GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Laminu kuwa wani irin masifeffen jin daɗi yakeyi, hakan yasa ya ƙara kutsowa cikin filin hakan ya bashi daman yin viewing da kyau.

Shi kuwa Jabeer tafarfasar da zuciyarshi keyi yayi masifar tsananta lokacin da yaji, Galadima ya zare mishi tattausar rigar shaddar dake jikinshi.
jin yasa hannunshi yana shirin zare mishi singlet ɗin jinshi ne yasashi, ƙara ambaton sunan Allah da sauri-sauri, sabida ji yakeyi tamkar ya buɗe ido ya shaƙo moƙoshin Galadima sai ya sumar dashi, tabbas da ace al’ƙalin gasarne ke cire mishi kaya da tuni ya daku.
Cak ɓari da karkarwan da jikinshi keyi ya bari,
Lokacin da yaji Galadima yasa hannunshi ya kwance zariyar dogon wondon jikinsa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun, Hasbunallahiwani’imanwakil.
Allahumma ajjirni fi musubati!!..”
Ƙasa idawa yayi, jin an saɓule wondon jikinsa yayi ƙasa,
da ƙarfi ya buɗe kwayar idanunshi da suka koma tamkar garwashin wuta. Tafarfasar da jininshi keyi shine abu mafi tartsatsi a rayuwarsa.
Hannunshi Galadima ya jawo da ƙarfi wanda dole yasa ya ɗaga sawunshi ya tsallake wondon ya zama babu komai a jikinshi dagashi sai Boxes wanda Allah yayi mai ɗan tsawone yazo har kusa da guiwarsa saidai a matse yake.

A tsakiyar filin ya tsaidashi kana ya juya ya koma ya zauna kusa da Lamiɗo.
Jalal ne ya sunkuya ya ɗauki wondon da sauri ya miƙa wa, Haroon.

Shi kam Jabeer zuwa yanzu,
Ya sani a duniya ba’a taɓa yi mishi tozarci sama da wannan ba, ji yakeyi a duk faɗin duniya babu garin daya tsana sama da garin Rugar Bani, bai taɓa jin haushi da tsanar wani abu a duniya ba sama da mutanen garin Bani, ji yakeyi ya tsanesu gaba ɗayansu, ya tsani komai nasu, baya so da fata da sha’awan komai nasu.
ƙasar garin ma da yake tsaye a kai ya zuba mata ido ji yake tamkar ya ƙonata ta sauya launi daga farin yashi zuwa baƙin yashi.

A tsakiyar taron kuwa, da sauri al’ƙalin gasar ya jawo hannun Ba’ana da ya zaro wata asirtaciyar bulalar tsamiya, daga cikin randar bulalinshi
sai wani motsi bulalar keyi tamkar tanada rai.

Bayan Jabeer al’ƙalin gasar ya kawoshi. Yana sake hannunshi masu busar al’gaita da sarewa suka farayi da ƙarfin su.

Lokaci ɗaya kuma ranar data take buɗe tarwal ta lumshe.
Mutanen kuwa sai tasowa da ife-ife akeyi. Kallo kuma kab ya dawo kan farar kekyawar fatarshi da kekyawan baƙin tattausan gargasa yayi mishi ƙawanya, iya kyan fatarshi kaɗai ya ishi ɗan adam kallo.
Da ƙarfi Jabeer ya taune lips ɗinshi, yana maiji tamkar zai hudasu sai ambaton sunan Allah yakeyi, babbar yatsar ƙafarshi ta dama yasa yana caka ƙasar garin, kana yatsunshi na hannun kuwa yasa babban yana zagaye kan ƴar manuniyarshi.
A yadda yake jin zafi da ƙuna da baƙin ciki a cikin zuciyarshi ya tabbatar babu wani abu da za’ayi mishi a yanzu yaji zafinsa fiye dashi, to me za’ayi mishi mai zafi sama da tsiraiceshi da akayi.

Ba’ana kuwa cikin dariyar mugunta da sautin amo mara daɗin ji, ya taƙar-kara ya ɗago bulaliyar asirin nan, da iya ƙarfin shi ya zabga mishi ita a tattausar fatar tsakiyar bayanshi.
Da ƙarfi su Jalal kab suka rumtse idanunsu.
Lamiɗo kuwa wani irin kallo yayiwa Jabeer da yayi.
Wani ir…..!

Biya darinki uku kacal domin jin wannan labari har ƙarshe.
Dan Allah da Manzonsa kada ku fitarmin da littafina.

Wannan shafin nakune gaba ɗaya waɗanda suka karanta FREE PAGE????????????????

                         By
            *GARKUWAR FULANI*Ido Laminu ya rumtse da ƙarfi. 

Ganin Sheykh Jabeer yayi wani irin tsayuwa na ingarman, jarumin namiji nitsuwa da kamala, sai lips ɗinshi dake motsawa a hankali yana ambaton Allah.
Shi kuwa Ba’ana cikin tsantsar mugunta, ƙeda, da zalumci ya ɗago bulalar nan da azaban karfi ya zabgawa mishi ita a inda ya zabga ta forko.
Wanda yasa gaba ɗaya mutanen wurin suka rumtse idanunsu.
Especially Lamiɗo da tawagarsa,
Shi kuwa Sheykh Jabeer, zuciyarshi ta rigada ta gama tafasa, idonshi baya ganin komai sai wani irin azabebben duhu, kunnuwanshi basa jin komai sai sautin muryar mahaifinshi da kuwa Umaymah. Da suke bashi umarnin cewa dole yayiwa Lamiɗo mubaya’a.
Wani irin azaba mai girgiza ran mutun a jikinsa yakeji yana sukarshi har cikin ƙahon zuciyarshi, sai dai duk wani sihiri na jikin bulalar duk baya tasiri a jikinsa illa dai dafin kuna min kam tabbas yana jinsu.
Barmuji wanda shine al’ƙalin gasar kuma mai irga bulalin.
Da sauri ya rumtse idanunshi lokacin da Ba’ana ya tsulawa Jabeer bulala ta biyar waccee, a take jini ya fara tsastsafo duk inda ta konta.

Arɗo Bani kuwa da Bappa da Alhaji Haro da Alhaji Umaru, da Sarkin aska, da sauran dattawan garin da kewayensa wani irin fargaba ne da taraddadi mai firgitarwa suke ciki.
Gaba ɗaya bakunamsu addu’o’in ne a ciki.

Laminu kuwa tuni yanata ɗaukar duk abinda ke faruwa a ƴar ƙaramar na’ura sa. Yanayi yana dariyar farin ciki.

Jalal kuwa da sauri ya rumtse idanunshi kana ya koma baya.
Jamil kuwa cur-cur yake zubda hawaye ganin yadda jini ke tsastsafo wa, a tsakiyar bayan Hammansun.
Haroon da kanshi tsoro ya rufeshi, yaji ranshi ya fara zargin anya kuwa bada biyu aka haɗa wannan gasarba.

Muryar Barmuji ce ta cika wurin gaba ɗaya da alamun tsananin tausayawa yace.
“Goma!”.
Alamar anyi mishi bulala ta goma kenan.
Shi kuwa Sheykh Jabeer Idonshi a buɗe suke, sai dai basa ganin komai sai duhu na tsantsar baƙin cikin abinda sashi yayi cikin bainal nasi a sashi tsayuwa da ɗan kampai,
Idanun nashi suna buɗe ras.
Launin su kuma ya sauya daga farin zaiba, zuwa jazir tamkar wanda maciji ya watsa dafi a cikinsu.
Gaba ɗaya fararen faratun yatsun hannunshi sun rine sunyi jazir tamkar wanda aka ƙunsawa jan lalle.
Ji yakeyi tamkar tsikarinshi akeyi da bakin allurai.
Tabbas duk da bai san dafin kunama ko macijiba, ya gane cewa akwai gubar dafin wani abu a jikin bulalin da ake tsula mishi tamkar za’a zare ranshi dasu.
duk ta inda hudar gashi yake a jikin shi, ji yakeyi tamkar ana soka mishi ƙarin kunamai.

Bukar kuwa, wani irin murmushin farin ciki yakeyi, ji yakeyi kamar ya fito ya taka rawa dan farin cikin ganin halin da jikan Sarki ke ciki.

Muryar na rawa Barmuji yaci ga da irge.
“Goma sha ɗaya! Sha biyu! sha uku! sha huɗu! sha biyar!!!.”
Cikin sauri Haroon ya iso inda suke, hankali a tashe ya kamo hannun Barmuji cikin sanyi yace.
“Kai kasheshi zakuyi ne? Bulalin har nawa ne za’ayi?”.
Cikin rawan murya Barmuji yace.
“In sha Allah bazai mutuba, bulali Hamsin za’ayi a ƙa’idar gasar, ba abinda zai sameshi tunda har gashi ya juri bulali 15 wanda a tarihin gasar Ba’ana babu wanda ya taɓa jurar koda bulala biyar ne”.
Da ƙarfi Hashim ya zaro ido tare da cewa.
“50 wannan ai zalumci ne”.
Da sauri Galadima ya miƙa ya nufi tsakiyar taron ganin Jalal ya nufi inda suke gadan-gadan bisa dukkan alamu kamo hannun ɗan uwan nashi zaiyi yaja su tafi.
Da sauri Galadima ya kama hannunshi cikin ɗaga murya yace.
“Kai Jalaluddin ina zakaje?”.
Cikin faɗa yace.
“Zan ja ɗan uwana mu tafi, in ku bakwa sonshi bakwa da buƙatar shi, mu muna sonshi munada buƙatar shi, a rayuwarmu domin mu dai shine farin cikinmu, shine silar zamanmu cikin masarautarku, da tuni kun koramu tamkar karnuka, shine kuka haɗa Deel a kashe mana shi, to kuji ku sani zamu bar muku masarautarku in dai ganinmu ne bakwa tson yi.”
Cikin faɗa Galadima yaja hannunshi yaje ya ajiyeshi gaban Lamiɗo.
Yana mai jin tausayin yaran.
Da ƙarfi Barmuji yace.
“Ashirin da biyar! Ashirin da shida!”.
Zuwa wannan lokacin gaba ɗaya jikin Al’Sheykh Jabeer Habeebullah yayi ruɗu-ruɗu. Tuni farin boxes dake jikinshi ya cika da jinin dake gangarowa ta bayansa da cikinsa, inda bulalin suke taɓawa duka.
Babbar yatsarshi ta ƙafar damanshi da yatsun hannunshi kawai yake motsawa, wanda suke nuna alamun yana nan da rai daram da kuma haiyacinsa.
Bayan wannan babu abinda yake motsawa a jikinshi,
Cake ƙasar garin yakeyi da yatsar kafar tashi.
yatsun hannunshi kuma, motsasu yake yana tasbihi dasu, wanda shima cikin zuciyarshi yake ambaton Allah dayi mishi kirari da kyawawan sunayenshi.
Zafin da yakeji a jikinshi tabbas ya wuce zaton mai zato.
Taune lips ɗinshi na ƙasa yayi da fararen haƙoranshi tamkar zai hudasu, sai dai har cikin ƙashin haƙoran nashi yake jin azabar dafin dake cikin wadannan bulalin masu masifar siddabaru, sai dai babu wani siddabaru da yayi tasiri a kanshi ko a jikinsa domin shi Allah ya riƙe, Ba’ana kuwa tsafi ya riƙe.
Wannan gasace tsakanin gsky da ƙarya, bawai gasar caɗi bane kamar yadda mutanen wurin ke kallo.
Haka yasa duk da safin wannan bulalin sam basu kai zafin da yakeji a ranshi na sashi ya tsaya gaban dubban al’ummar garin da ɗan guntun wonɗo a jikinshi ba.
Allah ya sani shi mai kunya ne, kuma shi mai suturce kanshine, shida kanshi yana jin kunyar kanshi da kanshi.
Baya zama haka ko a ɗaki sabida yana tuna in mafa ya kaɗaice yana tare da Raƙib da Atib Mala’iku makusantan ɗan adam, wanda in ka bar tsiraicinka ma su kauda ido sukeyi daga gareka.
Shiyasa shima yake kauda ido daga kan kanshima bare wani.
Allah ya sani babu wani abu da aka taɓa yi mishi a duniya ya ƙona mishi rai sama da wannan abun.
Tabbas da an barshi hakama, yafi jin zafin hakan sama da waɗanan bulalin.
A ranshi yake wani irin kuka mai cin rai yana mgnar zuciya.
“Anci min zarafi an wulaƙantani an tozarta ni a gaban waɗan mutanen da wasun cikinsu zindigan kafuraine. An barni tamkar mara kima da galihu, wannan shine iya maƙurar zalumcin da akayiwa rayuwata a karo na biyu”.
Sam baya jin zuciyarshi tanada raunin da zai iya zubda hawaye kan bulalin nan shiyasa ko zafinsu bai zame mishi abin zubda hawaye ko ihu da bakiba ko gudu ko wani motsi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button