta iso gabanshi cikin rawan murya tace.
“Gata nan Yah Ba’ana”.

Wani irin murmushi mai yelwa yayi wanda saida fararen haƙoranshi suka fito ras.
Da idonshi ya nuna mata cinyarshi.
Cikin kuka ta sunkuyo ta kwantar mishi da Afreen bisa cinyarshi.

Kana ta kife kanta cikin cinyoyinta ta saki kuka.

Shima kukan ya saki mai rauni.
Kana yasa tafin hannunshi ya shafi kan tattausan suman gashin Afreen hawayenshi na kwarya suna ɗiga kan goshinta.
A hankali yace.
“Masha Allah, Allah ya raya mana ita bisa imani al’farma Annabi da al’ƙur’ani Allah yasa mahaddaciyar al’ƙur’ani ce, ya azur tata da miji na gari”.
Karo na forko da Sheykh ya motsa lips ɗin shi a hankali yace.
“Amin ya Allah”. Sabida daɗin Addu’ar da akayiwa ƴarshi.

Itama Shatu cikin kuka tace.
“Amin thumma Amin”.
Sai kuma ta ɗago kanta a hankali jin yana cewa.
“Naji lbrin Ummey ta tuno baya ta gane ahlinta ance min ma wai ɗan ta ne ya aureki ko?”.
Ina ta kasa mgn sai kuka,
Ummeyn ce ta sharce hawayenta a hankali tace.
“Eh Ba’ana na tuno baya, na gano ahlina Allah ya saka da al’khairi ya biyaka da mafi kyawun sakamako”.
Cikin rauni yace.
“Amin Amin Ummey”.
Sai kuma ya kalli Bappa dake ta kuka a hankali yace.
“Bappa kana kukan baka cika min al’ƙawarin da kayi bane?”.
Da sauri Bappa ya gyaɗa kai alamar eh.
Kai ya jujjuya kana a hankali yace.
“Ba laifinka bane, ƙudirin ubangijine ba gashi yanzu Ɗiyar Shatu ce a cinyata, wani bazai haifi ɗan wani ba ai. Ni na yafe muku yanzu na yarda na gane komai nufin Allah ne.
Sai dai kuma ina neman yafiyarku al’ummar Rugar Bani baki ɗaya busa duk wata cutarwa da nayi muku.”
Sai ya kuma kalli ɗaya daga cikin yaransa da suka shigo tare a hankali yace.
“Koda bana da halin muku bayani, ga Droo zai muku dukkan bayanin abinda ke tafe, gaba ɗaya na mishi bayanin komai kafin mu taho”.
Sai kuma yayi shiru jin duk anyi shiru ana jinshi sai shessheƙan kukan Shatu dake tashi.
Kalato yawun bakinshi yayi ya haɗiye sabida wata irin azabebben ƙishin da yakeji tamkar zai kashesa.

A hankali ya kalli Ummey cikin rauni yace.
“Ummey ƙishi nakeji ki sanmin ruwa”.
Yayi mgnar yana kallon Shatu data zuba mishi ido da sauri.
Ya sani ta tuno bayanin daya taɓa yi matane na cewa in an bashi ruwa yasha zai ɓace zai tsiri.

Haƙƙun kuwa itama abinda ta tuno ɗin kenan sai dai bata saniba ya kakkarya duk waɗan nan abubuwan.
Cikin rani yace.
“Shatu Insha”. Yace
lokacin daya amshi kofin ruwan da Ummey ta miƙo mishi.
Shiru batayi mgna ba sai kukanta daya ƙaru.

Sheykh kuwa zuwa yanzu Allah ne kaɗai yasan abin da yakeji a zuciyarsa sabida azabar zafin kishi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button