GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Yana zuwa ya miƙawa sarkin Bakan,
yana amsar ƙoryar,
ya ajiyeta a gabanshi jakar fatar ruƙimi da yakesa magungunanshi a cikine ya sauƙe daga kafaɗarshi, kana a hankali ya fara harhaɗa magunguna a cikin madarar,
saida yasa komai sannan ya kalli Inna yace.
“A bani zuma da zam-zam”.
Da sauri tace.
“To”. Kana ta miƙo ta ɗauko mishi, koda ta kawo da sauri yasa zumar da zam-zam ɗin ya gaureyasu,’.
Kana ya bawa Malam Liman da Arɗo Babayo sukayi mata tofin ayatul shifa, a ciki, kana ya amshi kwaryar.
Inna ya miƙawa kwaryar yace.
“Gashi bata tasha”.
Amsa tayi kana ta matso kusa da matar a hankali tasa mata bakin kwaryar a bakinta.
Tare da cewa. “Bismillah ki Sha”.
A hankali ta buɗe bakinta, ta fara shan madarar shanun nan da magungunan, masu haɗe da zam-zam da zuma da kuma rahamar ayatul shifa.
Saida ta sha mai yawa sannan ta kauda kanta.

Ae fa a take saiga naƙuda ta tashi gadan-gadan. Ganin haka yasa su Arɗo kab suka fito woje ya rage daga ita sai Inna.

Ganin haka yasa Malam Liman tura Ori da yanzu ya shigo yaje ya kira matarsa ta taimakawa inna su amshi haihuwar.

Ba jimawa kuwa Iya laure tazo, kai tsaye cikin ɗakin ta wuce.

Cikin ikon Allah a take a sauƙaƙe Allah ya sauƙeta lfya, ta haifi yarta mace ƴar ƙanƙanuwa.

Bayan sun yanke cibiya sun gyara,
komai na wurin.
Kana Inna ta taimaka mata tayi wonka,
ita kuwa iya laure wonka tayiwa jaririyar ta haɗeta cikin zanin Inna ta bawa Parvina daketa tsalle.

Koda suka fito daga wonka,
konciya tayi a kan katifar, kana iya laure ta kontar mata da ƴar a gabanta.

Ajiyan zuciya ta sauƙe mai ƙarfi kana a hankali ta lumshe idonta, tana son ta tuno wani abu na rayuwarta ta baya amman ina ta kasa tunowa,
Abu ɗaya takeji bata manceba sunan Allah wanda tunda ta dawo mutun taketa maimaita kiranshi a zuciyarta dan taji bakinta bazata iya magana ba, amman a ranta tanaji tana bitar karatun al’ƙur’ani mai girma da tarin addu’o’in kamar yadda takeyi tun tana a tsunstsuwar ma.

Ganin tayi shiru ne kamar maiyin bacci yasa inna da iya laure suka fito woje.
Sashin Arɗo Babayo suka nufa,
suna shiga sukayiwa juna barkar haihuwarta lfy.
Shiru sukayi baki ɗayansu bayan duk sun zauna kamar yadda Sarkin Baka ya umarcesu, gyaran murya yayi kana a hankali ya fara magana.
“To da forko dai sai dai muce. Alhamdulillah, mun godewa da yasa sanadinmu wata baiwar Allah zata samu waraka daga mugun cuta na magauta maƙiya azzalumai marasa tsoron Allah”.
Kai suka jinjina alamun gamsuwa, shi kuwa tonkoshe ƙafa yayi kana yaci gaba da cewa.
“Kamar yadda kuka gani a yanzu mutunce bani adam ce ba tsunstsuwa bace kamar yadda kuka gani da zata a baya, aikin sihirine kawai ya maidata haka.
Amman Alhamdulillah tunda gashi yanzu Allah yayi ikonshi ya karya abun da akayi mata ya kuma sauketa lfy dama shi asiri tasirinshi kaɗanne ga wanda yayi imani da Allah kuma dole gsky zatayi halinta watan-watarana”.
Arɗo Babayo ne yace.
“Allah mai iko, mutun a maidashi tsuntsuwar Boleru kai abinnan da al’ajabi”.
Kai ya gyaɗa mishi tare da cewa.
“Ɗan Adam kenan mai wuyar gane hali babu mai sanin halin mutum sai Allah, domin shi ɗan adam dare”.
Sai ya kuma kalli Inna tare da cewa.
“Yanzu tayi magana ne?”.
Da sauri Inna tace.
“A a batayi mgna ba sai dai in anyi magana tanaji kuma tana ganewa”.
Kai ya rausayar tare da cewa.
“Zatayi magana in sha Allah, yanzu aci gaba da kula da ita yadda ya dace zan bata magunguna kuma,
sannan kada kuji tsoronta ko kaɗan in sha Allah ba mai cutarwa bace”.
Malam Liman ne ya gyara babbar rigarshi tare da cewa.
“To wannan baiwar Allah’n ko daga ina ta fito? Ko ta yaya zamu gano yan uwanta danginta ahlinta ko wani nata a duniya?”.
Sarkin bakanne yayi ɗan gyaran murya kana yace.
“In sha Allah ita in ta dawo haiyacinta, zatayi mana bayanin komai zata faɗa mana sunanta sunan garinsu sunan iyayenta sunan mijinta da anguwarsu sai mu mikata garesu”.
Appa ne ya ɗanyi ajiyan zuciya tare da cewa.
“Allah ya bata lfy ya kuma dawo da ita cikin haiyacinta, kuma in sha Allah duk wani abu daya kamata ayimata a duniya zan mata har sai munga ta samu’ lafiya ta koma ga iyayenta”.

Da haka sukayi ta tattauna duk abinda ya dace ayi mata.
Anan kuma sarkin baka yaje da kanshi ya ɗaure mata karayar hannunta yayinda Parvina kuwa ke like da ita…!

Haka Inna da iya laure sukayi ta kula da ita a cikin wannan satin sunan…!

                  ************

…Bayan shekaru Goma sha biyu…

Cikin Ƙasar Kautal A Jihar Ɓadamaya state.

A wani yanki na Ɓadamaya state, cikin Shikan local Government area a wata rugar FULANI mai suna.
RUGAR BANI

Garin Shikan wani yankine daga yankunan Ɓadamaya yankine mai tarin ƙabilu ma banbanta addinai da al’adu wanda duk yankun Ɓadamaya shida Bimu sune sukafi tarin ƙabilun sai dai babbancin mafiya yawan kabilun Bimu musulmaine saɓanin mafiya yawan ƙabilun Shikan kafurine maƙiya Allah da Manzonsa.

Shikan shine sashin da yafi tara ƙabilu mafiya yawa, masu baƙaƙen zuciya ƙabulun da hasken addini bai cimmusuba.
Ƙabila mafi rinjaye a yankin Shikan itace ƙabilar ɓachama. Mafi akasari Ɓachamawa mutanene kafurai ne marasa ɗigon imani a zuƙatansu marasa son zaman lfya, mugunta da kisa shine abinda ke sasu farin ciki, abinda kawo ya sanine duk sanda akaji jihar Ɓadamaya cikin wani tashin hankali to daga ƙabilar ɓachama ne.

Duda yawan ƙabilu na garin Shikan hakan baisa fulani sun sakar musu garinba, domin tushen garin na fulanine, sabida kowa yasan makiyayi basa nesa da wurin damshi da ruwa, domin rayar da ababen kiwonsu.
Haka yasa akwai musulmai Hausawanmu da tarin yawa cikin garin Shikan, wanda duk rintsi da wahala sunƙi barin garin, koda yake hakan baya rasa nasaba da irin al’barkatu da ni’imomin da Allah yayiwa garin.

Daga gefen. Garin Shikan akwai babban kogin da yakeda ruwa biyu wanda ko wucewa zakayi ta kan babban gadan da titin da zai kaika cikin Ɓadamaya zaka hangi ruwane kala biyu a kogi ɗaya basu kuma taɓa haɗewa wuri ɗaya ba da izinin ubangiji.

Gefen kogin ta dama wata babbar Rugar fulani mai suna Rugar Bani ce mai tarin tarihi, rugace mai girma wacce Ubangiji ya ƙawatata da ababen buƙatar yau da kullum, wannan Ruga itace yanki mafi sanyi a yanki Ɓadamaya state rugace damu fulani muke ce musu JOTTAN MA’EN Bi ma’ana fuli mazauna wuri ɗaya, ba ire-iren fulani makiyaya masu tafiye-tafiye bin rugageba, fulanin Rugar Bani fulanine makiyaya masu tarin dabobi masu tarin yawa, Rugar Bani Rugace da aƙalla fulaninmu sunyi sama da shekaru dari da ashirin awannan Rugar, shiyasa harda gini zamani da kyawawan gidaje fulanin sukayi, yayinda kuma akwai bokkokinma a cikin Rugar tasu wanda kuma suka sayi filin da kuɗinsu zufansu a hannun sarkin Shikan na wancan zamanin ya sayar musu yankin wurin gaba ɗaya sun biya kuɗinsu ya kuma basu takardu su, suna zaune a nan suna noma suna kiwo.
Rugar Bani na zagaye da ƙauyukan ƙabilun Ɓachamawa da tarin yawa, wanda nan gefensu ƙauyen Bonon yake wanda nanne dodon tsafin ƙabilar ɓachamawan take wanda sunan dodon tsafin nasune suka sawa suna ƙauyen suna Bonon. Kauyen Bonon shine zuciya da karfin kafuran nan, sunyi imani dashi, fiye da zaton mai zato, koda laifi wani yayi bonon ake kaiwa ƙara kuma muddin bonon ya tsinewa mai laifinsun to zai lalace ya ɗai-ɗaice dashi da zuriyarsa baki ɗaya, da yake sunyi imani da hakan kuma yana faruwa suna gani shiyasa bonon yake tamkar zuƙatansu, kamar dai yadda in jikin ɗan adam idan zuciya ta ɓaci gagganji na ɓaci to haka bonon take a wurinsu… Wannan kenan

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button