GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

A hankali ta matso gabanshi sunkuyowa ta ɗan yi cike da kunyar wai fitsari nakeji.
Ƙasan jallabiyar ta ɗago kana ya sunkuyo ta cire mishi.
Ta ajiye gefe.
Ƙara matsota yayi dagashi sai fararen tattausan gajeren wondo iya guiwa sai boxes dake can ciki
Sai Senegal fara, daya sata cikin ƙugun gajeren wondon.

A hankali yace.
“Ciremin mana”. Yayi mgnar yana matsota, a hankali tace.
“Ta yaya?”.
Ƙugunshi ya nuna mata.
Tare da cewa.
“Zaro snglet ɗin daga cikin.”

Cikin sanyi ta motso kauda kanta tayi gefe, sabida nauyinshi da kunyarshi da kwarjinshi sun mata yawa.
A hankali ta kai hannunta kan ƙugunshi da nufin ta kamo snglet ɗin ta zaroshi sama.
sai kawai yaji sauƙan hannunta kan Sheykh ɗinsa dake ts….!

Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300 ki sayi katin Mtn ki copy NUMBERS ɗin ki turo min ta number nan da nakeyin whatsApp da ita 09097853276. In Kuma special Group kikeso wanda za’a gama Part two a maƙo biyu, to Kiyi min transfer’n ɗin 1k a susuna na Jaiz bank.
0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai kiyi screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta wannan number din da ta whatsapp 09097853276.
Banda VTU bana so in kinyi babu ruwana.

                            By
               *GARKUWAR FULANI*

Ɗinshi, ta ɗan shafa, wani irin Yar-yar haka tsikar jikinshi ta mimmiƙe a take wani abu yaji yana game jikinshi.
Ita kuwa ba tare da ta fahimci ina ta taɓa ba, ta kuma yi sama da hannun hakan yasa yaji.
Kamar tana mishi wani abune da zai iya tafiya da numfashin sa.

A hankali yace.
“Ha’ahhhhsshh”.
Da sauri ta juyo lokacin kuma hannunta ya isa kan gunshin.
Zaro snglet ɗin tayi ta gaba.
Kana ta tura hannunta ta baya ta jawo, ta fito dashi, tare dasa hannunta biyu ta ɗagoshi tayi sama dashi.
Karo na forko kenan da taga surar jikinshi ziraran miraran tana cikin haiyacinta.
Domin wacca ranar da har ta riƙe baki robar wondonshi bata cikin haiyacinta.

Cikin wani irin yanayi ta zubawa faffaɗan kekyawan ƙirjinshi ido, wanda tattausan gargasa tsilli-tsilli ya yi masa ƙawanya.

cire mishi tayi.
Kana yace.
“To sasu cikin washing machine ki wonkesu.”
To tace kana ta tattarusu ta juya ta nufi inda washing machine ɗin yake.

Shi kuwa sunkuyowa yayi ya cire gajeren wondon ya rage dagashi sai boxes.

Ita kuwa buɗewa tayi ta sakasu ciki.
Da sauri ta juyo jin yana ce mata.
“Amshi wannan ma kisa”.
Da sauri tayi ƙasa da kanta sabida ganinshi haka yayi matuƙar zuwamata a bazata.
Ya razanata.
Rumtse idanunta tayi kirib.

Ajiyeshi yayi a kafaɗanta kana ya juya ya shiga cikin bath ɗin.

Ya fara sakarwa kanshi ruwan ɗumi ya kori duk ƙarnin kana ya fara sa sabulu.

Ita kuwa da sauri ta sasu.
Ciki ta wonkesu a gaggauce.

Ta tsanesu, kana ta shanyasu inda taga ya shanya mata zaninta randa suka dawo, rangadin.
Tana gamawa ta fita.

Shi kuwa kusan awa ɗaya yayi yana murza jikinshi.
Allah yasani baya son ƙazanta ko kaɗan bare ƙarnin jini.

Koda ya fito sha biyu tayi, har ta wuce.
Kimtsawa yayi cikin wasu manyan kayan yadi Getzner mai masifar kyau da tsada lemon green kalanshi, sai aikin da aka yarfawa babbar rigar da zare Royal blue, mai ɗan karen kyau.

Hularshi Royal blue da ratshin lemon green da black blue kaɗan kalanshi mai kyau.
Wasu takalma masu taushi da kyau Black blue, wani turare ya fesa mai ɗan karen daɗin shaƙa.

A hankali ya fito falon sabida ƙarfe ɗaya dai-dai lokacin.
A konce ya sameta bisa 3 str da alamun bata da lfy.
Cikin gajiya yace.
“Yunwa nakeji”.
Jin hakane yasa ta taso a hankali.
Bayanshi tabi.
Kujera yaja ya zauna.
Ita kuwa gefenshi ta tsaya,
gasesshen naman tasa mishi a plate kana ta tasa mishi daddaɗan romon.
Sannan ta ɗan ɗebi haɗin kebeji da nama tasa mishi.
Spoon and fork tasa mishi kana ta ajiye mishi a gabanshi.
Hannunta ya zubawa ido yana kallon jan lallen da tayiwa yatsunta, sai kuma ya ɗan kauda kanshi.
Ita kuwa flaks ɗin tea ta jawo.
A hankali tayi taku zuwa jikin show glass ɗin shi.
Buɗewa tayi cup and tea spoon ta ɗauka.

Zama tayi jin cikinta na kartawa.

Tea ta haɗa mishi kana ta miƙo mishi amsa yayi tare da cewa.
“Jazakallahu khairan”. Tea ɗin ya kurba ba tare da yaci komaiba.

Ita kuwa a hankali ta kifa ƙirjinta kan, table ɗin tare da rumtse idanunta.
Murya can ƙasa tace.
“Amin”.
Ido ya zuba mata, har saida ya shanye rabin kofin.
Sannan ya fara cin naman.
Ido ya lumshe jin ɗanɗanon naman ya ratsa mishi jijiyoyin baki, yawunshi sun tsinke.

Yana kallonta yana ci, har saida ya cinye na plate ɗin data zuba mishi tas, kana ya shanye tea ɗin gyatsa yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah”.
Miƙa wa yayi ya nufi wurin washing hand Baby, wonke hannunshi yayi kana ya kuskure bakinshi.
Zuwa lokacin har an kira sallan azahar ana gab da shiga Masallacin.

Da sauri ya fito. Ba tare da yace mata komaiba.
Ba kowa a falon, sai dai yaji motsin Ummi a kitchen.
Da alamun ta fara suya ma.

Da sauri ya fita, a can masalacin ya samu su Jalal.

Ita kuwa Aysha a hankali ta miƙa ta tattara plete da spoons ɗin da yayi amfani dasu da kofunan, ta fito falon.
Tanata haɗa zufa.

Kitchen ta shiga.
Nan ta samu Ummi da Saratu suna ta aikin suya
Larai kuma tana can tanayi musu nasun.

A hankali tace.
“Ummi kawo in karbeki jekiyi salla kinga har lokacin ya tafi”.

Cikin kula Ummi tace.
“Zaki iya kuwa Aysha nafa lura baki da lfy”.

A hankali tace.
“Zan iya jekiyi salla”.

To tace kana ta fita ta tafi.

Ita kuwa ta amsheta.

Tana idar da salla ta dawo tace.
“Jeki kwanta ki huta”.
Batayi musuba sabida tana jin masifeffen ciwon ciki jikinta har rawa yakeyi.

Wonka ta farayi wai ko zata denajin zufar.

Tana fitowa tasa wata tattausan atampa, riga da siket, kalarta orange mai kyau sai rashin yellow-yellow kaɗan a ciki.
Batayi wata kolliya ba, amman tayi kyau sosai kalar kayan yazo kusan iri ɗaya da kalan fatarta,
ɗinkin ɗan ɗagos.
Ɗaurin ɗankwali mai sauƙin tayi.
Kana ta fesa turare.
Da sauri ta konta jin cikin ya murɗa ko mayafin bata yafaba.

Tana kwanciya kiran Hibba na shiga wayarta.
Da sauri ta ɗauka tare da cewa.
“I miss you Hibba”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Nanda wata ɗaya dai zakuzo auren Ya Haroon sai kin mana wata uku muma yadda nayi muku”.
Dariyar ƙarfin hali tayi tare da cewa.
“Har biyarma zanyi”.

A hankali ta juyo ta kalli Ummi dake bakin ƙofa tana sallama.
“Wa alaikissalam. Ummi shigo mana”.

“A a sauri nakeyi ki fito Sheykh ne yace kije”.

Fuska ta kwaɓe tare da cewa.
“To”.
Hibba ce tace.
“Aunty Aysha bawa Ummi wayar”.
Da sauri tace.
“To Ummi ga Hibba zaku gaisa”.
Murmushi Ummi tayi kana ta juyo tazo ta amshi wayar.
Sannan suka fito tare, da mayafin a hannunta.
Tana worworeshi ne ta nufi falonshi.

A falon ta sameshi, zaune a Dinning area.
Kujera ya nuna mata, a hankali ta zauna.
Shi kuwa tasowa yayi ya dawo kujerar dake kusa da ita.
Foodflaks ɗin ya buɗe, plate ɗin da ya ɗauka a show glass ɗinshi.
Yasa mata Special Arish da haɗin naman da kwai.
Da kuma na Kabejin.
Tura mata gabanta yayi tare da cewa.
“Kici”.
Fuska ta ɗan yamutsa tare da cewa.
“Banajin yunwa”.

Tea ya haɗa mata tare da miƙo mata yace.
“Kici ko”.
Tea ɗin ta amsa sanin ruwan ɗumi ne.

Shi kuwa ido ya zuba mata dole yasa taci.
Bayan ta ɗanci ne yace.
“Meyake miki ciwo”.

Kai ta girgiza alamun babu.
Hularshi ya ɗan tura ya maidashi ƙeyarshi kaɗan tare da cewa.
“Kenan ƙarya Ummi tayi cewa baki da lfy kuma tunda gari ya waye bakici komaiba”.
Da sauri tace.
“A a ba ƙarya bane”.
“Uhumm!”. yace tare da tura mata plate ɗin dole taci, kaɗan kana tace ya isheta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button