GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

To Ummi tace kana ta miƙe ta fito falon forko dasu.
Saratu da Larai ta kira sukazo suka ɗauki kayan.

Nan suka fara da sashin Hajia Mama.
Koda aka nuna mata kayan shiru tayi cikin wani irin yanayi ta gyaɗa musu kai tare da nuna musu hanyar fita ba tare da tace ko ƙalla ba.

Daga nan gidan Galadima da sauran dottawan masarautar suka nufa.
Sai da suka gama da gidajen manyan kana suka nufi, Side ɗin Gimbiya Saudatu kasancewar itace matar babban ɗan Lamiɗo.

Wani irin masifeffen kallo tabi sarƙar tamɓarin Masarautar Joɗa da akasa cikin kayan kana ta kalli Ummi tare da cewa.
“Uhummm za’a kuma kenan, wata sarƙar aka kirkiro ko dai waccar ɗin ce aka gano?
Ita dai Ummi kai ta sunkuyar.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu Baba Basiru dake gefenta ta kalla tare da cewa.
“Ashe ɗan naku waliyi ne?”.
Da sauri yace.
“Waliyi kuma”.
Cikin takaici tace.
“Eh to gani nai wata shida kenan da yin aure.
Ace bai kusanceta ba sai yauwa ai da gani kasan munafurcine da ƙarya, harda basu dawakai ma’aurata ko meye manufar hakan?”.
Cikin nuna tsantsar tsana Baba Basiru yace.
“Wani salone hakan”.
Ita dai Ummi dasu Saratu sun gaza tashi.
Cikin bala’i Baba Nasiru da yanzu ya shigo yace.
“Kai da Allah ku ɓace min da gani”.
Da sauri suka ɗauki kayayyakin suka fice, sukaci gaba da nunawa.

Su kuwa Gimbiya Saudatu da muƙarraba ta suakaci da tattaunawa.

A hankali Dr Kubra ta shigo falon ta sallama a bakinta.
Su Jalal ta samu suna breakfast kamar kullun.

A falon ta zauna bayan sun gaidatane, Jamil yace.
“Ummi tayi cikin masarautar Joɗa jirata zata zo”.
“Okay ba matsala”. Dr Kubra ta faɗi tana gyara zamanta.

Jim kaɗan sai ga Ummi ta shigo su Saratu na biye da ita a baya da kaya niƙi-niƙi.
A ƙa’ida a hannun miji za’a danƙa kayan sai ya haɗa da nasa tukuicin ya miƙawa amaryarsa.

Cikin sakin fuska Ummi ta kalli Dr Kubra tare da cewa.
“A a lale marhabin da Dr”.
Murmushi tayi kana tace.
“Yauwa Ummin Sheykh ya mai jikin”.
“Alhamdulillah jiki da sauƙi.
tace.
Tana amsar kayan hannun Saratu.
Tare da cewa.
“Yauwa kawosu nan, kije ki kawowa Dr ruwa”.
To Suratu tace.
Ita kuwa Ummi amsar kayan tayi kai tsaye falonshi ta nufa da sallama a bakinta, yadda ta barsu haka ta samesu.
kai tsaye bedroom ta wuce da kayan taje ta ajiye kana ta dawo ta wuce ta ɗauko sauran sannan taje ta ajiye, tana fitowa tazo kusa dasu cikin kula tace.
“Yauwa Sheykh gacan tukuicin masarautar Joɗa, sai ka da kashi gareta sanda kaso”.
Kai ya jinjina ba tare daya ɗago kanba.
Ita kuwa Ummi Aysha ta kalla tare da cewa.
“Aysha tashi muje ga likita tazo”.
Cikin sanyi ta buɗe idonta kana tace to.

Ita kuwa Ummi tuni tayi gaba.

Yunƙura tayi a hankali ta miƙe tana mai cewa.
“Wash Allah na”.
Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
“Allah’nmu dai”.
murmushi yayi ganin yadda ta fara tafiya.
Cikin yin ƙasa da murya yace.
“Dawo ki zauna ba inda zakije kina tafi like ƴar kaciya.
ki tsaya zan duba abina da kaina, zanyi gyaran ɓarnar da nayin”.
Cikin rauni tace.
“Ni bana so ita zata dubani”.

Kanshi ya gyaɗa kana yace.
“Okay”.

Ummi kuwa jin shirune yasa ta dawo,
nan yace su shigo nan ɗin.

A mutunce Dr Kubra ta gaisa da Sheykh kana ta kalli Aysha cikin kula tace.
“Meke damunki?”.
Ido ya ɗan zuba mata don jira yake yaji me zata ce.
Ajiyan numfashin yayi a hankali jin tace.
“Kaina ne ke min ciwo sosai, sai kuma zazzaɓi, da jiri nakeji idona na ganin duhu”.
Juyowa tayi ta kalli Sheykh cikin sanyi tace.
“Dr ni ai bansan ka dawoba, da bazanzo ba. Gaka a wuri kuma me amfanin nemana.
Yanzu zamu fita da Jamil sai in turo mata mgnin da kaga ya dace”.
Kai ya jinjina kana yace.
“Kin san maganin wanda baka saniba yafi daɗin karɓa a wurin wasu, rubuta mata kawai ba matsala ki bawa Jamil ɗin ya kawo.”

To tace tana murmushin yadda Aysha ta turo baki.

Bayan ta fitane Ummi kuwa ta zauna.
Ferfesun zabi ta zuba a plate yana zuba tiriri mai ƙamshi kana tasa mata tea, sannan tace.
“Zoki zauna kici kinji ko!”.
Tana faɗin haka ta fita.

Shi kuwa Sheykh kanshi a sunkuye idonshi kuma na kan Aysha, a fakaice yake kallon Ummi bayan Ummi ta fitane, ya ɗan ɗago kanshi kana ya ajiye warshi, kusa da ita ya matso, a hankali ya gyara zamanshi suna fuskantar juna, Fork ɗin ya ɗauka ya riƙe yana dan sa Fork ɗin yana saɓule kasusuwan daga jikin naman kanshi a sunkuye yace.
“Ki dena hararata mana, me nayi miki haka kike min mugun kallo?”.
Tura ɗan bakinta tayi cikin zubda hawaye tace.
“Ni ban harareka ba”.
Kanshi ya gyaɗa ba tare da ya kalleta ba, kana ya sa hannunshi ya ɗauki cup ɗin, miƙa mata yayi har kusa da bakinta.
Kana ya gyaɗa mata kai alamun ta sha.

Wani irin lumshe ido tayi hakan ya bawa hawayenta daman zubowa.
a hankali ta buɗe idonta ta zubasu kan fuskarsa,
wani irin masifeffen abu takeji cikin zuciyarta, zirin kwayar idanunshi ta zubawa ido.
Tabbas Yah Ba’ana kekyawa ne ajin forko, amman yau data nazarci fuskar Sheykh sai take ganin ko rabin kyanshi Ba’ana bai samuba.

A hankali ta buɗe lips ɗinta jin ya manna mata kofin.
Lumshe ido tayi lokacin da taji ɗumi da ɗanɗanon team ɗin, wanda yake tamkar Ummey’nta ne ta haɗashi.
Kaɗan tashe ya janye kofin, kana yasa Fork din ya soki tattausan soƙan gasashen naman.
Bakinta ya nufa sashi tare dasa hannunsa ɗaya ya riƙe hannun damanta ya fara murzawa a hankali kana cikin yin ƙasa da murya yace.
“Haa”.
Ya ƙare abun da alamun ta buɗe bakin.
Haka nan taji ta kasa yi mishi musu, cikin sanyi ta buɗe bakin yasa mata tsokar,
Ido ta lumshe sabida wani irin masifeffen daɗi da taji naman yayi mata, Allah ya sani bata taɓajin gashin naman da ya mata daɗi irin na yau ba.
wani ya kuma bata, still ta amsa taci.
Kana ya kuma bata cup ɗin tea ta kurɓa, haka yayi ta bata tanaci yana bata tea kana yana murza tafin hannunta cikin nashi saida tayi gyatsa kana a hankali tace.
“Alhamdulillah”.

Ganin ya kuma miƙo matane yasa ta kauda kanta tare da lumshe idanunta tace.
“Yah Sheykh na ƙoshi”.

Kanshi a sunkuye yace.
“Ban yardaba”.

A hankali tace.
“Allah kuwa”.
Numfashi ya ɗan fesar kana yace.
“To muga cikin”.
A hankali tace.
“Gashi”.

Hannunshi yasa bisa cikin nata, kana a hankali yace.
“Ɗaga rigar”.
Tura baki tayi cikin jin bacci tace.
“In ɗaga kuma?.”
Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Na’am ki ɗaga inga in cikin ya cika, sai muje bedroom inga wurin ciwon kuma”.
Cikin zuba mishi ido tace.
“Uhumm”. Sai kuma ya ajiye plate da cup ɗin a gefe kana ya miƙe tsaye,
hannunsa yasa ya miƙar da ita tare da cewa.
“Mu tafi bedroom”.
Kai ta gyaɗa kana ta juya kamar zatayi bedroom nashi, sai kuma tayi maza ta nufi ƙofar babban falon da sassarfanta tanayi tana buɗa sawunta alamun tana jin ciwon tafiyar.
Ganin kamar yana biyo tane yasa ta ɗanyi ƙara tare da cewa.
“Wayyo Ummey zai kamani”.
Sai kuma ta fara sassarfa tanayi tana yarfa hannunta.

Ido ya zuba mata yana kallon tafiyarta, cike da wani shauƙi. Murmushi yayi kana ya ɗauki sauran tea ɗin ya shanye.
Ajiye cup ɗin yayi ya tsallaka kwanukan ya nufi bedroom ɗinsa dan gaba ɗaya jikinsa ba ƙarfi yakeji ga alamun zazzaɓi ga bacci ga wani masha’hurin farin ciki.

Yana shiga ya kwanta lokacin ɗaya kuma bacci yayi gaba da shi.

Aysha kuwa a can falonsu ta samu Ummi, riƙe waya da alamu da Umaymah take mgna.
Tana ganinta ta mike tsaye tare da kamo hannun ta, bedroom ɗin Ayshan suka nufa tana mai cewa Umaymah.
“Alhamdulillah komai ya kusa baiyana da izinin ubangiji.
Gata ma”.
Ta ƙare mgnar tana miƙawa Aysha data zaunar a bakin gadonta waya, cikin sanyi Aysha ta amsa kiran da Umaymah tayi mata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button