GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Shi kuwa Sheykh tana fita.
Ya bita da ido da wani murmushi mai tarin manufofi.

A hankali ya ɗan sunkuyar da kanshi ya kalli jikinsa.
Wani dogon numfashi ya fesar kana ya juya a hankali ya shiga ɗakinshi kai tsaye Bathroom ya faɗa.
Ruwan sanyi ya sakarwa kansa, wai ko zai samu nitsuwa.
Alhamdulillah kuma ya samu nitsuwa, haka yasa yayi al’wala bayan yayi wonkan.
Wata jallabiyar ya zura.

Yana fitowa yayi walaha. Kana ya kimtsa cikin wani farin yadi mai ɗan karen kyau da taushi yadin farine ƙal ɗinkin riga da wondo da gyariya ne.
Gariyar tasha aikin hannu da zare surfani royal blue sosai ya fito ras.
Hula damanga ya murza a kanshi itama royal blue.
Tattausan sajenshi ya kwanta lib. gashin kansa kuma yi lib ta gefe gefen kanshi da ƙeyarsa.
Wasu takalma sau ciki yasa suma royal blue.
OudKareem ɗinsa mai sasayyan ƙamshi ya fesa a duk sasan jikinsa, kana ya ɗauki wayarshi dake gefen gado ya zura a al’jihun gariyar.

A hankali ya fito falonshi. Cikinsa ya ɗan shafa tare da cewa.
“Wayyo Mamey na Yunwa”.
sai kuma ya zauna bisa kujerar da suka gama bidirinsu shida Shatu.

Murmushi yayi ganin wayarta a gefenshi. Kai ya jinjina yana mai jin masifar daɗin wannan yanayin da suka kasance a ciki.
Abincin ya zuba, a plate ya faraci yana ɗan kurban kunun nono mai ɗumi wanda yasa a kofi.
Sosai yaji daɗin kunun sabida yayi ɗan tsami.
Sosai abin ya bashi mmki domin shi dai baya son abu mai tsami ko kaɗan.
Amman yau yanajin daɗin tsamin da kunun yayi sosai a bakinsa.

Sosai yaci abinci wanda rabonsa da haka, tun kafin su dawo Tsinako auren Haroon”.

Koda ya gama komai.
Sai ya rurrufe ko ina na gidan kana ya fito.
Sabida yau ɗin yana son zuwa gidan Malam Abubakar malaminshi kenan?”.

So amman zai shiga wurin Lamiɗo tukun.

Su Ummu kuwa a gidan Hajia Kubra sosai taji daɗin zuwansu matuƙa.
har taji jikinta ya ɗan ƙara worwirewa.

Hira sosai Ummi da Hajia Kubra da Aunty Juwairiyya keyi.

Shatu kuwa da Samira matar ɗan Hajia Kubra suka tafi sashinta, Samira nada saukin kai da saurin sabo da ɗan karen surutu.
Haka yasa taja Shatu da zance sosai.

Shi kuwa Sheykh yana shiga Part ɗin Lamiɗo kai tsaye har bedroom ɗinsa ya wuce.
A bakin ƙofar ya ɗan tsaya tare da yin sallama.
“Wa alaikassalam. Jabeer shigo”.
Yaji Galadima ya amsa mishi tare da bashi umarni”.
A nitse ya shiga.
Zaune ya samesu.
da wasu takardu a gabansu.

A hankali ya zauna gabansu kana fuskancesu da kyau.
cikin nitsuwa yace.
“Na’urar CCTV Cameran dake sashin berbelar ya samu matsala.”
Da sauri Lamiɗo yace.
“Tun yaushe.”
Kanshi ya rausayar kana ya ajiye system ɗinshi a gabansu.
Kat rida ya ɗan zaro cikin ɗan wani ƙaramin abu dake hannunshi gefen System ɗin ya soka abun kana ya ɗan danna play sannan ya juya system ɗin ya fuskancesu.

Cike da mamaki suka zuwa system ɗinshin ido.

Shatu suka gani tsaye tsakiyar falon Hajia Mama.
Ita kuwa Hajia Mama, tana zaune bisa kujera.
Batool kuwa na can gefe.
Wani irin taku na isa da rashin tsoro Shatu takeyi har ta isa gaban Hajia Mama.
Da gaba ɗaya jikinta kerma yake dan masifar ɓacin rai.
Cikin isasshiyar murya Shatu ta nunata da yatsarta manuniya kana tsuke tace.
“Uhummmm in ke Halimace Ni Shatu ce. Ni nan da kike gani wargice dai-dai da ƙugun duk wani mugun Masararutar Joɗa”.
Da sauri ta ɗagawa Batool hannu jin ta taso zatayi mgn cikin isa tace.
“Ke kul kada ki kuskura kice zakiyi mgn a kaina, ki tsaya iya matsayinki.
In kin samu mijina ya kalleki koda kallo biyu a wuni ɗaya to Ni kuwa Ni Shatu zan sashi ya aureki ba dai shine burinki ba, to ki kama kanki ki bari sai kin zama matar ahlin masarautar Joɗa kafin kimin mgn”.
Cikin shakku Batool ta koma ta zauna tare da zuba mata ido.
Ita kuwa Shatu yatsunta ta murza kana cikin haɗe fuska tace.
“Gsky na jinjina miki kin cika muguwa. Halima, dama mugu bai cika mugu sai ya boye kamanninshi.
To ki kula ki fita rayuwar mijina, wlh ki rabu dashi da ƙannenshi da yayanshi.
Ki kiyayeni kijin tsoron randa zan miki wankin babban borgo a masarautar Joɗa.
Wato ke gaki shegiyar makira munafuka mai fuskoki goma da ashirin ko, kina tare dasu kina cin dunduniyarsu kinata ciyar dasu mganunnukan tsafinki. To a hir ɗinki, wlh ko ciwon farce Mijina yayi ko ƙannenshi nida ke bibbiyu, kin sanni Ni dake kar tasan karne.
Kika kuskura kika sake aika min wani abu Part ɗina, babu shakka ubanki zanci.
Wato ke a dole kina jiran inzo in baki haƙuri ko?
To jira zakisha mmki”.
Tana faɗin haka ta juya ta fita.

Ita kuwa Hajia Mama cikin wani irin tafasan zuciya tace.
“Uhummmm yanzu za’a fara wasan”.
Cike da mmki da rashin sanin manufar zancenta da kalaman da Shatu tayi Batool tace.
“Hajia Mama, wai meke faru ne, me tsakaninki da ita, ko dai kawai dan ina son Sheykh ne ta tsaneki”.
Wani mugun harara Hajia Mama ta watsawa Kubra kana ta juya ta nufi bedroom ɗinta tana huci kamar zakanya.

Kusan a tare Sheykh Jabeer da Lamiɗo da Galadima suka sauƙe ajiyan zuciya, cikin murmushin Galadima yace.
“Alhamdulillah yarinya ta fara yaƙin kare mijinta”.

Murmushi Lamiɗo ma yayi kana yace.
“Alhamdulillah komai na tafiya yadda muke zato”.
Cikin taɓe baki Sheykh yace.
“To waya sata, ko ce mata akayi ban san waye Hajia Mama bane, ko ta fini saninta ne.
Ya za’ayi muna ɓoye abu tsawon lokaci ita zata zo ta nuna ta sani. Ai da bata jira kantaba kuma, tasha ciwon hannu”.
Murmushi Lamiɗo yayi kana yace.
“Koma mene dai a kanka takeyi”.
Kanshi ya kauda yana mai jin wani sanyi murmushi mai yalwa ne ya subce mishi kana yace.
“Uhumm wai mijinta ko kunya babu”.
Sai kuma ya haɗe abubuwan nashi kana yace.
“To nadai sa Jalal ya sake dasa wata Camerar ya kuma sake dasawa, ita kuwa sakarya kallon bugegge takewa Jalal in yana sade ɗinta tana mishi kallon kare da uban gidanshi bata san a tsakiyar tafin hannunmu takeba Jalal ya fita sanin makaman ɓoye abu.”
Yana faɗin haka ya nufi woje tare da ce musu lokacin salla yayi.

Nan masallacin Masarautar Joɗa yayi sallan azahar kana ya wuce gidan Malam Abubakar.

Koda yaje ya sameshi da baƙi.
Haka yasa suka zauna nan suna tattaunawa saida akayi sallan la’asar kafin baƙin suka tafi.

Nan suka samu suka zauna suna tattauna matsalarsu.
Har magriba tayi, sukayi salla a masallacin ƙofar gidan Malam Abubakar ɗin, basu fitoba saida sukayi isha’i.

Suna fitowa kuwa yace zai tafi.
Malam Abubakar ɗin yace a ai dole fa ya tsaya suci abinci.

Dole suka koma falonshi.

Baici komai ba sai kunun tsamiya da yasha.
Sabida sam bakinsa ba daɗi. Gashi yana jin zazzaɓin nan nashi na dare ya fara rufeshi.

Suna gama cin abincin kenan wasu mutane biyu mace dana miji suka iso falon bisa jagorancin ɗan Malam Abubakar ɗin.

Ya yunƙura zai miƙe ya tashi kenan sai kuma ya koma ya zauna jin Malam Abubakar na cewa.
“A a tsaya Muhammad ban gama da kaiba zauna ba matsala”.
Cikin sanyi yace.
“To”. Kana ya koma ya zauna.

Shi kuwa Malam Abubakar a hankali ya juyo ya fuskanci baƙin nashi bayan sun gaisane sukayi yar mgnarsu kana suka tafi.

Gyara zamanshi yayi ya fuskanci Sheykh da kyau cikin nutsuwa irin ta manyan dattijai yace.
“Muhammadu wlh wani tsautsayi ne ya ritsa Sulaimanu”.
Cikin nitsuwa Sheykh ya kalleshi.
Domin Sulaiman abokinshi ne, sabida shi ƙanin Umma matar Malam Abubakar ne, tare sukayi karatu da Sulaiman a wurin Malam ɗin shiyasa ya sanshi sosai, suna mutunci kuma.
Sulaiman ɗan kasuwane saye da sayarwa yake na golagolai masu tsadar gaske, yana zuwa sari ƙasashen ƙetare da dama yana kawowa Ɓadamaya inda yakeda manyan shagunan shi na saida golagolan. Ya haɓaka yayi ƙarfi sosai.
To matsalar rufe boda data shafi duniya baki ɗaya ne, ya sashi fara sari nan cikin ƙasar.
Yakanje wasu jihohin ya tsara.
A irin hakane ya faɗa hannun mugaye suka sarar mishi golagolan matar gwamnatin wata jihar mafarin matsalarsa kenan.
Haka yasa hukuma suka kamashi.
To shine damuwar ahlinsu baki ɗayansu.
Hankalin kowa ya tashi.
Sabida Sulaiman shine jigonsu.
Mutun ne mai tausayin yan uwansa.
Cikin sanyi Malam Abubakar ya gama yi mishi bayanin ya ƙara da cewa.
“Muna barar addu’arka Allah ya kuɓutar dashi ya tsareshi ya fito dashi lfy.
Kuma ina akwai taimakon da zakayi mana muna buƙata, yanzu haka ita Ummun taku tana can gida sun.”
Cikin tausayawa da tabbacin Sulaiman mutumin kirkine ƙaddarace tazo mishi a hakan yace.
“In sha Allah zamuyi ta addu’a, kuma da izinin ubangiji zanyi ƙoƙarin ganin ya dawo gidanshi”.
Cikin jin daɗi Malam Abubakar yace.
“Alhamdulillah Ngd matuƙa, Ataimaka Muhammad”.
Cikin tausayawa yace.
“In sha Allah kuwa”.
Daga nan sukaci gaba da tattauna matsalar.
Yayinda sosai yakejin azabebben zazzaɓin yana rufeshi.
Sai ƙarfe tara ya sallami Malam ya fita ya tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button