GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Numfashi ya ɗan fesar a sanyaye kana ya juyo da kyau ya fuskanceta, sannan ya matsota ya manna bayanta da ƙorjinsa.
Da sauri ta buɗe idonta tare da buɗe baki zatayi mgna sai kuma tayi shiru jin ya sunkuyo kanta kanta sosai daga koncen, kanta ya ɗaga kana ya ture pillow’n da kanta yake kai, sannan miƙar da hannunshi a wurin,
kanta ya kwantar bisa damtsen hannunshi da ya miƙar, kana ya juyota rigingine, ƙafarshi ya ɗan ɗaura gefen cinyarta kaɗan,
kana yaja cinyarta yasa tsakankanin cinyoyinshi.
a hankali ya fesar da numfashi kana murya can ƙasa yace.
“Shike nan baki da iska.
Kiyi haƙuri, Umaymah kawai na gayawa fa.”
Cikin wani irin masifeffen sanyi da jin daɗin kulawarshi gareta a hankali tace.
“Toh, amman Yah Sheykh da gaske inada iska ne wai”.
Kanta ya shafa kana yasa bakinshi ya sumbaci goshinta cikin son kawar da tambayar tata yace.
“Me Jahan ɗinkin yake miki in yazo wurinki? Yana mgna ne? In yanayi me yake ce miki?”.
Baki ta tura tare da cewa.
“Ni dai ba Jahan ɗina bane”.
hannunshi yasa a hankali ya fara janye dogowar rigar jikinta yanayi sama dashi kana yace.
“To na ji, me yake miki?”.
Cikin takaici tace.
“Ba kanaga kamar wai al’januna bane sai kake ɗaukar abin wasa to wata rana sai yamin ciki ai da ƙarfi”.
Cikin sauri ya rumtse idonshi da ƙarfi tare da yin sama da rigar sosai kana a hankali yace.
“Na yarda ai baki da al’janani.
To amman ta yaya zai miki ciki”.
Juyowa tayi ta fuskanceshi da kyau kanta na damtsen hannunshi, tattausan gemunshi na taɓa goshinta, cikin muryar da tafi kama data tsoro da raɗa tace.
“Duk fa lokacin da ya zo na ganshi sai yayi kissing lips ɗina.
Ɗazu kuma harfa kwance min igiyoyin wuyan rigata yayi, gasuba har yanzu ban ɗauresu ba”.
Cikin hikima ya zare hannunta ɗaya cikin rigar kana ya zare ɗayanma sannan yace.
“To sai kuma yayi me daya kunce igiyoyin?”.
ya ƙareshe mgnar yana ajiye rigar tata bisa inda ya ajiye al’kyabbar shi.
Kana ya zare jallabiyar jikinshi, ya ajeta, sannan ya matso gareta tare da jawo musu blanket yace.
“Uhumm”.
Cikin tsurawa inda yake ido tace.
“Harda sa hannunshi cikin rigata, kuma yana mammatse min ƙirj..”
Da sauri ya lumshe idanunshi tare da jawota jikinshi ya matseta gam har saida tayi ƙara sabida matsar tayi ƙarfi, shi kuwa Sheykh gaba ɗaya jikinshi tsuma yakeyi ya gama gamsuwa Shatu Mar’atussaliha ce.
Ya yarda ita bata da wanda ta yarda dashi a Masarautar Joɗa sama dashi bata ɓoye mishi komai, ya kuma gamsu da son kiyaye lfyarsa da takeyi.
Cikin wata iriyar fitinenneyar murya mafi daburcewa yace.
“Bana son ji, kuma kodama al’janin nakine, zanyi mgninshi da izinin Allah, bashi da hurimi da mallakin Muhammad, shi kaɗai yake mallakar abunsa, kuma ko gani nai wani bazai yiba in sha Allah a mutum dai babu mahaluƙin da zai min kutse a gidana ma bare a kan iyalina.”
Ita dai ba jinshi sosai takeyi ba, sabida wasu abubuwan da yakeyi mata sun zarta abinda Jahan ya aikata mata.

Dib, dib, dib, haka zuciyarta keyi lokacin da taji ya haɗe lips ɗinshi da nata, kana tattausan tafin hannunshi na yawo a cikin dukkanin sasan jikinta.
Gaba ɗaya sai tsoro ya rufeta, a hankali taketa jujjuya kai alamun a a.
A hankali ya rabe lips nasu, cikin sanyi tace.
“Ya Sheykh bacci nakeji”.
Uhummm yace kana ya gyara musu kwanciyar.

A can ƙasar Cameroon kuwa.
Ba’ana ne zaune gaban wani ƙasurƙumin bokanshi mai ƙara buɗa mishi ido, da koya mishi siddabaru iri-iri.

Wani ƙaton kaskone a gabansu.
Cikin muryar da babu daɗin amo boka Dumba ya cewa Ba’ana.
“Leƙa ka gani, gacan ajiyarka tana kwance tana bacci lfy lau babu wani mahluƙin namiji da zai iya taɓa koda farcenta ne bai mutuba, bare har ya shafeta ko ya kai ga taɓa wani sashin sirri na jikinta bare a kai ga ya kusanceta”.
Tuni Ba’ana ya leƙa kanshi yana ƙarewa fuskar Aysha kallo, cikin jan dogon numfashi yace.
“Boka Dumba to shi wannan haskenfa da yake kwance kusa da ita menene shi kuma wane haskene ya zagaye ɗakin da fuskarta?”.
Cikin yin cacuɓe-cacuɓenshi yace.
“Wannan haskene dake wanzu da izinin ubangiji haskene dake kare wanda ke kusa da ita sam bamu da tsumi ko dabarar ganin komai a kanshi, sabida shi mutum ne da bakinshi baya bushewa da ambaton Allah kana baya rabuwa da al’wala a jikinshi.
Ita kanta in dai tana kusa dashi ainun jikinta ya taɓa nashi to bazamu ga komai a kanta ba, batun kusanta ne dai tabbas babu mahaluƙin da zai kusanceta ya rayu, domin madadin ɗanɗanon ni’imomin da ko wacce mace take dashi, in namiji ya sadu da ita, to ita dafin kuna da macijiya ne ni’imarta zata shigeshi a sashi mai tsada a jikinshi kan gari ya waye zai mace ya bar duniya”.
Wata iriyar muguwar dariya suka kece da ita kamar zasu fasa kogon da suke ciki, boka Dumba ne yaci gaba da cewa.
“Kai dai ka gama aiyu kan ka hankalinka kwance, shi wannan da yayi sanadin faɗinka gasar Shaɗi har yasa kabar ƙasarku, tuni munsa ajalinshi a jikin matar da yakega matarsa ce, kaga koda baka tare da Shatu zata tayaka yaƙi ba tare da ta sani bama”.
Cikin jin daɗi da baƙar mugunta Ba’ana yace.
“Dole ma ya mutu, sai dai babarsa ta haifi wani hegen bafullatani mai jajayen kunnuwa”.

Daga nan sukaci gaba da hirarsu da tanadin hana fulanin ƙasar Nigeria da Cameroon zaman lfy.

A nan Ɓadamaya kuwa, cikin Masarautar Joɗa, a wannan lokaci na tsakiyar dare.
Suka fito cikin masarautar suka nufi gidan boka Tsitaka, garin yayi duhu yayi dim sai azabar zafi da ake tsulawa zafi irin na tsakiyar damuna irin wanda in an kwana biyu ba’ayi ruwan samaba, bisa alamu hadari ke diddigowa daga ƙasa shiyasa garin yayi dim babu alamun iska.

Suna shiga Boka Tsitaka ya kwashe da dariya tare da cewa.
“Lbri mara daɗin gashi can konce da matarsa bisa gado ɗaya, sai dai kun san ɗan naku ba’a iya ganin sirrinshi, ko matar tashi bana gani sai wani haske daya rufesu.
Kuma yana gab da ɗirkawa ƴar fulani ciki hegen yaro dan yanada ƙoyayen haihuwa da ƙenƙesa”.
Cikin tashin hankali ɗayan yace.
“Kusantar mata harda haihuwa, anya kuwa bazan sa a dandatse min wannan yaron ba, shin wai shi wanne irin mutum ne da baya jin sihiri da tuggu da makirci”.
Ɗayan ne yace.
“Ai kuwa koda ya haihu yarane dai bazasu rayuba”.
Dariyar mugunta Boka Tsitaka yayi tare da cewa.
“Ku dai kun iya kawo aiki kun kuma iya faɗin mugunta sai dai tabbas akwai wani wanda yake gefenku, da yake aikata musu fiye da shirinku, kullum in kun tuna yimasa wani abun kafinma kuyi abun zakuga fiye da hakan ya faru tun shekarun baya.
To bare kuma yanzu an sake samun wani taƙadirin ma yasa mishi ido”.
Dariyar jin daɗi sukayi kana sukaci gaba da muhawarar mugunta.

Washe gari azahar Gimbiya Aminatu ce zaune gefen Lamiɗo da ya kira Sheykh suna gaisawa, tare da cewa.
“Muhammadu Akwai babban uzurin dake buƙatar ka dawo gobe”.
Gyara zamanshi yayi tare da kallon Aysha dake gefenshi ita da Hibba da Jalal da sune suka kawo musu abinci a hotel ɗin da suke. Maida kanshi yayi ya jingina da kujera kana ya lumshe idonshi tare da cewa.
“Eh dama gobe zamu taho, amman sai dare jirginmu zai tashi.
Su Ya Hisham da Affan kuwa sunce sammako zasuyi wai tafiyar mota zasuyi”.
Cikin sauƙe numfashin Lamiɗo yace.
“To Allah ya kaimu ya kuma dawo daku lfy, itafa Juwairiyya sai yaushe zata dawo”.
Kanshi ya ɗan mirgina kana yace.
“Zan dai taho da Ya Jafar da Jalal, in bata gama uzurorinta ba, sai ta koma masarautar Jadda ta dawo daga baya.”
Cikin gamsuwa da hakan Lamiɗo yace.
“To hakan yayi Allah ya kawoku lfy”.
Amin Amin yace kana ya katse kiran.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button