GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Duk sukayi gaba, Sheykh kuwa na bayansu.
har yaje tsakiyar falon sai kuma ya ɗan tsaya jin Ummi na ce mishi.
“Shetu fa”.
Cikin saurin tafiya masallacin yace.
“Tana can ta faɗi wai ko ta karye ne naji tana cewa ban dai san mataba”.
Yana kaiwa nan ya fita, ita kuwa Ummi da sauri ta miƙe cikin zaro ido tace.
“Karaya kuma? Innalillahi yaushe”.
Tayi maganar tana nufar falonshi,
A bakin ƙofar shigowa sukayi kiciɓis da ita, da sauri ta tareta tare da tallabota, jin yadda jikinta ke rawane ta jawota suka fito falon cikin tausayawa tace.
“Sannu Shatu”.
Cikin tausaya Hibba taketa jera mata sannu.
Ajiyeta bisa kujera Ummi tayi tare da cewa.
“Baki sha ruwan ba ma ko?”.
Kanta ta gyaɗa mata alamar eh.
Hakane yasa Ummi tacewa Hibba ta ɗebo mata, abin shan ruwan a take kuwa ta kawo mata.

Bayan tasha ruwanne duk suka nufi cikin ɗaki dan yin salla.

Daga yin sallan magriba su Jamil suka dawo sukaci abinci kafin aka kira sallan isha’i, kana suka koma akayi sallan isha’i da asham sannan suka nufi harkokin su.

Shi kuwa Sheykh Jabeer daga Masallacin gidan Radio Ɓadamaya ya wuce, wurin yin shirin Fatawa.

Sai tara dai-dai ya dawo, gida.
A kitchen ya jiyosu.
Bisa alamu duk girkin abincin sahur sukeyi.

Shi kuwa bayan ya shiga, wonka yayi-yayi shirin bacci kana ya fito falonshi.

Soyayyan Arish da kwan ya ɗanci tare da tarfa ferfesun ya ɗan ci. masa biyu.

Jin cikinsa yayi tib ne, ya miƙe ya dawo falon.
zama yayi bisa kujera yana kiran Umaymah,
tana ɗagawa tace.
“Jazlaan ina autata, ya azumin yau dai?”.
Gajeren murmushi yayi tare da cewa.
“Umaymah autarki akwai raki, yau ita har ta fara lissafin an kai ɗaya saura 29/28”.
Dariya ta ɗanyi tare da cewa.
“Kaɗan ma daga aikin Hibba”.
Sai kuma tace.
“Ina ɗiyata kuma, ya azumin?.”
Kanshi ya ɗan jingina da kujera kana yace.
“Alhamdulillah”. Jin muryar Haroon na cewa.
“Wai ɗazu ina ka shigane inata kiran wayar ka baka ɗagawa”.
Gyara zamanshi yayi tare da kurban coffee ɗinshi kana yace.
“Na bar wayar a gida, da ɗaya na tafi na Fatawa”.

“To ya Amarya?”.

“Ban sani ba”.

Cikin dariya Haroon yace.
“Allah baka haƙuri”.

Amsar wayar Umaymah tayi sukaci gaba da mgnar kan tafiyarsu Umrah.
Daga bisani sukayi sallama, ya miƙa ya nufi ɗakin baccinsa.

A kitchen kuwa, bayan sun gama komai na sahur ne.
Ummi ta cewa Shatu taje ta ɗauko Foodflaks ɗin dake falonshi.

To tace kana ta juya ta tafi.
Koda ta shiga ɗan kalle-kalle tayi ganin baya nan, yasa ta harari falon ma gaba ɗayatare da cewa.
“Mugu”. Sannan ta ɗauki kwanukan ta fito.

Duk sauran abincin Saratu suka haɗawa ta kai musu ita da sauran hadiman.
Wanke-wanke tayi kana ta tattare komai sannan ta wuce part ɗin su.

Su kuma ganin har goma tayi ne, yasa sukayiwa juna saida safe duk suka shiga.

Yauma kamar daren jiya haka sukayi.

Washe garima haka suke tafiyar da rayuwarsu. Cikin tsari da kuma samun damar hutu da ibada dan ribatar watan Ramadan ɗin.

A hankali aka fara nisawa cikin watan Ramadan, kwanaki suna ɗan mirginawa da kaɗan-kaɗan.

Yau wunin azumi na biyar kenan.

Da hantsi bayan sunyi walaha sunyi karatun al’ƙur’ani.
Sanin yanzu Ummi na jin tabsir ɗin da yakeyi a masallacin Masarautar Joɗa ne yasa, Shatu tana gaisheta ta fito.

Hibba kuwa Side ɗin Aunty Juwairiyya ta nufa.

Ita kuwa Shatu falonta ta fito.
Bisa kujera ta zauna, tare da kiran
number Junaidu wanda Rafi’a ce, ta batashi data tare da bata haƙurin bazata samu zuwaba, sabida yayanta yazo sun koma jiharsu tare.

Ringing ɗaya ana biyu Junaidun ya amsa kiran ganin sabuwar number ne ya sashi cewa.
“Ban gane wake mgna ba”.
Cikin jin daɗin yadda taji muryarshi ras alamun ya samu lfy tace.
“Junaidu Adda Shatu ce fa”.
Da sauri ya tashi zaune bisa kekyawan gadon asibitin da yake kai tare da cewa.
“Laah Adda Shatu kece? Wlh ban gane muryarki ba, Adda Shatu ya gida ya kwana biyu, ya kewan gida, ya lbrinsu Junainah”.
Cikin sauri tace.
“Kai Junaidu duka wannan tambayoyin, ka bari mana in tambayeka ya jikinka, yasu Iri da Laure da Innaji da jikin”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah Adda Shatu duk jikinmu da sauƙin wasuma duk an sallamesu, yanzu nida Hamidu da Adamune kaɗai muka rage, kuma jikin da sauƙi sosai.
Sai dan Baba Madune yana shan wuya,
Satin daya wucema an sake yi mishi aiki”.
Cikin sanyi tace.
“To yanzu su waye ke kula daku”.
Kanshi ya rausayar tare da cewa.
“Uhumm mufa yanzu bamu da matsalar komai Adda Shatu kwantar da hankalinki, mun samu gata da kulawar wani babban likita mai mutunci.
An canza mana asibiti ma an kawomu wani asibiti kamar na ƙasar woje”.
Cike da jin daɗi tace.
“Alhamdulillah, dama dukkan tsanani yana tare da sauƙi”.

Dogon numfashi Junaidu yaja tare da cewa.
“Adda Shatu, ashe mun samu nasara, an kora mana mugun babarbarenen nan,”.
Uhum tace a taƙaice.
Shi kuwa Junaidu cigaba da mgna yayi.
“Adda Shatu Ya Salmanu ba lfy, yazo dubamu da jiki shima an kamashi gado.
Shi yake cemin wai su Bappa sun tafi Lardi. Ayyah Adda Shatu yanzu sai yaushe zasu dawo? Kina mgna dasu ne?”.
Cikin dariya tace.
“Faɗi gsky dai Junainah kake son tambaya dai. Junaidu.
Suna lfy ina mgna dasu. Sai bayan salla zasu dawo.”
Da sauri yace.
“Dan Allah Adda Shatu turo min number su”.
To tace tare da gyara konciyarta.
Nan dai suka ɗan yi hira, kana sukayi sallama.
Sannan ta tura mushi number su ɗin.

Suna gamawa ta kira Number Bappa.
Bugu ɗaya ana biyu ya ɗaga.
Cikin jin daɗin jin muryarshi tace.
“Ina kwana Bappa na”.

“Lfy lau Alhamdulillah Shatu ya Azumi, da baƙon wuri”.
Cikin sanyi tace.
“Alhamdulillah, Bappa yaushe zaku dawo”.
Dariya yayi mai ɗan sauti kana yace.
“Bayan salla”.
Cikin lumshe ido hawaye na zuba tace.
“Bappa ina jin kewarku, bani da kowa nawa kusa dani.
In na tuno su ya Giɗi hankalina na tashi Bappa inyi ta kuka babu mai sanin irin ciwon da nakeji a raina”.
Cikin sanyi yace.
“Kwantar da hankalinki Shatu, su Ya Giɗi suna raye, sai dai suna cikin mawuyacin hali, suna buƙatar addu’o’in ki musamman a cikin wannan mata mai alfarma, na sanki bakya wasa da riƙo da ibada, amman ki ƙara kan yadda kike, in sha Allah wata rana zasu dawo garemu, cikin sauƙaƙƙiyar hanya, addu’a itace abinda suke so, shiyasa na gaya miki abinda Allah ya nuna min a mafarki a kansu”.
Cikin sassanyan kuka murya can ƙasa tace.
“Zanyi Bappa zan ƙara zan dage, kuma zan roƙi a tayamu addu’o’in a masallatai da wurin tabsir.”
Cikin jin daɗi yace.
“Yauwa Shatu na, ki kwantar da hankalinki, ki zauna lfy da mutanen da kike tare dasu, kiyiwa mijinki biyayya, kiyiwa mayanshi biyayya bana son musu in babba ya gaya miki abu matukar bai saɓawa shariyar musulunci ba.”
Cikin sanyi tace.
“To”. Da sauri yace mata ga Junainah”.
Cikin jin daɗi tace.
“To a bata waya”.
Tsalle Junainah tayi tare da cewa.
“Adda Shatu, kizo Lardi garin da daɗi kullum sai an gasa mana zabbi ko Tattabaru, insha nono da zuma inci naman insha zuma, inci su inabi sai na ƙoshi”.
Cikin so da ƙauna da shaƙuwar ta da yarinyar tace.
“Allah sarki Junnu ke ko kewata bakiyi bako?”.
Dariya tayi tare da cewa.
“Nayi kewarku mana harda Ya Junaidu ma nayi kewarshki”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Na bashi number ku, zai kira ku gaisa”.
Tsalle tayi tare da nufar ɗakin Ummey.
Ita kuwa Shatu cikin dariya tace.
“Azuminki nawa”.
Da sauri tace.
“Azumi na ɗaya ranan nayi rabi daga safe zuwa azahar jiya kuma na ƙarisa rabin daga azahar zuwa mangriba”.
Wani irin dariya ne ya rufe Shatu dariya takeyi sosai.
Kewa da bege da son ƙanwar tata ya rufeta.
Da Sauri ta tsagaita da dariyar jin Junainah na cewa.
“Adda Shatu Bappa yayi aure an samo mana wata Inna mai kirki”.
Cikin mamaki tace.
“Ke Junnu ƙarya ba kyau fa”.
Da sauri tace.
“To ga Ummey ki tambayeta kiji”.
Ajiyan zuciya ta sauƙe jin muryar Ummey cikin sanyi da jin daɗi tace.
“Ina kwana Ummey na ya gida, ya Junnuna nayi kewarku, Ummey wai da gaske Bappa yayi aure”.
Murmushi mai faɗi Ummey tayi tare da cewa.
“To duk Alhamdulillah muna lfy eh Bappa yayi aure an bashi ƙanwar innarku, Indo kin santa ai ita take bin innarku, Bata taɓa haihuwa ba, to ashe mijinta ya rasu.
Shine yanzu aka aura mishi ita. Kuma tanada hankali kamar innarku”.
Cikin sanyin jiki tace.
“Eh na san Umma Indo tanada kirki, to Allah ya baku zaman lfy yasa kuyi irin zaman da kukayi da Inna”.
Amin Amin tace kana tai mata nasiha Sannan sukayi sallama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button