GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ai da gudu fa Hibba taje ta gayawa Shatu.
Sosai taji daɗi har ta ɗan saki jiki.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, ko inda Foodflaks ɗin suke bai kallaba, sabida ba tsarinshi bane cin abu mai nauyi in dare yayi, haka yasa iya madarar yasha,
kana yaci gaba da aikinshi.

Washe gari ranar Alhamis, wuni Umaymah tayi tana shirye-shiryen komawa.

Ta sallami duk mutanen da take mutunci dasu a fadan.
Dama cikin masarautar Joɗa cewa Gobe jumma’a da mangriba zata koma.

Washe gari ranar jumma’a, da misalin karfe sha biyu.

Duk suna zaune a falon harda Jafar, Jalal, Jamil, Imrane, Ya Hashim, duk suna cikin shigar jumma’a.
Dakon fitowar Sheykh suke jira.

Umaymah da Ummi da Aunty Juwairiyya kuwa, suma suna nan, cikinsu ana ɗan hira.

Hibba kuwa da Shatu suna kitchen dan Hibba tace in Shatu ta iya awaran couscous ta koya mata.

Suna nan zaune, Hajia Mama da hadimanta
Suka shigo.

Cikin jin daɗi Umaymah tace.
“Yanzu nake tunanin zanzo Side ɗinki Adda na”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Oh ai bazaki zoba, yadda kike tsakiyar yaranki yar uwa kam an manceta”.
Murmushi sukayi baki ɗayansu,
Batool da yanzu ta shigo da wasu hadiman suna rirriƙe da manyan bokitayen kande tsiraran masu cike da markaɗeɗɗen gyaɗa na kunu da miya sai ƙananan su kuma turaren wutane a ciki da biyu ɗaya dakekken yajin daddawa ɗaya dakekken yajin borkono komai bibbiyu. Sai galullukan man shanu. Da na zuma sai na Humra, kana sai manyan bako guda biyu.
cikin murmushin Umaymah tace.
“Iye Addana me na samu hakane?”.
Cikin sakin fuska tace.
“Abubuwan daɗi nasan kina son kayayyakin gargajiya”.
murmushi tayi tare da cewa.
“Duka wannan ai yamin yawa”.
Kallon kayayyakin tayi tare da cewa.
“Keda su Ummi ne, suma za suyi amfani dashi a Ramadan, Musamman ma da ɗan naki anan zaiyi azumi bana”.
Cikin jin daɗi Umaymah ta kwallawa Hibba kira tare da cewa.
“Kizo keda Aunty naki”.
To sukace kana suka kashe Gas ɗin da yake dama sun gama aikin.

Suna isowa Hibba taje ta zauna kusa da Hajia Mama da sauri tare da cewa.
“Hajia Mama an barni a nan zamuyi azumi”.
Cikin murmushi ta shafa kanta tare da cewa.
“Kai naji daɗi na.”
Sai ta kuma kalli Aunty Juwairiyya tare da cewa.
“An kai miki naki kayan Side ɗinki”.
Godiya tayi.

Ita kuwa Umaymah hannun tasa ta jawo bako ɗaya ta zuge zib ɗin shi ta fara fiddo ledodin dake ciki wanda dakekken busasshen kayan miya ne kamarsu.
Kuka, kuɓe, daddawa, citta, kanumfari, ganyen na’ana, zogale, da dai ire-iresu ne a ɗaɗɗaure a manyan ledodin masu layin baki da fari.
Cikin jin daɗi kayayyakin Umaymah tace.
“Kai nako gode naji daɗin kayan miyar nan, dan mu wurinmu suna wuyar samuwa.”
Sai kuma ta juyo ta kalli Shatu dake zaune gefenta,
Tayi wani irin kici-kici da fuska babu alamun wal-wala.
Cikin nuna jin daɗi tace.
“Ɗiyata ga kyautan Hajia Mama, komai bibbiyu ne ɗaya naki ɗaya nawa ne, kiyi godiya”.
Cikin wani irin kallo mai cike da ma’anoni da sarƙafe-sarƙafe ta gyara zamanta, tare da komawa ta jingina da kujera, ƙafarta ɗaya ta ɗaura bisa ɗaya tare da fara karkaɗa ƙafar cikin fuska a haɗe kana a daƙile ta nuna kayan tare da cewa.
“Bama so, Umaymah Bama buƙata”.
Cikin tarin mamaki da al’ajabi duk suka juyo gareta suka zuba mata ido.
Ummi da Umaymah kuwa har suna haɗa baki wurin cewa.
“Sabida me? Akanme zakice bakya so?”.
Ba tare da ta kallesu ba tace.
“Ba cewa nai bana soba, cewa nayi bamaso, itama Umaymah bata so.”
Cikin tsananin mamaki suka bushe suna kallonta,
Jalal ne ya zuba mata ido cikin haɗe fuska.
Hajia Mama kuwa wani irin kallo mai cike da tsoro da mamaki da al’hini da jin tsanar Shatu cikin ranta, ta rasa me wannan yarinyar take nufi da ita,
ta kasa gano me take gadara dashi.
Cikin tarin takaici da zafin rai tace.
“To kuma baki isa da gidan ba,
Bare ki zana layi a biki, ke in banda rashin sanin darajar manya har zaki gaya min haka, ko gidanku ba manya ne?.”
Cikin isa da ɗaga murya tace.
“Yesss! Gidanmu babu manya irinka, Bama so bazamu amsaba ki tattara tarukucenki kije ki bawa wasu can ba dai muba”.
Cikin tashin hankali Umaymah ta daka mata tsawa tare da cewa.
“Ke Aysha ki nitsu kisan da waye kike mgna”.
Cikin ɗaga murya tace.
“Na sani Umaymah na sani nasan da wacece nake mgna kece bakisan wacece itaba”.

Cikin mamaki da sauri Sheykh ya ƙarisa fitowa cikin tamfatsen falon shi.
sabida ya gama shirin jummarsa,
jiyo hayani da hargowane yasa ya nufo falon da sauri.
To jiyo muryar Umaymah ne yasashi buɗe ƙofar falon da hamzari ya fito.

Da sassarfa ya nufo falon.
Dai-dai lokacin daya isone,
Aysha ta miƙe tsaye cikin faɗa da tsawa ta nunawa Hajia Mama da hadimanta da Batool hanya tare da cewa.
“Maza ku tattara waɗannan banzayen tarkacen naku ku tafi dashi, ku ɓace min da gani. Ku fita daga nan! Ku fitarmin gidana”.
Ta ƙarishe mgnar da ƙarfi.
Wani irin miƙewa tsaye Umaymah tayi tare da yin sauri tasa hannunta ta….!

                          By
              *GARKUWAR FULANI*

Ta kamo hannun Jalal da ya miƙe tsaye da nufin yarfa mata mari.

Cikin wani irin masifeffen tsana, Hajia Mama takalli Shatu.
Kana da sauri ta juya ta nufi hanyar fita.
Sheykh da tunda ya fito yake tsaye tamkar an dashi ne,
yayi saurin bin bayanta tare da cewa.
“Hajia Mama! Mama!! Mama dan Allah kiyi haƙuri, kizo karki fita Please Mama karki fita, babu wata halitta da zata miki iyaka da sashina, in kin tafi kenan kinbi umarninta.”
Cikin tashin hankali yake waɗannan kalaman yana mai binta a baya.

Jamil kuwa miƙewa tsaye yayi ya zubawa Shatu idanu tamkar zasu faɗo ƙasa.

Aunty Juwairiyya kuwa, wani irin kallo mai sarƙafe da ma’anoni takeyiwa Shatu.

Ya Jafar kuwa wani irin kallo mai surke da murmushin jin daɗi yakeyiwa Aysha.

Ummi kuwa tuni jikinta rawa yakeyi da abinda ya faru.

Imran, Ya Hashim, kuwa ido suka zubawa sarautar Allah.
Hibba kuwa kuka takeyi tare da riƙo hannun Shatu tana ja tare da cewa.
“Aunty Aysha ki bari, Mamace fa! Kizo mu tafi ɗaki”.
Tanayi tana jan hannun Shatu da ƙarfin tsiya, dole yasa Shatu ta bita a baya.

Umaymah kuwa wani irin tashin hankali da tafasan zuciyane ya dirar mata lokaci ɗaya.
Da wani irin kallo tabi bayan Aysha dashi.

Duk wanda ya ganta yasan tana cikin tashin hankali.
Gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi.
Sun daɗe a haka, da kyar dai
Cikin wani irin tafasan zuciya ta saki hannun Jalal.
Tare da komawa ta zauna.
Da yatsa ta nuna musu hanyar fita daga falon. Murya a hargitse tace.
“Kul kada ka sake tunanin gigin ɗaga kayi nufin taɓa lfyar Aysha, bana so kul.
Maza Ku tafi masallaci”.
Sai lokacin suka jiyo sautin muryar Jabeer yana Hudba.
Wanda daga jin muryarsa kasan yana cikin baƙin ciki.

Wani irin numfarfashi Jalal ya sabke tare da yin koffa kana ya juya ya nufi hanyar fita shi matsalarsa meyasa Umaymah na mgn Aysha na mgn Umaymah na hanata abu tanayi.
Haka su Jamil da su Imran da ya Hashim da Ya Jafar suka fita.

Ita kuwa Aunty Juwairiyya wani irin tashi tayi ta fita ta nufi Side ɗin ta.

Ya zama Ummi da Umaymah ne kaɗai suka rage a falon.

Shiru sukayi tamkar ruwa ya cin yesu.
“Uhuhhmmmm”. Umaymah ta fesar da wani zazzafan numfashi mai ɗumi.
Hakama Ummi tagwayen numfarfashi masu nauyi ta sauƙe.
Kallon juna sukayi, cikin shiga al’hini wannan al’amari cikin tsoro da karaya Umaymah tace.
“Toh wai meye hakan? Meke faruwa ne? Me hakan yake nufi? Kaina ya kulle. Wani zagon kasan kuma aka shirya tsakanin Shatu da Hajia Mama ko dai dama da zagon ƙasan ne?.
Wake saƙa gadar zare, muna na bi ta kai ya rubta da mu”.
Wani numfashin Ummi ta fesar tare da cewa.
“Tabbas akwai babban al’amarin dake faruwa wanda bamu saniba Ni tsorona ɗaya kada a juya ƙoƙwalwar yar mutane.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button