GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Jin kakan nashi ya sake hannunshi da kalaman da yake jero mishine yasa ya ɗan kalleshi a hankali ya kuma sunkuyar da kanshi.
Sai ya kuma ɗan kalli Sarkin tare dayin mgna.
“Mulki yana da nauyi mai girmi Ni kuwa baya cikin tsarin jadawalin ababen buƙata ko sha’awa a rayuwata,”.
Murmushi Lamiɗo yayi tare da cewa.
“Ba sai lallai abinda mutun keso ke samu ba, bakuma dole ka rasa abinda baka soba”.
Ganin kakan nashi yaci gaba da tafiya ne yasa shima ya yaci gaba da tafiya.

Inda fadawanshi ke biye dashi a baya.

Yayinda fadawan Maimartaba kuwa suka tsaya a bakin sashin sa.

Sunyi tafiya mai nisa kaɗan kafin suka ratso ta gaban sashinsu mai azabar girma da kyau sashine mai ɗauke da part-part masu tarin yawa da girma wanda tsakanin ko wannensu da ƴar tazara sosaima.

A hankali ya ɗago hannunshi daga cikin babbar rigarsa da zazzafar al’kebbarsa ta rufe,
ɗan ɗaga musu hannunshi yayi alamun su tsaya daga nan.
Cikin abinda bai gaza 18 second ba duk suka rusuna ba tare da sun ƙara koda taku ɗaɗɗaya ba, kusan a tare suke cewa.
“Takarwarka lafiya ɗan Baban yaya Habibullah jikin Sarki Nuruddeen, jika ga sarki musulmai Jalaluddin”.
A hankali ya kuma ɗaga musu hannunshi alamun ya isa haka, dan shi dai Allah ya sani har ranshi baya jin daɗi da son wannan kirare-kiraren dan yayi imani da Allah zasu iya sawa ɗan adam ɗagawa da jin kanshi shi wani abune, zasu iya sa mutun yaji kansa a matsayin wani sarki mai iko bayan kuma babu wani Sarki sai Allah.

Yana tsoron ɗagawa ta samu mazauni a zuciyarshi, sam baya son wannan kirare-kiraren na zamanin jahiliyya ina dalili kana mutum ɗan Adam mai daraja azo ana wani ce maka toron giwa ko tozon raƙumi ko dokin ƙarfe yaya Allah ya karramaka yayika ɗan Adam ka bari na ƙasa da kai suna suffantaka da dabbobi.
A hankali yace.
“Ya isa, duk kuje kowa yayi uzurin gabansa in inada buƙatar ku zan nemeku”.
Shiru sukayi tare da baje manyan rigunansu suka zauna a inda ya dakatar da suɗin.
Kana sukace.
“An gama”.
Shi kuwa a hankali yake taku cikin shigarsa da tafi kama data limamen harami.

A hankali yake taku, har ya iso bakin ƙofar shiga side ɗinsa inda a nan dogari mai tsare mashigar sashinsa sarkin ƙofarsa ke tsaye.
Tuni Sarkin ƙofa ya miƙe yasa hannu zai buɗe mishi ƙofar kenan sai ya kuma ɗan rusunar da kanshi,
Ganin Jamil ya rigashi kai hannunshi ya buɗe ƙofar cikin salonsa na raha ya nunawa Hamman nashi ƙofar tare da cewa.
“Sheykh Dr Malam Hamma Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero Joɗa GARKUWA barka da yamma”.
Kanshi ya kauda daga kallon ƙanni nashi, sannan ya kutsa kai ciki,
da sauri shima Jamil ya mara mishi baya,
Cikin wani haɗeɗɗen corridor mai fitinenne ƙamshi da azabebben sanyi suke tafiya a hankali.

Tafiya kaɗan sukayi sai gasu cikin wani tamfatsen falo na al’farma da more rayuwa,
ɗaya daga cikin lumtsuma-lumtsuman kujerun kilisai na manyan sarakunan dake falon ya zauna a hankali.

Ido ya ɗago ya watsa ƙanin nashi su, cikin sauri Jamil yayi ƙasa da kanshi tare da cewa.
“Na tuba Hamma kayi magana ina tsoron hukunci da idanunka gwara kamin duka kon ka haɗani da wannan saggamemen na bakin ƙofar kan nan ya dakani kawai in huta”.
Kanshi ya kawar Cikin harshen larabci yace.
“Ban gankaba a masallaci”.
Da sauri ya durƙuso gaban Hamman nashi cikin yin wuƙi-wuƙi da idanu cikin sanyi yace.
“Ana Aspet ya Akhi, a matsallacin ƙofar gidansu, Khadija nai sallan jumma’ar”.
Kanshi ya gyaɗa kana ya kauda kanshi ya fuskanci wani katon majigi dake liƙe a jikin ginin yana fuskarta kujerar da yake zaune a kai.
Majigine dake ɗauke da full Qura’an, a hankali yake karatun cikin sassanyan murya.
Ganin hakane yasa Jamil ɗan rusuna duk da yasan ba amsa zai samuba cikin sanyi yace.
“Hajia Mama tana son ganinka”.
Kanshi kawai ya gyaɗa yaci gaba da karatun shi.
Ganin hakan yasa Jamil ya juya ya fita. Shikuwa Sheykh yaci gaba da karatunshi, kusan awa ɗaya kana ya shiga Bedroom.

Shine bai fitoba sai lokacin da sallan la’asar ta gabato, jin an kira sallane, yasa ya shiga ya sabunta al’wala kana ya fito ba kowa a wurin sun watse kemar yadda ya umsrcesu.
Sai can bakin mafita ya samu mutun huɗu, yana tafe fadawanshi na biye dashi wanda suma sunyi al’walan.

Jamil kuwa daga sashin Hajia Mama ya fito da nufin zaije side ɗinsu yayi al’wala.

A harabar gidan yayi kiciɓis da abokin tagwaicinsa wato Jalal, cikin sanyi ya kalli yadda Jalal ke zagaye da fadawa yana tafiya da yanayinsa da muddin zaka yanke mishi hukunci da ganin zahiri zakace cikekken ɗan iskane, sai dai a baɗinin ba haka abin yakeba.

Kekyawa ne shima dan shi yana ɗibin kamanni da Hamma Jabeer ɗin nasu sosai saɓanin Jamil da yafi kama da Babban yayansu, Barrister Jafar Habibullah Nuruddeen Bubayero.

Tafiya yake cikin shigar tsamari zamani, wondon a saɓule har kana iya hango boxes ɗinshi, kana ga wani irin kafirin aski da yayi mai ɗaukar hankali.
sam a rayuwarsa shi baya ta’ammali da manyan kaya,
Baya tsoro ko shayin ko shakkar kowa a duniya sai Hammansun kaɗai.
tafe yake bayinshi na biye dashi a baya, da wasu kolabe a hannunsu, cikin tsare fuska Jamil yace.
“Kai ku tsaya, kolaben menene wannan a hannunku?”.
Juyowa yayi a zafafe cikin halin faɗa yace.
“Kwalaben Giyane ko kanada maganne Akukkuturu?.”
Da azaban ƙarfi da tsoro Jamil ya zazzaro ido cikin ɗaga murya yace.
“Kwala ben giya a gidannan Jalal kasan abinda kake cewa kuwa? Kwalaben giya a Masarautar Joɗa”.
Ya juyo da masifa kenan yayi arba da Hamman nasu,
shiru yayi tare da yin ƙasa da kanshi, jiki a mace.

Shi kuwa Sheykh Jabeer idanu ya zuba mishi na wasu yan daƙiƙu kana ya juya ya nufi hanyar da zata sadashi da ƙofar tafiya masallacin Masarautar tasu ba tare fitar nan bisa dressing mirror suka ajiyesu kana suka juya suka fita.

Shi kuwa al’wala yayi ya nufi masallacin.

Ƙarfe tara dai-dai na dare. Sheykh Jabeer, ne zaune a bisa wani tattausan carpet mai azabar taushi,
Wata Hamshaƙiyar Gimbiyace mai cikan iko da muƙami, mulki, iko, cikin wani irin kallo mai cike da kulawa tasa hannu ta ɗauki ɗaya daga cikin nonon inabi dake cikin wani kekyawan tray dake gabanta miƙa mishi tayi tare da cewa
“Jabeer Yaushene tafiyar taku?.”
Tankwashe kanshi yayi bisa kafaɗunshi kana a hankali ya ɗan kalleta tare da motsa laɓɓanshi a hankali yace.
“jibi”.
ya faɗi mgnar a gajarce, gyara kishingiɗarta tayi bisa kilisan tum-tum dake gefenta,
Cikin kulawa tace.
“Da Umaymah zakuje ne?”.
Kanshi ya jujjuya mata alamun a a.
Kanta ta rausayar cikin ƙasaita tace.
“Naga kamar bacci kakeji Saida safe”.
Kanshi ya gyaɗa kana cikin girmamawa yace.
“Allah ya bamu al’khairi”.
Amin tace, shi kuwa daga nan ya fita ya tafi.

Koda ya koma sashinsa. A falo bakin ƙofar ya samu Jakadiya, tana ganinshi ta ɗan rusuna duk da tasan yana hanata hakan a hankali tace.
“Akarmakallahu, Umaymah ce take biɗar mgna da kai, ta kirayi layinka ba’a ɗagawa, shine tace in kawo maka wayar”.
Kanshi ya ɗan sunkiyar a hankali yace.
“Ummi kice mata tayi hakuri saida safe”.
Cikin mamaki jakadiya tace.
“Lafiya dai ko Sheykh?”.
Kanshi ya gyaɗa mata alamar eh lfy.
“To ba laifi zan gaya mata”.
Daga nan ta juya ta koma sashinta.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, daga bakin ƙofa ya dakatar da bayinshi.
Kana cikin nitsuwa ya kallesu tare da cewa.
“Sarkin ƙofar ka janye bayin dake bina da bin Jalal da Jamil, kaima ka koma can sashunku, ba’a buƙatar bibikon nan, in inada buƙatar ku Ummi zata sanar muku.”
Ciki girmamawa sukace.
“To Sheykh”. daga nan ya juya ya nufi ciki.
Su kuma suka juya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button