GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Dai-dai lokacin Larai ta shigo.
Bayan sun gaisa ne, ta ɗauki markaɗen waken ƙosan da zasuyi na kaiwa masallaci.

Da markaɗen tattasan da taruhu da al’basan.

Ita kuwa Shatu yau kunun basise ta dama mai kyau, ta cika kulolin.
Kana
Ta daura ruwan tea
Yana tafasa ta ɗura a flaks.

Duk wannan zabbin sunata sulaluwa suna bararraka sai wani irin masifeffen ƙamshi da yake tashi.
Har yawunsu na tsinkewa.

Fruits ta ɗebo a Fridge ta gyarasu ta shiryasu a tray biyu shiri mai kyau.
Kana ta medasu cikin ƙaramin Fridge ɗin data kashe dan sanyi su ya daidaita.

Larai na dawowa, suka fara suya.

Ita kuma ƙullun waken kaɗan ta ɗiba.

Kana tasa dafaffan ƙan data ɓare.
Da al’basan da kifin data tafasa ta murmusa a cikin ƙullun ta sa mai da Maggi curry da dai sauran kayan haɗi ta kulla alala.
Ta ɗaura a gefen tukunyar zabbin.

A ƙalla awa ɗaya zabbin na ɓararraka kana tazo.
Tasa jajjagen taruhu da al’basan,
A ciki.
Sai ta ɗan tarfa soyayyan mai kaɗan a ciki ganin kamar man jikin zabbin bazai mata yadda takeso ba.
Kayan ɗanɗano ta kuma sawa, da yankekken al’basa mai yawa ta zuwa a ciki.
Kana ta maida marfin tukunyar ta rufe. A hankali danderun zabbin ya fara taushi yana lugub cewa,
Ƙasusuwan suna saɓulewa daga jikin naman.

Tuni su Sara kuma sun gama soya ƙosan, nan ta ciccika kulolin da za’a fidda kana ta ɗiba musu nasu, daban.
Sannan suka tattare mata wurin suka tafi sabida ita ta kusa gama nata aikin.

Koda alalan ya nuna ta kwashe tasa a kuloli biyu.
Sai kuma ƙaramar kula daya.

Ya rage zabbin ne kawai a wuta.
Rage wutan tayi sosai yadda zasuke jin wutar na ratsasu da kyau.

Tattare wurin tayi ta kimtsa komai.
Kana ta fito falo.
Ƙarfe biyar da rabi.
Tace lokacin data zauna ta ɗauki wayarta Ummi kuwa na cire lallenta.
Ya kuwa yi baƙi yayi kyau.
Hibba ce ta shigo cikin
Langwaɓe kai tace.
“Aunty Shatu me ake dafa mana yau tun waje can ake jiyo ƙamshin na fitowa a gidanki”.
Cikin gajiya tace.
“Tuwone miyar taushe”.
Cikin zumbura baki tace.
“Tab wlh bazanci ba, inyi azumi a bani tuwo ta yaya zan haɗiyeshi, yaseen zan koma wurin Aunty Juwairiyya nagama tayi awara, ƙamshin gidanki na jiyo na gudo”.
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
“Hibba dai cokali a saki a daɗi ko?”.
Murmushi sukayi dukansu kana suka konta
A kan kujerun.
Ganin Ummi ta miƙene yasa Shatu cewa.
“Yauwa Ummi duba mana kitchen ɗin kiga ko Danderun yayi”.
To tace kana ta shiga ta duba.
Sannan ta fito tare da cewa.
“Yayi sosaima, kai gskyar Hibba nima da bana jin ƙamshi yau naji ƙamshin girkin.
Jeki sauƙe kawai kiyi wonka kuzo ki huta kafin a kira salla”.
To tace kana.
Ta miƙa taje ta sauƙe. Binta a baya Hibba tayi tare da cewa.
“Wai Aunty Shatu bakuga lallena bane banji kunce yayi kyau ba”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Kayya Hibba ai yanzu kam idanunmu basa gani”.
Ta ƙarshe mgnar tana sauƙe tukunyar,
Kana ta ɗauki Foodflaks guda uku biyu manya ɗaya karami.
Gaba ɗaya ƙasusuwan sun saɓule.
Romon yayi kaurin diddigin nama.
Rabin zabuwa ta sawa Sara da Larai a ƙaramar kular.
Kana tasawa Gimbiya Aminatu gudar.
Su kuma tasa musu ɗaya da rabin a kularsu.
Kular datasa alala data kosai ta jere a babban tray’n.
Da tray’n fruits, ɗin a gefe.
sannan da flaks ɗin kunu ta bawa Hibba tare da cewa.
“Ki kawai Gimbiya Aminatu.
Na ƙaramar kular nasu Sara ne”.
Amsa tayi kana ta fita.

A can ta samu Ya Jafar shida Lamiɗo bisa alamu yau tare zasuyi buɗa baki.

Ita kuwa Shatu Hibba na fita.
Ta sauƙe babbar tukunyar tafashen naman kajin ta ajiye gefe.
Dama zabbin duk a freezer’n suka sasu.

Ɗan buɗe bakin tukunyar tayi yadda zasu sha iska su kama jikinsu. Jajjageggen Attaruhu da al’basan kuma ta sashi a Fridge.

Kana ta fito da komai ta jere musu a dinning table.

Sannan ta wuce ɗakinta. Wonka tayi da ruwan sanyi duk da bata son sanyi
To amman duk jikinta huruwa yake tamkar wuta.
Haka yasa tayi da ruwan sanyi.
Tana fitowa ko mai bata shafa ba.
Wata atamta mai taushi riga da zani, ɗinkin Borno sitayel
yayi masifar yi mata kyau.
Ɗan kwalin ta ɗaura a sauƙaƙe sabida duk jikinta rawan yunwa da azaba yakeyi.

Cikin falon ta fito nan ta samu Hibba ta dawo.
Jalal, Jamil, suma sun zo.
Ummi ma ta fito da alamun tayi wonka.

Tana isa ana kiran salla.
Nan sukayi buɗe baki da fruits kawai sai kunun suka ɗansha, kana kowa yaje yayi sallan.
Sannan sukazo sukaci sauran kayan kwalamarsun.

Suna tashi sukayi sallan isha.
Zuwa lokacin kuma anata raɗe-raɗin ba’aga wata bafa.
Wannan lbrin shiya tada hankalin Hibba da sauran mutane irinta, a gefe harma da Jamil
Sabida azumi ɗayan nan da za’a ƙara wasu ganinshi suke kamar shekara ɗaya za’ayi ana azumin sai kaji anata gunaguni da cewa wai anƙi a faɗa ne.
Shatu kuwa murna tayi dan ita bata samu tayi lalle ba.
haka yasa gobe zata ƙarisa aikinta a nitse.
Jin an kira salla za’ayi Asham ne yasa Hibba zubda hawaye tare da cewa.
“Wlh zan kira Umaymah da Hamma Jabeer ina dai saudi sunyi salla Ni babu ruwana salla zanyi”.
Ta ƙarishe mgnar tana kiran layin Umaymah yanata ringin ba’a ɗagawa.
Hamma Jabeer kuwa data kira baya shiga ma gaba ɗaya. Haroon kuma shima yana shiga baya ɗagawa.
Dariya Shatu tayi tare da kunna tv tace.
“kalli Hibba suma asham sukeyi”.
Da sauri tace.
“A a kam Isha’i ne”.
Ganinfa da gaske Hibba keyi yasa suka sherata sukaje sukayi asham kana suka dawo.
Kitchen suka shiga, soya kajin sukayi suya mai kyau kana suka ajiye.
A gefe.
Jalal ne ya leƙo kitchen yace.
“Ummi azumi talatin zamuyi bana”.
Dariya tayi tare da cewa.
“Aiko gacan Hibba nata fushi.”
Shigowa yayi plate ya ɗauka ya miƙawa Shatu tare da cewa.
“Aunty a samin nan”.
Amsa tayi tare da saka mishi soyayyen naman kazan.
Dakekken yaji ta saminshi a gefen
Fridge ya buɗe ya ɗauki Du-du tare da cewa.
“Wannan fa yaushe aka fara kawoshi”.
Ummi ce ta kalleshi tare da cewa.
“Naga Shatu tafi sonshi ne yasa nace akawoshi”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“To nima bari in taɓa shi”.
Nan ya fita falon.

Su kuwa suka ƙarisa aikin.
Suna ƙoƙarin fitowa ne.
Jamil ya leƙo tare da cewa.
“To yau kuma meye za’ayi mana na sahur ne”.
Jalal dake bayanshi ne yace.
“Yo azumi ɗaya ai ko tazarce zamuyi”.
Hararan Jalal yayi tare da cewa.
“Hege daka ci kaji kayi tak ba, mutun kamar kura”.
Murmushi Jalal yayi tare da cewa.
“Yes naci in kuma ƙara”.
Hararanshi Jamil yayi tare da cewa.
“Mutun sai son nama kamar ba bafulatani ba sai kace babarbare”.
Da sauri
Jalal yace.
“Yo dama aini Arbabarbare ne”.
Dariya Ummi tayi,
Ita kuwa Shatu Jalal ta kalla tare da cewa.
“Me zan dafa mana to?”.
Tsaki ya ɗan ja tare da cewa.
“Kiyi mana Coucous da miyar hanta kawai”.
To tace kana ta juya ta fara aiyin.
Cikin sa’a ɗaya ta gama ta fito.

A falo ta samesu suna.
Waya da Sheykh yana ce musu kadafa suyi sakaci suyi sallan, dan babu lbrin ganin wata.

Hakan dai suka haƙura.
Bayan yaga waya da sune.
Umaymah ta shigo ta sameshi zaune yanacin inabi.
Gefenshi ta zauna da wata jakar.
Miƙa mishi tayi tare da cewa.
“Kace ranar salla da safe in an sauƙo idi dai zaku tafi ko?”.
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
“Haka dai Wannan tsohon Galadiman ya buwayeni da zancen komawar”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Abbanka ma yace min ranar sallan zaku tafi”.
Kai ya gyaɗa.
Ita kuwa gyara zama tayi tare da cewa.
“Tsarabar me ka sayawa Shatu da ƴar ɗakinta Hibba”.
Da sauri ya kalleta tare da cewa.
“Umaymah tsaraba kuma.
“Yo tsarabar me zanyi sai kace wani sabon zuwa, Ni ibada nazo yi ba tsaraba ba”.
Jakar ta nuna mishi tare da cewa.
“To ni kam ga tsaraba ka kai musu, wannan na Shatune Hibba gobe zan dawo da nata.
Kai kuma in kaso ka koma hannu rabbana”.
Kanshi ya sunkuyar kamar baijiba.
Sai kuma tace.
“Jazrah tace in gaidaka, wai tunda kazo bata ganka ba”.
Cikin sanyi yace.
“Yoh dama ya zanyi in bari ta ganni yarinya sai kallon masifa”.
Miƙewa Umaymah tayi ta fita.
Tana fita Haroon da Ya Hashim suka shigo. Nan suka ɗanyi hira kafin suka tashi suka tafi masallacin dan shabiyu ta kusa a fara tuhajjudin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button