GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

“Eh tasha, tana shane ma ta fara aman”.
Ya bashi amsa.

“Yauwa haka akeso Sheykh ba komai yanzu duk kaifin gubar ya karye ta harar dashi yanzu zatayi bacci kuyi mata wonka da ruwan sanyi.
Tana farkawa kuyi mata wonka da ruwan sanyi kuma zata dawo dai-dai da izin Ubangiji”.

Da sauri ya katse kiran bayan yace.
“Ok thanks Dr”.

Ita kuwa Shatu ajiyan zuciya ta sauƙe tare da meda kanta ta jingina da kujera ganin ta bar aman.
Shi kuwa Umaymah ya kalla tare dayi mata bayanin da Dr yayi mishi.
Da sauri ta iso garesu ta amshi ƴar kana ta wuce Bathroom.
Wonka tai mata da ruwan sanyi ɗan kwalinta ta wore ta naɗeta a ciki.
Tuni tayi bacci kafinma ta fito da ita.
A hankali ta zauna bakin gadon Shatu gefen Aunty Amina da Khadijah dake waya da Abboi Appansu kenan tanai mishi bayanin duk abinda ya faru.
Cikin tashin hankali da mamaki Abboi yace.
“Subahanallahi, kai wannan gida nasu akwai sarƙaƙiya.
yanzu ina Parvina?”.
A hankali tace.
“Tana falo can naji kamar harda Lamiɗo ma yazo da kanshi, amman yanzu yarinyar gata nan ta farfaɗo harma tayi bacci”.
Cikin kula da son ahlinshi especially Parvina a hankali yace.
“In sha Allah nida Dedden ku da Al’ameen zumu zo gobe gobe da izinin ubangiji, dama tun tuni ma shiryawa hakan, in Parvina ta shigo kice ta kirani”.
Da sauri tace.
“Toh Appa”.
Guntun murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
“Babanku kika gayawa ne?”.
Cikin alamun karaya da lamarin gidajen sarauta tace.
“Eh Umaymah”.
Kai kawai ta gyaɗa tare da gyarawa jaririyar kwanciya.
Aunty Amina kuwa sunkuyowa tayi tana kallon fuskar Babyn.

A falon Shatu kuwa sosai Lamiɗo ya kwantar mata da hankali kana suka tafi Gimbiya Aminatu na biye dasu a baya.
Bayan ta shiga ta ƙara duba Babyn.

Umaymah kuwa fitowa falon tayi suka zauna a nan.
Ita kuwa Shatu bedroom ta koma ta konta tasa yarta a gaba tofi takeyi mata tana kallon fuskarta Allah ya sani ji takeyi kamar bata tsiraba shiyasa har yanzu hanjin cikinta ke kaɗawa.

A hankali ta jawo wayarta.
Abboi ta kira, bayan sun gama gaisa ya alhinta abinda ya faru ya ɗaura da cewa.
“Dama can gobe zamu zo ko ba komai zanzo inga amryata, inga mummunace ko kekyawa”.
Ya ƙare mgnar da ƴar raha da son kontar mata sa hankali.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Allah ya kawomku lfy Appa na, da Ummey na da Junainah take kamafa”.
Tayi mgnar cikin jin kunya duk da yawan shaƙuwa dake tsakaninsu.
Murmushi yayi tare da kallon Dedde dake jin duk tattaunawar da sukeyi yace.
“Ato kekkyawace sadaki ta garken shanun Bappa zai bata”.
Dariya sukayi baki ɗayansu kana sukayi sallama da juna.
Daga nan kuma Bappa ta kira, wanda tun ɗazu Abboi ya shaida masa abinda ya faru yana ɗagawa yace.
“Shatu na ya jikin Aisha ƙaramar dai?”.
A hankali ta ɗan shafa kan Afreen tare da cewa.
“Alhamdulillah Bappa na ba komai ta samu lfy gatama tana bacci”.
Cikin jin daɗi yace.
“Alhamdulillah ga Ummeynki tun ɗazu hankalinta a tashe yake”.
Amsa Ummey tayi cikin kula tace.
“Boɗɗo na me sukayi miki?”.
Cikin yin ƙasa da murya tace.
“Ummey na so sukayi su kashe miki jikarki tun baki ganta ba, dan Allah da Manzonsa Ummey na kizo gobe”.
Cikin kaɗuwa da begen son ganin Shatu da ƴar tata tace.
“In Sha Allah Gobe za muzo tare da Abboi da izin Ubangiji”.
Cikin jin daɗi tace.
“Alhamdulillah naji daɗi na, Gobe ina cikin gatana”.
Su kuma ta kalli Umaymah da ta shigo yanzu tare da cewa.
“Alhamdulillah Umaymah na Gobe Ummey na zatazo da Bappa na da Deddena da Abboi”.
Cikin wani irin masha’hurin farin cikin alamun son tabbatuwar wani abu Umaymah tace.
“Alhamdulillah Allah ya kawo mana su lfy”.
Amin Amin sukace baki ɗayansu.

Haka dai akayi wunin sunan jiki a mace da abinda ya faru.

Sai can da yamma ne da Afreen ɗin ta farka daga baccin suka ganta lfy lau kafin hankalin kowa ya kwanta.
Nan Umaymah suka fito da kayan suna na gani na burgewa, da aka haɗawa mai jego da Ɗiyarta.

Kayan da Sheykh yayi musu kuwa abin sai dai ace son barka.

Gaba ɗaya wunin yau shima ya kasa fita ko nan da can tunda akayi sallan Jumma’a ya shigo ya wuce Side ɗinsa.
Bini-bini ya kira Shatu ko Umaymah ya tambayi jikin yarinya.

Bayan sun dawo sallan la’asar ne.
Jalal ya biyoshi har cikin falonshi, gefen Haroon ya zauna kana a hankali yace.
“Shima sarkin al’adun sunan harda shi a sahun Magauta sai dai biya shi Hajia Mama tayi da dubu ɗari bakwai daga baya yace min tace in ƴar ta rasu zata cikata mishi dubu ɗari uku ya zama one million”.
Cikin mamaki Haroon yace.
“Ikon Allah ikon gaske, wai ita wannan shegiyar matar meyasa bazamu fito mata a fili bane mu nuna mata mun san komai mu kuma juyo kanta”.
Cikin taune lips Sheykh yace.
“Uhumm bazaku gane bane,”.
Da sauri Umaymah dake shigowa tace.
“Ni na gaji bazamu gane me ɗin ba kuma”.
Cikin wani irin yanayi mai rauni cikin sanyi murya na rawa yace.
“Affan ina ɗagawa Hajia Mama kafane sabida Affan ina jin takaici in na tuno a cikinta Affan ya fito, ku kun san waye Affan kun kuma san asalin zahirin gskyar so da ƙaunar da yake mana, kunsan yadda yake faman faɗa da yaƙin sauya mahaifiyarshi daga mummunan ɗabi’a eh zuwa kekkyawan ɗabi’a.
Ta yaya zanci zarafin ta al’halin Affan ya ɗaukeni matsayin Uba ya ɗaukeni ciki ɗaya muka fito,kada ku manta son da Affan kewa Mameynmu Jalal ka duba tarin son da Affan yakeyi muku kaida Jamil.
Ko a lahira wani kanci al’barkacin wani.
Ina barine sabida ko Affan zai samu nasarar juya halinta”.
Ya ƙarashe mgnar hawaye na zubo mishi.
Gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi tabbas sun san waye Affan ko su Jalal basa so da shaƙuwa dashi kamar Affan.
A hankali yace.
“Duk abinda nasa Affan zaiyi minshi babu musu koda baya son abin duk inda na aikeshi zaije min duk abinda na bashi zaɓi zaɓina yake bi, Affan da kanshi ya fara nuna min baya son inci abincin Hajia Mama wacce take uwace a garesa, yayi hakane sabida zargin tana samin abu a cikin abinci.
Yasha yin kuka yana mgiya in ya tareta tana wani abun me zanyiwa Affan in nuna mishi halaccin ɗan uwantaka banda in rufawa mahaifiyarshi asiri”.
Shiru yayi ganin kiran Affan daya shigo wayarshi.
Jiki a mace itama Umaymah ta zauna.

A hankali ya kara wayar a kunne bayan a amsa kiran.
“Assalamu alaikum Hamma Jabeer”.
Affan ya faɗa cikin tsananin so da ladabi ga ɗan uwan nasa.
“Wa alaikassalam Affan kana lfy”.
Sheykh yayi mgn yana mai jin wasu zafafan hawaye na tsastsafo mishi.
Murmushi Affan yayi cikin yanayin shi na Happy mood yace.
“Alhamdulillah Hamma Dr Akarmakallu Yah Sheykh, mun sauƙo lfy”.
Jingina bayan sa yayi da kujera tare da cewa.
“Alhamdulillah Affan Allah yayi ma al’baka”.
Da sauri yace.
“Amin Hammana”.

Sai kuma yace.
“Jamil ne yazo ya daukomu a airport to yanzu mun biya mun sauƙe Yah Sulaiman da Malam Abubakar.
To gani tare dasu Giɗi ɗin yanzu su ina zamu kaisu, umarni nake jira Hamma?”.
Cikin sanyi yace.
“Alhamdulillah Affan ku dawo dasu masarautar Joɗa ku wuce dasu Part ɗinsu Jalal a sauƙesu a can.
Bawa Jamil wayar”.
Da sauri yace.
“An gama sir yadda kace haka za’ayi ga Jamil ɗin”.
Ya kare mgnar yana miƙawa Jamil wayar.
Saƙale wayar yayi da kafaɗarsa tare da cewa.
“Assalamu alaikum Yah Sheykh”.
Gyaɗa al’kyabbar jikinshi yayi tare da cewa.
“Wa alaikassalam Jamil ka kaisu part ɗinku ɗakinka ka nuna musu Bathroom suyi wonka.
Aunty Rahma zata kawo musu abinci ka tabbatar sunci sun ƙoshi.
Sannan Jalal zai ɗauki Dr Kabir zaizo ya dubasu in sunada matsalar lfy zai kula da komai”.
Cikin gamsuwa Jamil yace to yana kallon kekyawar fuskar Giɗi ta madubin motar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button