GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Dan Allah da Manzonsa in dai kin san zaki sayi littafinane ɗan ki fiddashi na roƙeki da Allah da Manzonsa da darajar su. Kada ki saya bana so, ki riƙe kudinki.

                        By
              *GARKUWAR FULANI*

????????????????????????????????????????????

????️????????????????????????????

             *GARKUWA*

                   PAGE 9

                            NA
              *AYSHA ALIYU GARKUWA*

   ????????????️????????????????????????????


    *FREE PAGE* 

TURO KATIN MTN NA ƊARI UKU KACAL ta wannan number 09097853276 DOMIN SAMUN DAMAR KARANTA littafin GARKUWA, ba tare da haƙƙin kowa a kankiba. Akwai Special Group shi kuma na 1k rak, ki turoshi ta asusuna na Jaiz bank. 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai ta WhatsApp 09097853276

~Ga masu buƙatar kayan gyara na amare, akwai set-set masu kyau, a ƙananan robobi masu sauƙin kuɗi, akwai kuma na manyan robobi masu zafi, akwiasu dai-dai da tsarin al’jihun mai ƙarfi da mai rauni, ina araha ina hana bashi. Koda kuɗinka saida rabonka, kayan Kamfani daban dana shago.~

Al’ummar Hausawa mazauna Saudiya wannan shafin nakune kyauta gareku, domin jiya da yau saida mai zaton babu wasu masu karanta littafi sama daku. Nasha mamaki da sanyin safiya naita cin karo da numbers ɗin ƙasa mai tsarki suna ta antayo min manyan kuɗi na ƙasa mai tsarki tun ina ƙidaya numbers ɗin +966 har dai abun yaci tura sabida yawansu, ashe daga zauren Umar Maisanyi sukayi ta antayowa gareni. Godiya mai tarin Yawa Umar maisanyi mai Tsakar gida You tube limamin tsakar gida

Walƙiya mai tsananin haske da tartsatsi wanda saida ya haska gaba ɗaya, dajin ya zamana, har kana iya ganin inuwar dogayen bishiyoyin wurin da sukayi musu ƙawanys.
Wani irin tsoro da firgici da karkarwan ne ya bijirowa Aysha.
Cikin dauriya da sabo da ganin ire-iren irin waɗannan ababen a wurin kiwo, Hinde ta kamo hannun Shatu tare da cewa.
“Kai Aysha babu komai fa walƙiyace kawai fa kai”.
Sai kuma tayi dariya tare da cewa,
“Uhum a hakan kike tunanin jurar taraddadin da muke gani cikin tsaunuka in muna kiwo”.
Janye jikinta tayi daga jikin Hinde, hannun tasa ta tattare gashin kanta dake baje a kafaɗunta, tubkeshi tayi cikin, fidda numafashin tsoro take karisa addu’o’in datake tayi a bakinta, a hankali taja da baya ta jingina da jikin ƙatuwar bishiyar Gamji dake gefensu, jingina kanta tayi jikin bishiyar gamjin tana jin yadda zuciyarta ke harbawa, pat-pat da azaban ƙarfi domin tasan Hinde bata san me idonta ke shirin hango mataba,
ita kuwa Hinde, a gabanta take tsaye ya zamana sun fuskantar juna.
Su Ya Gaini kuwa sun duƙufa kiwonsu kamar dai yadda suka saba, ruwa ko iska ko zafin rana da ƙishi baya kora makiyaye daga kiwo a daji ya dawo gida.
So duk kowa yana yankin da yake bawa dabobbin tsaro, sam basuma hango su Aysha sosai.

Ita kuwa Shatu idonta dake lumshe ta fara ƙoƙarin buɗewa sabida wani irin tashi da taji tsikar jikinta nayi.
Hinde kuwa ido ta zuba mata tana ganin yadda ƙirjinta yake sama da ƙasa alamun tsananin firgita.
A hankali ta ware manyan kyawawan idanunta.
Wani ƙaton curi, dake can bayan Hinde ta zubawa ido sabida wani abu da take gani kamar hayaƙi yana fitowa ta ƙananan ƙofofin curin. Ita kuwa Hinde bata san meke wakana ba sabida, ita baya ta bawa curin, asalima yanzu kanta ta ɗaga sama tana shan ruwan dake cikin goranta.

Ita kuwa Shatu so take ta janye idanunta daga kan wannan CURIN amman sai taji ta kasa, bugun da zuciyarta keyine ya tsananta, lokaci ɗaya jikinta ya fara tsuma da karkarwa zufa mai azabar zafi ta fara tsastsafo mata tako wani hudan gashin jikinta.
Yayin da zuciyarta. Ke harba jini one litter. A Cikin ko wanne one second. Bakinta ta buɗe da nufun furta addu’o’in dake jere a zuciyarta amman sai taji ta kasa, zuru-zuru tayi da idanunta lokacin da taga wani dogon abu yana fitowa daga cikin babban ramin dake tsakiyar CURIN nan, a hankali ta ɗaga kwayar idanunta sama tana bin abin da kallo, wani irin dogon numfashi taja, ganin abun nan yana miƙewa yana yin sama, abun dogo kamar igiya sai dai kuma yanada zane kala-kala red, yellow, green, blue.
Kuma abun biyune ɗaya a sama ɗaya a ƙasa, cikin ranta take iya ammabaton sunan Allah ganin zahiri fitowar bakan Gizo daga cikin curi Allah ya nuna mata, ras zanen bakan Gizon nan yayi kama da kalolin kolliyar jikin rigarta,
Kanta ta ɗaga sama, tana bin Bakan Gizon da kwayar idanunta, tana gani har ya haura sama can ya konta a gicciye gabas da yamma kudu da arewa, kana kuma mai hasken ras yana sama mai ɗan dishi-dishin yana ƙasa. Wanda a falsafar al’ummar Duniya ake cewa suma mata da mijine, muddin kaga mai hasken in ka zuba ido zakaga mai dishi-dishin wanda akecewa, mijin shine dishi-dishin kuma shike goyo matarsa shiyasa sai ake ganin mai hasken shine a sama.

Wasu irin numfarfashi take ja da azaban ƙarfi da razana, kar-kar haka jikinta ke rawa.
Cikin tsoron halin da take ciki Hinde ta wurgar da goran dake hannunta, tare da cewa.
“Hande en boni, yau munga ta kanmu Shatu me haka meya sameki?”. Ina babu mgna sai zamewa da ta farayi tanayin ƙasa alamun zata faɗi, ganin hakane yasa, Hinde juyowa da ƙarfi ta fara rabƙawa su Ya Gaini kira.
“Ya Gaini! Ya Seyo! Ya Lado, Wayyo Ya Giɗi kuzo kuga abinda Shatu keyi”.
Maganarta ta karshece ta sasu, tasowa a guje gaba ɗayansu suka nufosu da gudu,
kafin su isoma Aysha ta faɗi ƙasa zaune, sai karkarwa da rawan sanyi takeyi.
Suna isa Ya Gaini yasa hannu ya tallabota ganin yadda taketa karkarwa, idanunta na rufewa,
Seyo ne ya kalli Hinde cikin kiɗima yace.
“Subahanallahi Hinde me ya sameta?”.
Cikin kuka Hinde tace.
“Ban saniba wallahi haka kawai naga tana karkarwa”.
Giɗi ne ya zauna kusa da yayan nashi kanshi ya sunkuyo kanta yana kiran sunanta a jere a jere.
“Aysha! Shatu. Ayshatu tashi buɗe idonki ki gaya min meya sameki meke miki ciwo”.
Ina babu magana saima kara rumtse idanunta da tayi tare ƙara ƙaƙƙame jikin Ya Gainin nata.
Ya Lado ne da Seyo suka sunkuyo kanta addu’o’in suka rinka tofa mata, duk addu’ar da tazo bakinsu tofa mata sukeyi, Giɗi kuwa ruwa yasa a tafin hannunshi yana shafa mata a fuskarta.

Cikin al’hini sauran makiyayan duk suka iso kansu, ganin yadda suke birkice ne ɗaya daga cikin ƴaƴan Alhaji Haro da kuma Alhaji Umaru sukace.
“Gaini mu tafi gida da ita, tunda dama lokacin tashinmu yayi, an kusa fara tafiya masallacin juma’a.”
Cikin damuwa Giɗi yace,
“To ai bazata iya tafiya ba”.
Seyo ne ya miƙe cikin sauri yace.
“Bari inje in kawo doki sai mu ɗaurata a kai”.
Da sauri Manu ɗan Alhaji Haro yace.
“Yauwa yi maza, kunga ku kuma Gidi kuje duk ku haɗo mana kan dabbobi ku fuskantar dasu hanyan gida”.
Ai kuwa haka akayi sauran yaran duk suka kaɗa shanun.
Koda Seyo ya kawo dokin, shida kanshi ya hau baya sannan aka ɗaura mishi ita a gabanshi, a haka suka nufi gida.

Koda suka isa gida, da kanta ta taka har zuwa cikin gida, suna biye da ita a baya.
Kai tsaye ɗakin Ummey ta shige, bisa gado ta konta ta duƙunƙune tana rawan sanyi.
Da sauri Ummey da Inna da Junainah suka biyota a baya.
Cikin tsoro Inna tace.
“Subahanallahi Shatu meya faru”.
Ummey kuwa gefenta ta zauna, tare da jawo borgo tana rufe mata jikinta.
Giɗi ne da yanzu ya shigo, shine ya basu lbrin iya abinda suka sani.
Seyo kuma cewa yayi a mata hayaƙi.
Haka kuwa akayi sukayi mata hayaƙin kana Ya Gaini ya zauna yayi mata rubutu nanma aka wonke aka bata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button