GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ta ƙareshe mgnar tana miƙewa zata fita.
A hankali Ummi tace.
“Kiyi haƙuri JUWAIRIYYA KINSAN abubuwan sai a hankali kada ki damu, kin san mutun in yanada ƴar matsala wasu lokutan ma, ba yin kanta bane”.
Uhum kawai Juwairiyya tace ta fita.

Sukuwa sukaci gaba da hirarsu.
Washe gari Hajia Mama ta aiko hadimanta su kawowa Sheykh dambun nama.
Suna shiga tace, suje su rabashi an basu.

Dama Ummi kam tasan za’ayi hakan.
Sheykh dake shigowa kuwa cewa yayi.
“Ke aka bawa ne da zaki kyautar dashi”.
Fuska ta ɗan yamutsa tare da cewa.
“Bazaka ci bane”.

Amsar kwanon yayi a hannun Ummi tare da cewa.
“Kuje kuce ngd”.

Daga nan ya nufi ɗauki shi.
Da sauri ta miƙe tabi bayanshi.

Yana shiga ya ajiye kwanon kan Bedside drower’n.
Ɗauke kwanon tayi tare da cewa.
“Dan Allah dan Annabi kada kaci, ka barshi, in dambun kakeso ai nayi maka”.
Taɓe baki yayi tare da cewa.
“Nata yafi daɗi akan naki ai”.
Da sauri ta kalleshi idonta na cicciko da hawaye.
Juyawa tayi ta fita da kwanon.
“In kinje kin boye kizo”.
Yace mata, to tace.
Ai kuwa taje ta zubar dashi ta bawa Saratu kwanon tace ta maida mata.

A zaune ta sameshi da wata leda a gabanshi.
Nuna mata ledar yayi tare da cewa.
“Gashi ni na mance tun zuwanmu Umrah Aunty Hafsat da Umaymah suka bada sukace in baki”.

Sunkuyowa tayi ta ɗauki ledar tare da cewa.
“Ngd matuƙa Allah ya biya musu buƙatunsu”.

“Amin Amin”. Yace.
Juyawa tayi ta fita.

Shi kuwa wayarshi ya zaro yabi bayan kiranda Haroon yaketa mishi.

Ita kuwa Aysha tana shiga ɗakinta ta buɗe ledar.
Turarukane masu kyau da ƙamshi.
Harda setin na miski da manshi da samubulunshi da turaren.
Taji daɗin su sosai.
Dan dama yanzu take shirin tayi wonkan tsarki.
zata ci gaba da salla daga la’asar.

Wonkanma ta shiga, ta fitowa tasa ɗaya daga cikin dogayen rigunan da suka turo mata.

Yau kwana goma da yin salla ya kama saura kwana sha biyar auren Haroon da Jannart ƙanwar Juwairiyya.
Tako ina shirye-shiryen biki ya kankama.
Washe gari kuwa su Aunty Hafsat da ahlinta duk suka zo.

Kai tsaye masarauta Leddi julɓe suka nufa.
Daɗi a wurin Sitti babu bayani.
Ga ƴaƴanta ga jikokinta, dan Umaymah ma ta kasa jira su iso wurinta randa sukazo da safe suka iso ita kuma da yamma ta iso.
Farin cikin Sitti da Jadda basa faɗuwa.
sai dai duk sanda sukayi irin wannan haɗuwar, yana tono musu tabo da damuwarsu da tashin hankali su.

Hibba ce ta kira, Aysha, take sanar mata.
Su Aunty Hafsat sun iso. Yanzu an fidda ankon aure da tsara duk abubuwan da zasuyi.
Kwanan Umaymah uku a can ta koma ita da Hibba da Isha yar Aunty Hafsat budurwa, kamar Hibban komai na biki Umaymah ta shiryawa Aysha shi.

Yau auren kwana bakwai bikin.
Suna zaune shida Ummi suna tsara tafiyar tasu.
Dan dole Juwairiyya zataje, amman zata tafi da Ya Jafar da yaransu da Jalal.
Su kuwa zasu tafi da Jamil da Ummin.

Sai Hajia Mama da su Ramla da Batool da har yau bata komaba.

Kiran Haroon ne ya shigo wayarsa.
Bayan sun gaisa ne yake cewa.
“Wai kai Sheykh yaushe zaku zone? Dudufa yau saura kwana bakwai ne, kuma daga gobe za’a fara hidimomin”.
Da sauri yace.
“Kai haba Haroon ka nitsu mana kaja numfashi kayi mgna a hankali.
Ni dai bazan je duk sauran shagulgula kiɗe-kiɗe da raye-raye kuba bazan ce kada kayi bane, sanin Abun harda Aunty Rahma iyayen bidi’a.”
Cikin hatsala Haroon yace.
“Za dai kazo kayi mana walima kam”.
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
“Eh walimar maza ba, shima dan Abba da kanshi ne yamin mgn da dan ta kaine ba yi zamba sabida, ba amfani da abinda ake faɗa a walimar akeyi ba”.
Dariya Haroon yayi tare da cewa.
“To Ustazu Allah ya kawo ka lfy”.
“Amin”. yace
“To yaushe zaku zone?”.
Jibi ya bashi amsa a taƙaice.”

Daga nan sukaci gaba da hira.

Yau saura kwana biyu bikin kuma yaune zasu tafi.
Aunty Juwairiyya da Ya Jafar da Jalal kuwa tun jiya suka tafi.

Su kuma yau zasu tafi da dare.

Ƙarfe takwas dai-dai jirginsu ya tashi zuwa jihar Tsinako.

Tara dai-dai jirginsu ya sauƙa cikin birnin Tsinaku.

Bayan sauƙansu da wasu ƴan daƙiƙu, aka buɗe jirgin, kana aka fara fita, daki-daki.
Kasan cewar Ummi da Jamil na ta bakin ƙofar sune suka fara fita.
Sheykh Jabeer da Aysha kuwa suna can VIP Side. Hakan yasa kusan sune ƙarshen-ƙarshen fitowa.

A hankali yake taku cikin nitsuwa da kamala ta nitsastsun malamai magada annabawa.
A hankali ya saƙo ƙafarsa kan step ɗin forko na farfin jirgin.
ido ya lumshe tare da buɗesu yana son jihar Tsinako so mai tarin yawa sabida, yanada jigo shaƙiƙai masu sonshi fiye da yadda suke son kansu.
Su Umaymah, Haroon, ga ƙarinsu Aunty Hafsat, da Aunty Rahma, da ahlinsu.

Hannunshi yasa ya tattare bakin faffaɗan al’kyabbar jikinshi mai masifar kyau da taushi tare da sheƙi.

Yanayin garin da ɗan hadari, ko ina yayi lib, garin yayi duhu yayi baƙi mai kyau, gajumare masu duhu sunyisa sararin samaniya ƙawanya.
Ga wasu kyawawan ciyawi kore shar da suka malale can baya kaɗan, iska mai sanyi ke busowa tana ratsa jiki da jinin mutanen dake wurin.
A hankali take biye dashi a baya inda ya taka ƙafarsa ya cire nan take taka tata ƙafar.

Tayi shigar larabawa tayi masifar kyau, kasan cewar tasa Niƙabi baka iya ganin komai sai fararen idanunta da take ɗan jujjuyawa.

A hankali ya gama sauƙa kan, steps ɗin.
Yayinda ita kuma take step ɗin ƙarshe.
Kanta ta ɗan juyo jin dirin wani jirgi a bayansu yana tashi, yana keta gajumare.
Hannunshi yasa a hankali ya kamo nata, da sauri ta ɗan juyo jin hannunshi cikin nata.
Takowa tayi ta sauƙo kana ta fara bin takunshi sabida bai rigaya ya sake mata hannun ba.

Suna sauƙa gefen jirgin kaɗan baifi taku bakwai sukayi ba, suka isa gaban wata tsaleliyar mota fara ƙal mai sheƙin sabunta, ganin dogarai guda biyu a gefe da gefen motar sanye da jajayen kaya da surkin kore, sai tabka-tabkan rawuna, ne ya tabbatar mata su akazo ɗauka.

Shi kuwa tafin hannunshi ta haɗe da nata ya sarƙafe yatsunshi cikin nata.
Wasu dattawane suma sanye da kaya da rawuna amman su ba shigar dogarai sukayi ba, bisa alama suma, sunada ƴar saurata.

Da sauri suka nufi gabasu.
Suna isa dottawan suka ɗan saki murmushi tare da cewa.
“Barka da isa lfy Malam Jabeer”.
Murmushi ya ɗanyi tare da cewa.
“Barka dai Baba Wambai”.
Sai kuma ya juya wurin ɗayan tare da cewa.
“Barka da yamma Malam Liman”.
Ya ƙarishe mgnar yana miƙa musu hannunshi na dama,
dan dana hagu yake riƙe da hannunta.
Cikin kulawa Malam Liman ya amshi hannunshi tare da cewa.
“Allah yayi maka al’barka ya bada ladan raya zumunci”.
Amin Amin yace.
Cikin nitsuwa Aysha ta gaidasu, cike da jin daɗi suka amsa, tare da juyawa suka nufi motar, da tuni dogaran nan biyu sun buɗe musu, bayan motar.

A hankali suka nufi can yayinda Wambai kuma da Malam Liman suka kama hanyar tafiya dan motarsu na can woje.

Shi kuwa Sheykh suna isa ya ɗan ja da baya tare da sakin hannunta, ya nuna mata hanyar shiga da hannunshi.
A nitse ta rusuna kana ta shiga.
Bayan ta shiga ne, ta gyara zamanta tare da lumshe idonta sabida wani irin masifeffen ƙamshi da sanyi da sukayi mata sannu da zuwa a lokaci ɗaya.
Gyara zamanta tayi ganin yana shigowa, can gefe ta matsa,
shi kuwa yana shiga ya zauna, da sauri dogarin dake gefenshi ya kamo bakin al’kyabbar jikinshi ya samishi ita, ta ciki. Sannan ya maida ƙofar ya rufe.

A hankali motar ta fara juyawa alamar direba na ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button