GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Kiss ya sakar mata a goshi kana a hankali yace.
“Toh kafin wani jinin yazone kuma ciki ya shiga”.
Cike da al’hini tace.
“Yah Sheykh ban ganeba”.
Cikin tsananin jin daɗi yace.
“Allah kuwa Aish kinada ciki, na kimanin watanni uku har ya shiga na huɗu, yana ma gab da fara motsi”.

Da sauri ta ɗan ja da baya ɗage rigarta sama kaɗan tayi tare da zubawa cikinta ido, ya ilahi ya mujibadda’awati ta faɗa hawaye na kwaranyo mata murya na rawa tace.
“Innalillahi Dr.
Afreen na da watanta biyar kacal kuma ace ina da ciki, yarinyata zata sha wuya, na shiga uku”.
Da sauri ya jawota jikinshi ya ruggumeta tsam cikin kwantar mata da hankali yace.

“Baki shiga uku ba Aish, al’janna zaki shiga da izinin Ubangiji, aihuwa rahamace Shatu, wasu suna nema ido a rufema Allah bai basuba mu kuma ya bamu.
Kuma Alhamdulillah batun Afreen nima da fari hankalina ya tashi so da naga.
Ba abinda nonon yayi mata sai ban damuba, ni yamin ma ko kin sani kawai kina ɓoye min ne, sabida kada in sani in nuna farin cikina har Magauta su gane shiyasa baƙi in gaya miki na gane”.
Cikin zubda hawaye tace.

“Yah Sheykh daga haihuwa da kwana arba’in fa kenan na samu ciki”.

Dariya mai sauti yayi tare da cewa.
“Ance miki ni ɗin wasane, bugu ɗaya nakeyi ƙollo ke shiga raga.
Gashi kema ɗin ma zalamemmiyace da an baki saiki karɓa.
Toh mu godewa Allah kinji ko Mar’atussaliha, muyi farin ciki da abinda Allah ya azurtamu dashi, kiyi Sujjadar godiyar Allah kiyi hamdala sai mu roƙi Allah yasa tagwaye ne, ina kina son ƴan biyu?”

Cikin jin sanyi da daɗi tace.
“Uhumm sosai ma kuwa Yah Sheykh”.

Kai ya ɗan ronƙofa ya sumbaci lips ɗin ta kana yace.
“Toh Allah ya bamu”.
Amin Amin tace.
Kana yaje yayi al’wala ya wuce masallaci.
Ita kuma ta ɗauki Afreen ta wuce da ita.
A falo ta samu Junainah ta miƙa mata ita kana ta wuce.

Bayan kusan wata biyu kenan lokacin cikin ya cika wata biyar.
Sosai ya ɗan fito cas sai kuma tayi yar ƙiba.
Afreen kuwa yanzu tana dafa abu ta miƙe tsaye.

Aurensu Jalal saura wata 4.
Alhamdulillah tana fama da karatunta, kuma wanda yanzu suke shekarar ƙarshe ita da Rafi’a shiyasa ma aka kai bikin da nisa dan Rafi’a ta ida.

Tana ruggume da Afreen ta shiga Part ɗin Mamey, dawowarta daga makaranta kenan.
Da sauri Mamey tasa hannu.
Ta amshe Afreen sai kuma ta kalli Sara dake biye da ita a baya tace.

“A’a Sara ya haka, kin barta da jaka da wannan lukutar ƴar tasu”.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Wlh Mamey Afreen na min son inna a soka asha jinin jikinka, wai sai taƙi Sara ta amsheta dole sai ni zan riƙeta”.
Ta ƙare mgnar tana dungure kanta.
Dariya ta karketa kanar tasan abinda akace..ita kuwa Mamey da sauri tace.
“Toh Sara ɗauko mata abinci.”

To tace kana taje ta ɗauko mata.
Bayan ta ɗauko ta ɗauki nata ta tafi.
Ita kuwa Mamey serilac ɗin Afreen ta dama kana ta fara bata.
Tana bata tana kallon Shatu.
Sai kuma ta ɗan yi gyaran murya tare da cewa.
“Da sauƙi ma ai duk da wahalan karatun da rainon bai sa kin rameba”.

Kanta ta ɗan sunkuyar ta kalli cikinta cikin yin ƙasa da murya tace.
“Toh ba cewa yayi wai inada cikiba”.

Da sauri Mamey ta danne dariyarta tare da cewa.
“Wai ne ma Shatu? Har yanzu a wai yake?”.

Cikin ɗan jin kunya tace.
“Uhum”.
Nan dai sukayi ta hira daga bisani ta miƙe ta koma Part ɗin ta.

Alhamdulillah shirye-shiryen aure nata kan-kama.
Tare da shirin naɗin sarauta.
Tako ina tako wani lungun da saƙon masarautun gargajiya na Arewacin Nigeria da kudancin, dama maƙotan mu kamarsu Niger, Cameroon, Chadi. Da dai sauransu duk takardar gayyatar naɗin sarautar sabon sarkin masarautar Joɗa ya riskesu.
Shiri iya shiri akewa bikin da yake haɗe da ɗaurin auren mutane shida.

Cikin Shatu kuwa ya girma ya fito ras, sabida yayi watanni takwas.
Afreen kuwa Alhamdulillah tana gudu ko ina yanzu ga gwarancinta ras.
Watanninta goma sha ɗaya amman in ka ganta zakayi zaton Yar watanni goma sha biyar ne.

Alhamdulillah su Shatu sun kammala karatun su lfy, komai yayi yadda ake buƙata.

Hajia Mama kuwa duniya tayi mata atishawar tsaki.
Sabida kuturta ya kuma shiga yatsunta na tsuntsayen.

A hankali take tafiya Afreen na riƙe da yatsarta.
Tana ta gwaranci.
“Abba! Abba! Abba!”.
Murmushi yayi tare da buɗe mata hannunshi da sauri ta tsaki yatsar Shatu ta nufi inda Sheykh ke tsaye, cikin tarin farin ciki yace.
“Oyoyo Mamina”.
Kana ya ɗagata sama.
Murmushi Affan yayi tare da cewa.
“Afreen sarkin wayo ita kowa natane”.
Jamil ne yace.
“Hmmmm ai ni jiya ta bani mmki.
Wai Ance Abbanmu na kiranta zai bata sweet wai sai tace.
“Bata so Abbanta a kawo mata”.
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
“Kuma daga baya ta bishi da gudu tana Abba cha ciwiut”.

Murmushi Sheykh yayi kana ya sauƙeta, tare da kallon Shatu dake zaune ta tasa cikinta gaba.
Cikin wasa ya kalli Jalal daya shigo yanzu yace.
“Jalal ko dai zamu ɗaga bikin kun nanne sai Aish ta haihu zatafi sakewa”.

Da sauri ya katse wayar da yakeyi da Hibba tare da cewa.

“A’a me yayi zafi, tasha zamanta a ɗakinta mun hutasshe ta zuwa bikin”.

Jamil kuwa kwaɓe fuska yayi tare da cewa.
“Uhumm wai a ɗaga”.

Dariya Affan yayi tare da kallon Sheykh dake musu murmushin wasa nan dai sukaci gaba da tattaunawa kan bikin.

Alhamdulillah yau bikinsu Jalal saura mako ɗaya rak.
Komai ya kankama.
Tuni baƙi sun fara cika masarautar Joɗa tako wani yanki.
Hotels din Ɓadamaya Lamiɗo da Sheykh sun kama fiye da rabinsu sabida, sauƙar baƙin da suke tsastsafowa tako wani yanki.

Yau jumma’a wanda ya kama sauran kwana bakwai cin a nawa Sheykh rawani jumma’a mai zuwa kenan.
Wanda ya kama kuma ranar za’a ɗaura aurensu Jalal tuni su Umaymah da tawagarta sun iso.

Tun da safe kuwa yau Shatu ta tashi da ciwon mara, kaɗan-kaɗan.

A haka take ta sabgoginta, sabida tana tare da amare duka uku.

Sha ɗaya dai-dai na safe Allah ya sauƙeta lfy ta haifi ɗanta na miji santalele.

Farincikin a ahlin Sitti ba’a mgn.
Bayan an gama kimtsa mai jego da jaririnta kato fari ƙal dashi.

Suna kwance Sheykh ya shigo.
Cikin tarin farin ciki dan yana gidan Malam Abubakar ne Yah Jafar ya kirashi ya masa al’bishir.

Cikin jin daɗi ya zauna gefen Shatu.
Tare da miƙawa Safiyyah hannu ta miƙa mishi jaririn murya cike da zallan farin ciki yace.
“Alhamdulillah masha Allah. Allah na gode maka, da wannan kyauta da kaimin. Ya Allah kasa baɗi iwar haka mu samu tagwaye”.
Dariya sukayi baki ɗayansu ganin yadda Shatu ta zaro idonta cikin alamun tsoron tace.
“Wayyoooooooo Allah na. Yah Sheykh sai kace wata inji”.
Aunty Rahma ce tace.
“Ato ai da alamar hakan zakuyi tunda gashi a shekara ɗaya an samo irin tagwayen Nana Faɗima”.
Ummi ce dake gefe tana fifitawa Shatu tea tace.

“Ko ƴan ukune Allah ya kawosu akwai masu tayaki rainon su.
Inji gashi yanzu Afreen tunda aka yayate, sai dai tazo ta leƙaki tayi gaba abinta”.
Da sauri yace.
“Uhumm yauwa Ummi na gaya mata dai”.
Ya ƙare mgnar yana sumbatar goshin yaron cikin tsananin farin cikin da son yaron.
Sai kuma ya kalli Mamey dake shigowa yace.
“Mamey da waye yake kamane?”.

Matsowa gabanshi tayi ta kalli fuskar jaririn kana tasa hannunta ta tallabo tashi fuskar.
Cikin jin daɗi tace.
“Da kai yake kama”.
Cike da jin daɗi yace.
“Alhamdulillah”.

Nanfa akaci gaba da hidima.

Yau kwana biyu da haihuwar Shatu.
Zaune yake agaban Mamey da Abbanshi, kai ya ɗan ɗago ya kalli Abbanshi tare da cewa.
“Ummm Abba nace wanne suna za’a sawa yaron?”.
Murmushi mai cike da jin daɗi Abba yayi tare da cewa.
“Na baka zaɓi zaɓawa ɗanka sunan da kafi so”.
Murmushi mai cike da jin daɗi yayi tare da cewa.
“Mamey kefa, ko Jadda kikeso inyi mai suna”.
Yayi mgnar cikin raha.
Da sauri tace.
“Mutun da ɗan shi mun baka damarka a matsayinka na uba”.
Kanshi ya sunkuyar tare da cewa.
“Ngd matuƙa da wannan damar”.
Daga nan ya sallamesu ya miƙe ya fita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button