GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ya juya ya kwanta, a haka sukayi bacci.

Washe gari da asuba kuwa.
Ta koma ɗakinta tayi baccinta.

Shi kuma yana dawowa masallaci, yayi Azkar ɗinsa.
Kana ya ɗauko gorar zam-zam.
sannan ya ɗauki ganyen magarya guda bakwai, cikin wanda ya amsa wurin Gimbiya Aminatu tun jiya da yamma.
Sa ganyen yayi a cikin gorar bayan ya ɗan sha ruwan ya rageshi.

Kasancewar bakin gorar nada ɗan faɗi.

Haka yasa ya zauna dashi bisa kan sallayarshi.
Ayatul shifa ya fara karantawa yana tofawa cikin ruwan zam-zam da ganyen magarya guda bakwan.

Kulhuwa

Falaƙi

Nasi

Ƙuluhiya

Ayatul-kursiy

Amanar-rasuulu

Attaba’u ma tatlush-shayaɗeenu ala mulki Sulayman.

Ita kuwa Aysha a hankali taje tayi wonka bayan Umaymah ta haɗa mata komai na wonka.
Koda ta fito kasa saka rigar tayi sai dogon wondon kawai ta saka.
Ganin hakane yasa Umaymah ta miƙo mata rigar dama da ɗan madaidacin hijabi a jikinta.
Da hannun hagu ta amshi rigar, ta tsaya tana kallon Umaymah.
Ita kuwa Umaymah cikin bada umarni tace.
“Kije Jazlaan ya saka miki rigar”.
Cikin sanyi tace.
“Umaymah Hibba tazo ta saka min”.
Fuska ta haɗe tace.
“Kije ya saka miki nace ko”.
Cikin sanyi tace to.
Kana ta juya ta funi Side ɗinsa.

Ummi da Hibba da Saratu kuma suna Kitchen.

A hankali ta shiga falon.

Shiru tayi tana tunanin ta yaya zataje tace mishi ya saka mata riga.

Hakan yasa a hankali ta warware karin gugar rigar.
Sannan tasa hannunta na hagun ta riƙe wurin zip ɗin, sannan tasa bakinta kuma ta riƙo wuyan rigar.
Zut taja zip ɗin ta buɗe shi.
Hannunta na hagu ta zura cikin hannun rigar.
Sai kuma ta cireshi a hankali tasa hannun damanta mai ciwon a hankali.
Ya zama rigar na kan kafaɗar hannun damar Tata.
Shi kuwa Sheykh ya gama yin tofin, ya ɗauko goran ruwan ya nufi falon don zai maidashi cikin Fridge.
A hankali ya turo ƙofar.
Dai-dai lokacin ita kuma tasa hannun hagun nata mai lafiyar ta kamo hijabin jikinta ta ɗagoshi ta gaba zata cireshi.
Ya zama daga ita sai dogon wondon, daga ƙugunta zuwa shafeffen cikinta da ƙirjinta dake cike tab-tab da jajayen Caɓɓule duk suna fili.

Wani irin ƙara tayi a hankali jin hijabin ya riƙo ɗan kunnenta yaja da ƙarfi.
Da sauri tace.
“Wayyo Allah na ya zanyi hannu mai ciwo hijabi ya riƙe ɗan kunne, riga bata shigaba”.
A hankali ta fara juyi tana kiran Ummi Ummi.
sabida duk yadda ta motsa hijabin sai taji ya ƙara jan hujin kunnenta.

Yadda take taku tana juyi ne yasa jikinta keyin wani irin kaɗawa.

Shi kuwa Sheykh, wani irin masifeffen numfashin ya fixga da azaban ƙarfi.
Rumtse idonshi yayi da sauri.
Tare da juyawa ya fuskanci Dinning area idonshi a rufe.
Yana jin tsikar jikinshi yana zubawa yana mummiƙewa.
Zuciyarshi na harbawa a dubu.
Yana isa ya ajiye goran kan Fridge ɗinsa.
Sannan ya juyo da sauri.

Juyowar da zaiyi kenan yaji yayi karo da ita.
Ta manna bayanta a ƙ….!

                      By
       *GARKUWAR FULANI*Bayanta da ƙirjinshi.  

Da sauri ta ɗan koma gaba tare da cewa.
“Innalillahi”.
Sai kuma ta tsaya ta juyo ta fuskanceshi da kyau.
Idonshi ya rumtse da sauri, Allah yasani bazai iya jurarar ganin waɗannan ababen ba masu masifar tada hankalin da gigita kwakwalwar ɗan adam.

Ido a rufe ya buɗi baki murya can ƙasan maƙoshi yace.
“Me hakan?”.
Da sauri ta fara ja da baya tana cewa.
“Ka tafi! Ka tafi!”. Buɗe idon yayi a hankali kana yayi taku biyu zuwa uku ya kamota, a hankali yace.
“Ke meyasa bakya nitsuwa ne akan komai! Yanzu a hakan ina zakije a tsiraranki”.
Ya ƙareshe mgnar yana sa hannunshi ya janye rigarta dake cikin hannun ta.
A hankali hannunta na hagun ta zaro tare da rufe ƙirjinta da ko rabinsu bai rufuba.
Cikin sanyi ya matsota da kyau, a hankali yace.
“Me zakiyi ne?”.

Murya a kunyace tace.
“Zan saka rigatace kuma na kasa shine. Umaymah tace inzo in baka kasamin.”

“Uhummmm”. Shine abinda ya iya furtawa sabida ji yake kamar bazai iya mgna ba.

Ita kuwa cikin sauri tace.
“Wash”. Jin ya fara jan hijabin.
Da sauri tace.
“Kayi min a hankali kunnena”.

Ba tare da ya sunkuyo ya kalleta ba yace.
“Meya samu kunnen?”.

Cike da kunya tace.
“Hijabin ya sarƙafe min ɗan kunne”.

Bai tanka mata ba, sai hannunshi yasa ya buɗa hijabin.
Ya maidashi a hankali yasa yatsunshi biyu, yana cire ɗan kunnen.

Matsota ya kumayi, kana ya samu ya warware garkuwan ɗan kunnen daga jikin yadin hijabin.
Sai kuma yasa hannunshi ya cire mata hijabin duka.

Ya zama daga ita sai wondon dake manne a jikinta.

A hankali ya sunkuyo ya ɗauki rigar tata, sannan ya juyo ya zama tanata cikin falon shi yanata baƙin ƙofar shiga,
Yayi mata ƙawanya da jikinshi.

Idonta a sunkuye, hannunta na saman caɓɓullenta.
Zura mata rigar yayi a wuyanta.
Cikin nitsuwa ya buɗe hannun rigar na dama ya sakamata cike da takatsantsan.
Sannan a hankali yasa hannunshi ya kamo hannunta na hagun ya saka mata hannun rigar.

Cikin hikima ya sake rigar tayi ƙasa, sannan a hankali ya juyo bayanta, dai-dai ta wuyan rigar yayi kana yaja mata zip ɗin.
Ɗan sunkuyowa yayi ta kafaɗanta, ganin gaban rigar bai dai-dai-ta yadda ya kamata bane yasa a hankali yasa hannunshin cikin wuyan rigar.
ciki da mamaki da tsoro ta rumtse idanunta.
Shi kuwa hannunshi yasa ya dai-dai-ta caɓɓullenta cikin breastcub ɗin.
Kana ya dauki ɗan kwalin ya ɗaura mata a kanta kamar mayafi kana ya juya ya nufi.
Dinning area yana maijin wani irin yam-yam da tafin hannunshi ke mishi tun sanda ya taɓa caɓɓullenta, hannunshi yasa ya ɗauki goran zam-zam ɗin da ya mata addu’o’in karya sammu.
Gabanta ya dawo, ita kuma tana ta son ɗaura ɗan kwalinta.
Goran ya miƙa mata tare da cewa.
“Gashi wannan shi zakisha duk sanda kikaji ƙishi.
In kinsha kuma ki ɗan shafawa hannun ki mai ciwon”.
Cikin yin ƙasa da idonta ta amshi goran tare da cewa.
“Ngd”.
Bai tanka mata ita kuma ta juya ta tafi.

A falo ta samu Ummi da Umaymah da Hajia Mama,
suna zaune.
Cikin wani irin yanayi ta kalli Hajia Mama kana tace.
“Ina kwana”.
Fuska cike da fara’a tace.
“Lfy lau. Alhamdulillah yau jiki da sauƙi ko?”.
A taƙaice tace.
“E”.
Daga nan ta wuce.
Hajia Mama kuwa Umaymah ta kalla tare da cewa.
“Khadijah ya lbrin Auren Haroon ne Kam?”.
Ajiyan zuciya tayi tare da cewa.
“To aure kam yazo ga mai nisan kwana”.
Bayan sallan layya da kwana goma za’a fara bikin”.

“A lallai aure kam yazo ga mai nisan kwana”.
Hajia Mama ta faɗa.

Ita kuwa Ummi murmushi tayi tare da cewa.
“Lallai jihar tsinako zata kwashi baƙi”.

Nan dai sukayi ta hira.

Sheykh Jabeer kuwa. A hautsune ya koma bedroom, kan gado ya kwanta tare da yin rubd ciki.
Idonshi ya rumtse da ƙarfi wai ko zasu dena harsasho mishi hoton abinda ya gani.

Kiran da akewa wayarshi ne ya sashi jan tsaki
Karo na uku yanajin kiran yana shiga.
Ya sani babu mai mishi wannan kiran mafarautan sai mutun biyu.
Haroon ko Ahmad wani babban abokinshi ɗan kasar Cameroon.

Hannunshi yasa ya amsa kiran tare da danna amsa kuwa.
Tsaki yaja jin Haroon na cewa.
“Kai kace baka son yawan kira, in an kiraka sau ɗaya kuma baka ɗagawa dan wulaƙanci.
Ni kuma gani Sitti ce ta buwayeni da in Kira mata kai taji lbrin jikin amarya.”
Cikin sanyi yace.
“Yaushe kaje lamorde julɓe?”.

“Yau kwana biyar”.

A hankali yace.
“Anya kuwa Haroon in kayi aure bazaka dena aiki ba”.

Taɓe fuska yayi tare da cewa.
“Babu mamaki in bar aikin ma inji da amaryata”.

Ɗan gajeren tsaki yaja tare da cewa.
“Bawa Sitti wayar”.

Miƙa wa Sitti wayar yayi.
Cike da kulawa da so tace.
“Muhammad”.

“Na’am Sitti ya gida”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button