GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Jala, Jamil, Haroon, Hashim, Imran, Galadima, kuwa wani irin zazzaro ido sukayi.
Cikin tsananin kaɗuwa da firgicin batun Lamiɗo suka zuba mishi ido.

Bukar kuwa cikin karaji yace.
“Ba’ana Bukar shi zai kara dashi.”
Ya ƙarishe mgnar da fatan Ba’ana ya kashe wanda aka kira da Jabeer tunda jikan Lamiɗo ne.

Jabeer kuwa wani irin kallo yayi kakan nashi, irin kallon nan.
Na lallai kam tsohon nan ka haukace, ka zauce, ai bani bakam ko inuwata bazaku kuma gani a garinkuba bare kuyi wannan gwajin dashi.
Ga mamakinsu kab sai sukaji Arɗo Bani na cewa.
“A yau ɗinan kuma Yanzun nan, a kuma nan za’ayi gasar Shaɗi in har kun isa fulani.”
Sosai Lamiɗo yaji hakan bai mishi ba dan a zotonshi za’asa ranane ya koma ya shirya Jabeer kafin ayi gasar, to fahimtar ƙuresu suke neman yi, yasashi gyara zamanshi cikin danne fargabanshi na anya Jabeer zai iya jura yace.
“Na Aminc….!

Yau bisa wani uzuri ban samu yin posting da wuriba, kana kuma ba editing a gurguje na watsoshi, bari in nemo PAGE 16 ko zuwa yan da yamma ne.

                   By
           *GARKUWAR FULANI*

????????????????????????????????????????????

????????️????????????????????????

             *GARKUWA*

                      PAGE 16

                            NA
              *AYSHA ALIYU GARKUWA*

                 ????????????????????????????????

FREE PAGE SUN ƘARE DAGA WANNAN PAGE 16 DIN IN DAI KIKAGA LITTAFINA GARKUWA BA TARE DA KIM BIYA NA SAKI A GROUP BA TO NA SATANE, DAN ALLAH DA MANZONSA KADA KU FITARMIN DA LITTAFI DAN ALLAH KU BARI IN SAMU KUƊI zuwa makka????????????

Littafin GARKUWA na kuɗine dan Allah da Manzonsa kada ki karanta na sata, kada ki watsamin littafi a sata, turo katin MTN na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276 ki biya ki karanta cikin aminci ba tare da haƙƙi naba. Ko kuma ki biya 1k domin shiga Special Group wanda cikin sati biyu rak za’a gama Part 1, da izinin ubangiji kana a shiga 2, turo dubunki ɗaya ta wannan asusun 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidan biyanki ta wannan number 09097853276 in baki da halin biyan dubu ɗaya ko baki da ra’ayi kina iya turo ɗarinki uku kacal da ban tsauwalaba sabida halin rayuwa da muke ciki. Dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenki kada ki sai littafina in dai kin san niyarki ki saya ki fitar da shine in kuma. Har kin sayane to dan Allah da Manzonsa gaya min in baki kuɗinki in cireki a group na, dan Allah???????? nace badon niba

“Na Amince!”. Cikin tarin mamaki Jalal, Jamil, Imran, Haroon, Hashim, da duk sauran tawagar Lamiɗo suka, zazzaro ido cikin tarin mamaki da al’ajabi, sam basuyi zaton jin haka daga gareshi ba,
Ya Salmanu kuwa wani irin farin cikin mara misaltuwa ne, ya rufewa, domin yana ganin ikon Allah da yake nuna mishi zahirin abinda yake nuna mishi a mafarkansa tsawon kwanakin da yake a gadon asibiti.

Ba’ana kuwa da tun ɗazu ya iso, wani irin ihu yayi mai cike da farin ciki, da jin daɗin yana ganin zaiyi abinda gaba ko kashe mutanen Rugar Bani sukayi gaba ɗaya, masarautar Joɗa bazata kulasuba,
Wani irin tsuma da karkarwa jikinshi keyi sabida azabar muguntarsa dake tasowa.

Arɗo Bani ma wani murmushi manufa yayi tare da cewa.
“To, ina gwanin naku?”.
Cikin karaɗi Ɗanzagi, ya kalli Jabeer tare da cewa.
“Malami ba faɗen Allah, malamai magada annabawa, Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa, GARKUWAN sarki Lamiɗo, jikan sarki, mai martaba Nuruddee. Jarumin Masarautar Joɗa.”
Gimtse bakinshi yayi ganin wani irin kallo mai ma’anoni da yawa da Jabeer ke watsa mishi,
Cikin yin ƙasa da murya tare da tsuke fuskarsa, ya ɗan ronƙofo kanshi, kusa da Lamiɗo murya a kausashe yace.
“Wannan tatsuniyar da kukeyi, bafa koyarwan shariya bace”.
Da sauri Lamiɗo ya katseshi da cewa.
“Eh amman koyarwar Masarautar Joɗa ce”.
Cikin kufula yace.
“Ya ina ce maka Allah kana cemin gadon masarautar Joɗa ce”.
Cikin haɗe fuska da ƙasaita Lamiɗo yace.
“Eh ba addini bane, kuma sai an yishi dan gadon masarautar muce”.
Kanshi ya kuma motso dashi jikin kakan nashi cikin taɓe fuska yace.
“Okay to ai sai ka tashi, ka tsaya su zaneka ciki da woje”.
Cikin kausasa murya Lamiɗo yace.
“Kai ne dai zaka tashi”.
Cikin watsawa kakan nashi wani kallo na lallai ma tsohon nan kanka ya kwance yace.
“Ai bani bane sarkin, kaine sarkin ko?”.
Cikin faɗa Lamiɗo yace.
“To ko Ubanka bai isa in sashi abu yace bazaiyi ba”.
Jin muryar Lamiɗo ta ɗan yi samane, yasa fadawanshi suka miƙe tsaye,
Ware rigunansu sukayi, suka kamgesu da jajayen rugunan nasu, ta yadda babu mai ganinsu,
Cikin haɗe fuska Jabeer yace.
“Yesss shi bazai ƙiba, tunda kai ubanshi ne, Ni kuwa babu wanda zai sani in zauna in bawa wani ƙaton fatar jikina ya zane, kai jimin zancen son zuciya, kai ni kaɗaine jikanka, a duniya, a nanma baga Ya Hashim ba ai shine babban jikanka, zancen gsky na gaji da wannan tirsashe-tirsashen naku, kanada ƴaƴan ai, ka kira ɗaya daga cikin ya’yan ka yazo ya wakil ceka mana, Amman ni dai kam Muhammad Jabeer babu wani tsohon da zanyiwa mubaya’a in tsaya wani gardin makiyayi ya ɗimeni, tunda ba faɗin Allah bane”.
Ya ƙarishe mgnar yana yunƙirin tashi tsaye.
Da sauri Galadima yasa hannu ya kamo nashi, fuskar ya kwaɓe tare da komawa zaune yana gyara hiramin kanshi da al’kyabbar jikinshi,
Cikin tausasa harshe Galadima yace.
“Jabeer kafa san ma’anar GARKUWA a masarauta.”
Cikin sanyi da ganin kima da darajar dottijon Jabeer ya kwaɓe fuska tare da cewa.
“Nifa shiyasa wannan mulkin bawai sonshi nakeyi ba, sabida wannan tsarabe-tsaraben daba na addiniba, a buwayi mutun dashi, yaya nasan abu ba Allah ne da manzonsa suka wajabta mana shiba, ace in zauna a cutar dani.”
Cikin sanyi Waziri ke jujjuya mishi kai a hankali yace.
“Jabeer Garkuwa fa, kake dole ka kare martabar Masarautarmu kana ka nunawa su fulanin da kake Garkuwarsu kai Jarumine”.
Rai a ɓace ganin sufa da gske sukeyi, cikin dakiya yace.
“Bana so, ita wannan sarauta ta GARKUWAN FULANI ku bawa duk wanda kukeso, ni ban nemaba dama”.
Shiru Haroon yayi dan gskya harga Allah shi wannan abun yazo masa a bazata.
Jalal kuwa cikin haɗe fuska yace.
“Wannan ma ai zancen banza ne,
An bawa Ya Jafar Galadima, ko kwana ashirin baiba a kai, aka birkita masa rayuwa, kana yanzu kun likawa Hamma Jabeer wani GARKUWA kun kwasomu kun kawomu Rugar fulani, wai kuna cewa ayi gasar duka dashi.”
Da sauri yayi shiru ganin Jabeer ya ɗaga mishi hannu.
Jamil kuwa tuntuni idonshi ke tsastsafo ruwan hawaye dan gani yake so ake a kashe Hammansu a ƙarar da ƴaƴan ɗakinsu,
Laminu kuwa ɗan Gimbiya Saudatu matar bappansu Sheykh kuma Kani ga Yah Hisham wani irin dariyar jin daɗi yakeyi.

Shi kuwa Lamiɗo, wayarshi ya zaro, Mai alfarma Sarki Jalaluddin ya kira wanda yake kane ga Jabeer. Wanda ya haifi Mamanshi.
Bayan sun gaisane yayi mishi bayanin abinda ke faruwa, jin haka yasa yace ya bawa Jabeer wayar.

A tsakar filin Rugar Bani kuwa, tuni.
Arɗo Bani ya bada dama na suduka yana shekantawa gari cewa.
Ana gamgamin Shaɗi yanzu-yanzu tsakanin Ba’ana da kuma jikan Sarki Nuruddeen.

Tuni an firfito da ganguna anata kaɗe-kaɗe da bushe-bushen sarewa, kana ana buga babban gangan dake tsanar da makotan Rugar Bani sauran rugage alamun za’ayi Shaɗi yanzu.

Kafin kace kobo, Rugar Bani ta cika tayi maƙil da mutane, Maza da mata, matasa da tsoffi, sabida an san duk sanda za’ayi Shaɗi ana bada sanarwar, kwana uku kafin nan to jin wannan na gaggawa kuma da jikan Sarki za’ayi yasa, mutane taruwa, gashi ranar jumma’ace, duk matasan rugogin suna, gida tunda suka dawo sallan jamma’a.
Rugar Bani ta cika tayi maƙil da bani adam, tako wacce kusurwa tsastsafo akeyi kusufa-kusufa.
Jin karan tamɓarin ganganr Shaɗi ne ya ƙara gaiyato mutane harda na cikin garin Shikan, tuni ƙabilun Bonon sun garzayo cikin Rugar Bani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button