GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Haka yammacin ranar ta yishi a bedroom ɗin ta.
Sai Hibba dake ɗebe mata kewa ne.
Da Umaymah taga basu fito bane itama taje.

Washe Gari yau Jumma’a, kuma yaune ta cika sati ɗaya cib a gida.
Kuma tunda yazo gidan sau uku taga Sheykh Jabeer, tun randa ya wucesu, suna batun abinci bata sake ganinshi ba, koda a gilme ne.
Yanzu ta saba da Umaymah Sosai hakama Ummi
Ita da Hibba kuwa shaƙuwa ta fara ƙarfi a tsakaninsu.
Tana jin Hibba kamar Junainah.
Jamil da Jalal Haroon suna ɗan zama asha hira dasu.
Yau ne kuma Haroon zai tafi Leddi julɓe, sabida yayi masifar kewan Jannart ɗin shi, wacce taƙe ƙanwace ga Aunty Juwairiyya, kuma ƙawance ga Ibrahim.

Ƙarfe ɗaya dai-dai, Sheykh Jabeer, ne tsaye gaban dreesing mirror yana fesa turare bayan ya gama shirin jummarsa tsab.
Yau shigar baƙar Al’kebbar da farar jallabiya yayi.
Yayi wani irin kyau mai cike da sheƙi.
Kusan a tare suka jero da Haroon wanda yake cikin shigar ƙananan kaya.

Su kuwa suna falon suna, zaune.

Jamil da Jalal da Ya Jafar kuwa suna tsaye alamun fitowar Sheykh suke jira.

A hankali Shatu ta ɗan ɗago kanta jin wani irin masifeffen ƙamshi mai daɗin shaƙa.

Da sauri ta janye ƙwayar idanunta,
Sabida idonta da suka faɗa cikin ƙwayar idanunshi.
Wanda shi kuwa Jalal yake kallo ganin wani shegen wondo wai shi crezi ne ko meye ne oho, duk yana ɓuɓɓule har kana iya ganin farar fatar cinyarsa.
ga saɓulellen wonɗo ga kafurin aski.
fuskarshi ya tsuke tare da jan gajeren tsaki wanda shiyasa Jalal juyawa, ya nufi hanyar fita yana cewa.
“To Ni banifa da manyan kayan nan, yanzu bari inje in duba ko inada jallabiya sai in saka a kai zan biyoku daga baya.”
Da ido suka bishi. Haroon da Jamil kuwa murmushi sukayi.
A haka suka fita suka tafi. Har sunje bakin ƙofar fita ba tare da ya juyoba yace.
“Umaymah ku tashi lokacin salla yayi”. Ya ƙarishe mgnar suna fita
To tace.

Kana suma su Ummi suka nufi ɗakinsu.
Aunty Juwairiyya kuma ta wuce Side ɗinta.

Ita kuwa Shatu da Hibba suka tafi ɗalinta.
Hibba ce ta fara shiga tayi al’wala.
Sannan itama Shatu ta shiga.

Tana fitowa daga bathroom ɗin tayi wani irin….!

Uhummmmmm tuni mun gama shimfiɗan lbrin GARKUWA yanzu dai muna cikene dumu-dumu .

                        By
            *GARKUWAR FULANI*Tsayuwa tare da kasa kunnuwanta.

Tana jin sautin zazzaƙar muryashi.
Yana kudba.
Akan laduban fuskantar watan Ramadan wanda zuwa yanzu kwanaki ne suka rage.

A hankali ta fara taku tana
Nufo inda Hibba ta shimfiɗa musu sallaya.
Ita kuwa Hibba ido ta zuba mata ganin yadda ta kasa kunne.
Cikin murmushin tace.
“Aunty Aysha me kikeji”.
A hankali tace.
“Wannan me sunan malamin da yake huduban nan. Kamar inada wa’zuzzukanshi amman kuma, ban san sunanshi ba, kamar dai kam nasan wannan Muryar”.
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
“Lallai ma kam Aunty Aysha wai muryar Hamma Jabeer ɗin ne ma kike cewa kamar kin santa, kamafa kikace, lallai kam my Aunty”.
Da sauri ta kalli Hibba domin zuwa yanzu ta gane waye suke cewa Hamma Jabeer, Ko Sheykh, ko Jazlaan, ko Muhammad wani lokacin Umaymah na kiranshi haka.
Ta kuma fahimci wai shine mijin da aka aura mata.
Ta kuma gane sun taɓa haɗuwa sau biyu kafin yau.
ganin tayi nisa a tunnine yasa Hibba cewa.
“Aunty Aysha”.
Murmushi ta ɗan yi tare Dasa hannun ta amshi hijabin da Hibba ke miƙo mata.
Cikin ranta take mgnar zuci.
“Uhumm mutun duk rayuwarsa tana cike da ƙalubale da matsaloli Magauta sun sashi a tsakiya kota ina ya juya suna tare dashi.
Amman bauɗewa ta hanashi ganewa, sai anyi mgn yace wai anayi mishi ihu a kai.
ko shi kunnen macijine dashi da yafi kowa jin sauti.
sai iya lillibka ɗika-ɗikan al’kyabbar yanata ɓoye jiki kamar wani mace”.
Mitsss ta ɗanja gajeren tsaki tare daci gaba da zancen zuci.
“Yana nan jiki duk matsaloli ya bari mutun yaga iya inda abunda ke kan yatsunshi ma, ya gagara, shine kullum cikin al’kyabba har ƙasa uwa shine limamin harami.
Sai an kasheshi a banza yasa ƙannenshi da iyayenshi a matsala.
Danni matsalar rashin yayuna har huɗuma ya isheni damuwar duniya bazan ƙarawa kaina damuwar waniba”.
Da sauri ta juyo ta matso kan sallayar sabida jin har masallacin sun sallame sallar, sabida ta daɗe a tsaye tana zancen zuci.

Nan dai sukayi salla, kana Hibba ta miƙa ta fita
Ita kuwa Shatu, sabuwar wayarda aka saya mata jiya da sabon layi aka haɗa mata komai ne, tasa hannunta,
ta jawo.
tare da komawa ta kwanta bisa sallayar.
Layin Bappa tasa kana ta kira.
Jin bata shiga bane yasata gane, sun tafi kenan.
Cikin sanyi ta kira ɗaya layin na wancan ƙasar tasu.
Cikin sa’a kuwa ya shiga sai dai ba’a ɗagawa.

Sau uku ta kira jin ba’a ɗaga ba, ta haƙura.
Number Rafi’a tasaka ta kira.
Tana ɗagawa tace.
“Rafi’a Garkuwa ce”.
Cikin tsananin jin daɗi Rafi’a tace.
“Alhamdulillah Garkuwa ya kike? Ina kike? Ashe kuma abinda ya faru kenan.
Alhamdulillah mun rabu da matsalar Ba’ana, jiya naje Rugar Bani, wai yau su Bappa zasu tafi Lardi”.
Cikin murmushi tace.
“Kai Rafi’a kimin mgna da ɗaɗɗaya mana zanfi ganewa”.
Cikin dariya tace.
“Eh kyace haka mana kinyi bulunbuƙui a masarautar Joɗa”.
Cikin sanyin jiki taja numfashin tare da cewa.
“MASARAUTAR Joɗa ko matsala, komai a bai-bai yake Rafi’a, bana fahimtar komai, tunda nazo cikin wannan masifeffen masarauta kaina a juye yake. Jina nake kamar a rami”.
Cikin rauni tace.
“Rafi’a abubuwan sunmin yawa, da wanne zanji.
Tabbas nayi farin cikin tsira daga tarkon ya Ba’ana, to amman ƙaddara batayi min adalciba data kawoni wannan wurin.
Kin sani Allah ya sani ina son Ya Salmanu”.
Da Sauri Rafi’a ta katseta da cewa.
“Kice Astagafirullaha kada ki mance da auren wani a kanki kike cewa kina son wani”.
Hawayen da suka cika mata ido ta share tare da cewa.
“Bana sonshi! Bana ko son ganinshi, kuma shima hakane baya sona baya son ganina. sauƙina ɗaya da shima ba sona zaiyiba, kowa zaiyi rayuwarshi babu ruwanshi da wani shiyasa hankalina bai tashi sosaima, sai dai ina cikin tarin damuwa Rafi’a, babu Ya Giɗi,Gaini, Seyo, Lado, Inna. Sannan Junainah,Ummey da bappa da nake gani inji sanyinma wai sun tafi Lardi,
ya zanyi inji farin ciki, ga wannan gida mai mutantani daban-daban wasuma naga tsanar shi wancan mai jajayen kunnuwan zasu ɗora a kaina, ko uwar meye haɗina dashi, da magautanshi zasu haɗa dani a ƙiyayyarsa, suji dashi mana, tunda bansan meya shuka musuba, dan shima na lura ba kanwar lasa bane bakine dashi, kan ace ɗirin yake ce musu konɗi, rashin tsoronshi na bani tsoro.”
Murmushi Rafi’a tayi tare da cewa.
“Yanzu dai ya batun karatunki?”.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Zan gayawa Umaymah”.
Cikin shaƙuwarsu Rafi’a tace.
“To sai na shigo, dan mgnar bazata ƙare a wayaba”.
Da sauri tace yaushe zakizo?”.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“In sha Allah dai kafin azumi zan shigo”.
Cikin sauri tace.
“Kafin azumi kuma azuminfa da ɗan saura bama kice gobe ko jibiba, Rafi’a in bakizo minba wa nake dashi da zai zomin?”.
Ta ƙarishe mgnar cikin rauni,
Cikin tausayin Rafi’a tace.
“To gobe ko jibi in sha Allah”.
Cikin jin daɗi tace.
“To sai kinzo.”
Daga nan sukayi sallama.

A ranar da yamma Haroon ya wuce jiharsu Jannart inda nanne masarautar sarkin musulmai take.

A hankali dai kwanakin sukayi ta gungurawa suna cuɗewa Ramadan nata ƙara gaba towa.
Yayinda duk al’ummar Annabi suketa shirye-shiryen tarban watan Ramadan.

Yau dudu saura kwana bakwai ne ake zaton za’a fara azumi, in bai cikaba ma kwana shida.
Tuni Umaymah nata shirin komawa Jihar Tsinako sabida Abban Haroon ya matsa ta dawo sabida shirye-shiryen Ramadan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button