GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

                        By
            *GARKUWAR FULANI*

Wata iriyar zuface ke tsastsafo mishi bisa goshinsa,
Kamar an watsa mishi ruwa.
Ya kamo lip ɗin shi na ƙasa yana taunewa.
Hannunshi dake cikin blanket ta zubawa ido.
Dan son gano abinda yakeyi,
shiru tayi sawon 5 minute kana, a hankali ta ɗaura tafin hannunta kan goshinta,
tare goge mishi zufar, daketa tsastsafowa duk da sanyin A/C dake ratsa ɗakin.
Idonshi ya saisaita lumshe su da yayi, ya sani Umaymah ce.
sabida babu mai shigar masa ɗaki kai tsaye sai ita.
Babu kuma mai taɓa mishi goshi haka sai ita.
Cikin kula tace. “Jazlaan!”.
A hankali ya gama buɗe idanunshi da sukayi jazir alamun tarin ƙuna da yakeji a ransa.
A hankali tace.
“Jazlaan!.” Ta kuma kiranshi a karo na biyu.
A hankali ya motsa lips ɗin shi alamun zai amsa mata.
Amman Ina zafin da zuciyarshi keyi ya danne harshensa hafimtar hakane yasata, nuna damuwarta a hankali tace.
“Kaci abinci?”. Ƙarya ba ɗabi’arsa bace ba kuma halittarsa bace, duk ɗacin gsky zai faɗeta, bare a kan kashi.
Kanshi ya girgiza alamun baiciba.
Cikin sanyi tace.
“To Muje kaci koda abu mara nauyi ne!.”
Da ƙarfin ya fizgo mgnar.
“Bazan ci ba”.
Ta sani yadda yayi mgnar, ta kubce masane, dan in ransa a ɓace yake baya mgna, ɓacin ran mai limini kenan babu faɗe-faɗe bare hargowa ko buge-buge.
Sanin ko ya zatayi bazai cin bane, kamar yadda ya faɗa mata yasa,
ta miƙe a hankali kanshi ta shafa tare da cewa.
“Saida safe”.
Kai kawai ya iya gyaɗa mata,
Haka ta fara tafiya, tana kallon yadda yake motsa hannunshi cikin blanket tabbacin. Wani abun yake yagewa.

Yadda ta bar Haroon haka ta sameshi saida safe tayi mishi kana ta wuce ta tafi.

A can Rugar Bani kuwa. Kamar yadda Ba’ana ya ɗaukarwa kanshi al’ƙawari haka ya bar ƙasar ya nufi ƙasar Cameroon Kai tsaye Yahunde ya nufa, cikin rugagen Fulani, yana tafiyarne da ɗan sauran tsafi da sihirin dake jikinsa.

A haka ya nausa cikin ƙasar Cameroon da yake jihar Ɓadamaya tana bakin bodar ƙasar ne.

Fulanin Rugar Bani kuwa, a daren wannan ranar sukayi gangamin ramuwa, suka faɗawa ƙauyukan kafuran ƙabilun ɓacamawa dake cikin Shikan da kewayenta.
Allah ya basu nasarar yaƙan kafuran nan.
Har suka samu damar ƙona ƙauyem Bonon wanda shine zuciyar ƙabilar ɓachama, kamar yadda Abuja take zuciyar Nigeria.
Cikin daren suka ƙona ƙauye dama dodon tsafinsu Bonon da suka ɗauka a matsayin Ubangiji su sun ƙonashi sun ɓadda shi a doron duniya sai dai tarihinsa.

Wannan labarin shine labarin.
Da gidajen rediyo dana tv da jaridu sukayi.
Breakfast dashi yayinda akayita kuzuzuta cewar Fulani sun zama ƴan ta’adda sun farma garuwa da yaƙi.
Uhummm wannan shine halin da Fulani ke rayuwa a ciki. A zalimcesu, kaji cib duniya babu mai yin mgn su kai ƙorafinsu a koresu. Gwamnatin kasar data jiha suyi kamar basujiba. In fulanin sun rama na lokaci ɗaya sai asa musu sunan ƴan ta’adda ko yan tada zaune tsaye, har ana ikirarin korarmu.????????????

Hankalin ƙabilun Ɓacamawa dake cikin Shikan duk suka ari ta kare.
Hausawa da Fulani kuwa kowa ya koma, cikin gidansa.
Domin Allah ne yabi kadunsu.

Sarkin Shikan da kanshi yayi masifar girgiza da yawan da Fulani sukayi cikin garinshi da kewaye.
Gashi an ƙone dodon tsafinsu nasu kuma babu abinda ya samu fulanin.
Hakane yasa shi kanshi ya arce, sai abu ya lafa ya dawo.

Su kuwa Fulani bayan sun gama.
Suka tsaya suka bawa yaransu da tsoffinsu mafaka, domin su basu kashe yara da tsoffi da mataba.
Anyi an gama, kafin hukuma tazo, ta ƙara sai saita Komai.

A cikin masarautar Joɗa kuwa. Washe gari da safe.
Lbrin ya rinski Sarki Nuruddeen, shine ya bada umarnin kada a kama bafulatani ko ɗaya.

Aysha ce zaune gaban Umaymah Aunty Juwairiyya na gefenta ita da Hibba, cikin kula Umaymah tace.
“Yauwa Aysha kinga wannan ki ɗauke ta matsayin yayarki ita ɗin yar babban Yayanmu ne wanda na nuna miki jiya.
Mijinta kuma ya’yan Jabeer ne, Side ɗinta na kusa da naku.
In kinga duk wani abun da baki fahimta ba ki tambayeta, in kin gaji da zaman kaɗaici zaki iya shiga wurinta, da wurin Mamanku, da kuma nan wurin Gimbiya Aminatu”.
A hankali ta ɗan kalli Aunty Juwairiyya, tare da cewa.
“Ina kwana Aunty”. Cikin jin daɗi Aunty Juwairiyya tace.
“Lfy lau ya baƙunta”. A hankali tace.
“Alhamdulillah!”.Hibba ce ta ɗan tsuke baki cikin sanyi tace.
“Shike nan ai, an gabatar mata da kowa sai ni aka ware”.
Murmushi Aunty Juwairiyya tayi tare da cewa.
“To Aysha ga Hibba wutar Umaymah, duk family itace auta a jikokin Sitti na nan ƙasar”.
Murmushi ta ɗan yi sabida ganin yadda Hibba tayi sai Junainah ta faɗo mata a rai.
Ita kuwa Hibba motsata tayi tare da cewa.
“My happiness”.
Cikin murmushi Aysha ta nuna kanta, alamun “Nice my happiness?”.
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
“Yes haka Umaymah tace wai kece farin cikin ahlimu da izinin ubangiji”.
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta.
Haka nan taji tana jin sonsu a ranta, Especially Umaymah da Hibba.
Aunty Juwairiyya kuwa da Ummi breakfast Suka gabatar mata, kana suka fita.
Umaymah da kantane ta haɗa mata tea mai kauri ita da Hibba kana ta zuba musu abincin da Aunty Juwairiyya ta kawo musu tare da cewa.
“Bismillah kuci abinci”.
tana faɗin haka ta miƙa ta fita,
Ita kuwa Hibba da tsauri ta gyara zamanta tare da ɗaukan Fork ta matso gaban plate ɗin da aka zuba mata soyyyan dankali da kwai, hannun tasa ta soki guda biyu tare da ɗagowa zata kai bakinta, sai kuma ta tsaya tare da zubawa Aysha ido ganin ta riƙe mata hannunta.
Cikin sanyi da ɗan sakin jiki da Hibba ta girgiza mata kai tare da cewa.
“Kada kici wannan abincin”.
Cikin juya ido Hibba tace.
“Meyasa!?”.
Kai ta jujjuya mata kana ta gyara zamanta, tare da ɗan kallon ƙofar shigowa ta gefen idonta.
Wani kekyawan Foodflaks da aka kawo daga sashin Gimbiya Saudatu ta jawo tare da cewa.
“Ki ɗiba a nan kici”. Cikin mamaki.
Hibba tace.
“Aunty Aysha, ai Bama cin abincin gidan Gimbiya Saudatu, kuma naga Hadimanta ne suka kawoshi”.
Cikin rashin gane manufar zancen Hibba tace.
“Meyasa bakwa ci?”.
Juyawa Hibba tayi ta kalli bayanta kana ta juyo ta kalleta da kyau kana a hankali tace.
“Bata son Hamma Jabeer dama duk ƴan uwanshi, cewa take zata kasheshi in ta samu dama, shiyasa Umaymah take hanamu cin abinci ta”.
Wani irin nannauyan ajiyan zuciya ta sauƙe tare da kallon Hibba cikin cushewar tunani ta kalli jerin kulolin da a ƙalla sun kusa takwas a gabansu.
Cikin sanyi tace.
“Buɗe su mu gani”.
Jin hakane yasa Hibba buɗe su ɗaya bayan ɗaya.
ita kuwa ido take zubawa duk kular da Hibba ta buɗe.
Kular ƙarshe wacce ke ɗauke da Chicken Ball’s mai zafi sai turiri yakeyi da ƙamshi.
ta nunawa Hibba tare da cewa.
“Kici wannan”.
Murmushi Hibba tayi kana tace.
“Yauwa shinema na Gimbiya Aminatu kuma ta iya girki tsohuwar hakana hadimanta, a plate ta zu musu. Kana suka faraci suna ɗan korawa da ruwan tea mai zafi da kauri.
Sunaci Hibba nata janta da hira duk da ita Aysha zuciyarta a cushe yake.

Bayan sun gamane, Hadiman Gimbiya Aminatu suka shigo suka tattare komai suka gyara wurin bisa umarni Jakadiya.

Ganin Aysha ta ɗan saki jiki da Hibba ne yasa, Umaymah ta wuce Side ɗinsa ita da Umminshi.

A falo suka samu Jafar, Jalal, Jamil, Haroon. Suna bisa kujerun Dinning area, Aunty Juwairiyya tana zuzzuba musu abincin.

Murmushi Umaymah tayi cikin jin daɗin ganin su, da wal-wala hatta Jalal fuskarshi a sake take.
Jamil ne ya kalleta lokacin data ƙara so kusa dasu, cikin murmushi yace.
“Umaymah mu sai yaushe za’a nuna mana Amaryar a gabatar mata damu, ta sanmu da kyau”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Ai ku tun daren jiya nagabatar da sunayenku da matsayinku gareta”.
Haroon ne ya ɗan kurɓi tea tare da cewa.
“Yo ai Ni dai ba sai an gabatar daniba, domin nasanta tun safiyar jiya kafinma a ɗaura auren ko Jalal?”.
Taɓe baki Jalal yayi tare da cewa.
“To ni mamaki nakeyi, ko dai dama ita tazone dan taga wanda za’a aura mata”.
Umaymah ce ta ɗan zauna kusa da Jafar tare da kallonsu kana tace.
“Babu sam ita kanta bata saniba bata zata ba bata tsammaci aurenta a jiyaba.
Sai dai arashi kukayi, Ni tun jiya da kuka gayamin nasan arashi ne kawai ya haɗaku a asibitin. Bata san komaiba akan auren nan hakama iyayenta, basu da zaɓine kawai dan sun san ƙa’idar gasar Shaɗi ne hakan yasa sukayi haƙuri.”
Kai Jalal ya jinjina tare da cewa.
“Uhummm mu dai yanzu yan kallone. Dan na sani tabbas yanzu za’a fara buga Game ɗin yanzu wasan zai soma”.
Cikin yin ƙasa da murya Jamil yace.
“Sosai ma, dan kuwa akwai kitimurmurar da za’ayi a masarautar Joɗa, wannan Ustaz Sheykh Malam akarmakallahu Hamma Jabeer ɗin, salonshi na dabanne a dukkan lamuran yauda kullum wannan auren dai zamuga ya zai kasance!”. Ya ƙarishe mgnar da yin ƙasa da murya sosai, yanayi kuma yana kallon hanyar falon Sheykh Jabeer.
Cikin haɗe fuska na wasa Umaymah tace.
“Al’khairi shine zai wanzu”.
Murmushi Haroon yayi tare da cewa.
“Inafa al’khairi a wannan abun da bashi da tushe, ni kaina naji baƙin cikin wannan al’amari, auren Muhammad Jabeer ya zama kamar a munafuce a ɓoye babu wani shiri bare kimtsi kun bari an auro mishi mace kamar auren ƴar tsana”.
Jafar kam abincinsa yakeci, ba tare da ya kulasuba.
Jamil kuwa sai murmushi yakeyi.
Jalal kuwa shiru yayi alamun nazari.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button