GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

A nan a gabanshi a gaban mahaifinshi. A gaban dubban al’ummar fulani makiyaya daketa tsastsafo tako wani sashi na duniya, a kuma gaban Lamiɗo da tawagarsa hakama Jalaluddin da tawagarsa.

Aka ɗaura auren Muhammad Jabeer da Aysha. Bisa koyarwan addinin Musulunci.

Sosai su Jalal, Jamil, Hashim, Haroon, Sulaiman. Sukayi mamakin wannan aure na ba zata. Ba zato ba tsammani.
Bayan an gama dai-dai-ta komai an ɗaura auren ne, kuma.
Lamiɗo ya kalli Arɗo Bani, cikin girma da ƙasaita yace.
“Yanzu zai tafi da matarshi.”
Cikin sanyi da al’hini Bappa yace.
“Allah rene yanzu kuma!?”.
Galadima ne ya amshi zancen da cewa.
“Haƙƙun yanzu zamu tafi da ita!”.
Arɗo Bani ne yayi murmushi mai cike da jin daɗin yace.
“To ba laifi ai, muje a fito muku da ita”.
Shi kuwa Bappa ido ya zuba musu.
Dan shi a zatonshi ba yau zasu tafin mishi da Shatunsa ba.

Nan duk suka ɗunguzuma, suka shiga motocin. suka nufi ƙofar gidansu Shatu.

Ya Salmanu kuwa, tuni ya shiga cikin gidan su.
Ya shiga ɗakinshi yana ta kuka kamar yaro. Bai tsamci haka abin kan iya juyewa ba, Ba’ana ya rasa Shatu shima ya rasata.

Suna isa ƙofar gidansu, duk motocin suka tsaya.
A hankali Bappa da Arɗo Bani suka kutsa kansu cikin gidan.

A tsakar gidan suka samu.
Shatu na zaune dan dawowarta kenan, hannunta tasa ta tallabe haɓarta ta zubawa su Junainah ido, shigowarta gida kenan daga dawowarta.
Cikin Ɓadamaya su Binto suka shigo gidan a guje suna ce mata wai an ɗaura aurenta da ɗan sarkin da akayi gasar Shaɗi dashi.
Jin hakane yasata yin murmushi tare sauƙe dogon ajiyan zuciya na gajiyar tafiyar da tayi, ido ta lumshe tare da cewa.
“Auren kuma wasane, da zai zama an aura min wani wanda ba’a san halinshi ba, ko ƴar tsana ma ai ba’a aurar da ita a hakaba bare ni”.
Ta faɗi mgnar cikin fargaban ganin yadda suketa rantse mata. Duk da bawai ta yarda da zancensu bane. Junainah kuwa dariya takeyi tare da ɗan tsalle-tsallenta tana cewa.
“Yeeh Auren Addana yazo, zanyi gayyan fati muyi gaɗa”.

Cikin zuba musu ido, ta zauna gefen, Ummey dake ta Binta da ido, cikin sanyi tace.
“Ummey na dawo! Ya jikin naki!?.”
Da sauri ta gyara zamanta tare da zubawa Ummey ido, cikin mamaki take kallonta ganin idanunta nata zubda hawaye ne, yasata cikin ruɗani da tashin hankali da fargabar abinda ke shirin faruwa da ita da rayuwarta.
A kiɗime tace.
“Ummey meya sameki? meya saki kuka? Jikin ne yake miki ciwo?.”
Sam Ummey bata iya mgna ba, sai kukan da takeyi,
hakanne yasa zuciyar Shatu karaya, cikin rauni wasu hawaye masu ɗumi suka fara tsiyayo mata.
Hakan ya ƙara ingiza kukan Ummey hakama,
Junainah sai ta raɓa gefensu tayi, zurui a zatonta aure abun daɗi ne ba kukaba to gashi taga su kuma kuka sukeyi.
Sosai Shatu takeyin kuka mai tarin dalilai.
Suna isa Bappa yasa hannunshi ya kamo nata, cikin sanyi yace.
“Taso kizo”.
Ido cike da hawaye ta mike tsaye bisa umarnin Bappa.
Shi kuwa Bappa cikin sanyi ya kalli Ummey da Junainah yace.
“Kada kuyi kuka, kuyi mata addu’o’in samun nasara a cikin wannan al’amari, muyi mata fatan aurenta ya zamo haske ne a rayuwarsa shi mijin da ahlinshin baki daya, fatanmu aurenta ya zamo ƙungiyar da zata jawo gskya cikin raminda aka binneta ya fito da ita kowa ya gani.”
Shiru Ummey tayi sai hawayen da suke kwaranya.
Hakama Shatu hawayenta wani na korar wani.
Ita kuwa Junainah faɗawa jikin Ummey tayi sukaci gaba da zubda hawaye.

Bappa kuwa hannunta yaja suka juya suna nufi hanyar fita.
Da kayanta na ɗazu wanda taje Genaral Hospital Ɓadawaya dasu, hatta hand bag ɗinta na rataye a kafaɗarta wayarta na ciki.

Cikin mamaki take bin bayan Bappa, tare da yin taku a hankali tana bin bayanshi yadda yake jan hannunta.
Arɗo Bani kuma na biye dasu a baya.

Suna fitowa ƙofar gidan, Haroon da Jalal suka juyo suka kalli juna,
Cikin tarin mamakin ganin kamar yarinyar ɗazuce.

Shi kuwa Sheykh Jabeer yana zaune cikin motar, shi ɗaya dan duk sun fita.
Da sauri ya dafe saitin ƙahon zuciyarshi jin ta tsananta bugawar da yakeyi.
A hankali ya maida bayanshi ya jingina da sit ɗin tare da rufe idonshi.
Yana mai jin sanyin A/C na ratsa mishi jiki da jini da zuciya.
Amman duk da haka zuface ke tsastsafo mishi a jikinshi sabida bugun da Zuciyarshi keyi ya wuce misalin.

A hankali ya juya kanshi ya kalli gefen hagunshi inda yaga motar Jadda da kuma Dr Aliyu ne da Barrister Kamal ke jere a wurin.

Bappa kuwa a hankali yake taku, yana nufo inda Lamiɗo ke tsaye Dogari na riƙe masa da laima, Ɗanzagi da fadawa na zube a kasa.

Ita kuwa Shatu cikin rawan jikin jin idanun mutane na yawo a jikinta dan ma Allah yasa akwai niƙab a fuskarta.
Take bin bayanshi. Shi kuwa Sheykh Jabeer yadda suke ƙara matso inda yake haka bugun zuciyarshin keta tsananta.
Suna isa gaban Lamiɗo Bappa ya miƙawa Lamiɗo hannunta cikin sanyi da nitsuwa da taushin lafazi yace.
“Allah rene, ga Aishatu matar Muhammad Jabeer.
Gata amana bisa jagoranci ka, nasabarka da yardarka.
Da kamala da nitsuwa da na gani a fuskar yaron yasa naji ƙarfin guiwar baku aurenta.
Ba tare da fargaba ba, yanzu kaine kaka kuma jagora a gareta”.
Sai ya kuma nuna Barrister Kamal da shima yana cikin wakilai, shi a zatonsa ma shine mahaifin Jabeer cikin sanyi yace.
“Kai kuma kaine matsayin mahaifi a gareta ku zame mata dangin ta data rasa, naso ace da mata a masu ɗaukanta, dan in danƙa amanarta a hannun macce yar uwarta.
Amman ba komai, na baku amanarta dan Allah kada a cutar da ita, domin nima ta kasance amanace a uwurina, domin ƴaƴan mu da muka haifama amanace Allah ya bamu kuma abun kiyayewa, bare kuma ɗiya irin Shatu ɗiyace da take da nasabobi masu yawa a gareni”.
Cikin gamsuwa Lamiɗo yasa hannunshi ya amshi hannunta daketa karkarwa, tuni niƙab ɗin fuskarta ya jiƙe jilak da ruwan hawaye.

Cikin Dattaku Lamiɗo yace.
“In sha Allah zan kula da dukkan lamuranta tamkar yadda nake kula dashi Jabeer, kuma kada ka damu akwai masu meye mata gurbin uwa ƙanwa yaya dama duk danginta a cikin masarauta Joɗo, baƙoma baya kukan maraici bare kuma, matar sashin jinina”.
Cikin sanyi da wasu hawaye Bappa yace.
“To Ngd matuƙa”.
Arɗo Bani ne ya dafashi tare da cewa.
“Ka sanya mata al’barka a cikin aurenta ba zubda hawaye ba.”
Sosai Haroon ya zuba mata ido.
Shi kuwa Sheykh Jabeer da mamaki yake kallon Bappa dake zubda hawaye.

A hankali su Bappa suka ɗan ja da baya.

Shi kuwa Lamiɗo ya juya ya nufi motar riƙe da hannunta.
Haroon ne yayi saurin buɗe musu marfin motar, suka nufoshi gadan-gadan.
Jalal kuwa ido ya zubawa yatsun hannunta da Lamiɗo ke riƙe dashi.

Shi kuwa Jabeer idonshi ya rufe da ƙarfi. Sai kuma ya buɗesu, dai-dai lokacin Lamiɗo ya kawota bakin ƙofar motar tare da cewa.
“Mamana kiyi bismillah ki shiga da ƙafar dama”.
Cikin shessheƙan kuka ta gyaɗa kai tare da yin bisimilla kana ta ɗan sunkuyo, sai kuma kukan ya kubce mata.
Shi kuwa Jabeer da sauri ya buɗe marfin motar ta gefen hagunshi. Kamar gilmawar walƙiya ya fita cikin motar.
Dai-dai lokacin da Shatu tasa ƙafarta ciki.
da sauri yasa hannunshi ya buɗe motar Jadda tare da shigewa ciki yaja marfin ya rufe sabida ji yayi zuciyarshi zatayi bindiga, wani irin dogon ajiyan zuciya ya sauƙe mai ƙarfi.

Ita kuwa Shatu, a hankali ta shiga ta zauna, don batama lura da shi bane tabbas dai taga mutun ya fita cikin motar.
Tana shiga Haroon ya maida marfin ya rufe
Shida Lamiɗo suka koma sit ɗin bayan wannan sabida su a zatonsu Jabeer na ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button