GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Cikin kuka Hadi yace.
“Bazan iya guduba Sale su kasheni kawai, ina zanje bayan sunyiwa garin zobe.
Da ƙarfi Hadi ya abka jikin Sale Jin ansa gatari an sari kafaɗarsa ta dama,
Juyowar da zaiyi kuma aka tsira mishi mashi a ƙirji.
Nan take ya cika, hakama Sale.

Cikin gidansu Shatu kuwa.
Ummiy ta sallame sallan kenan, taji.
Inna dasu Innawuro suna kurma ihu da salati.
Yunƙurawa tayi da azama jiki na rawa ta nufo woje.
Fitowanta yayi dai-dai da lokacin da aka sare kan Innawuro, wanda kan yayi tsalle ya faɗo kanta, kana ya gangara ya faɗa gabanta.
Wani irin ihu mai cike da karaji gauraye da salati ta kurma lokacin da taga an burmawa Inna mashi a ciki.
Ihunta da salatinta ya jawo hankalin su, sukayo kanta.
Sai dai kafin su isoma ta yanki jiki ta faɗi babu numfarfashi tamkar matacciya.

Koda suka iso, dariya suka kece da ita cikin rashin imani ɗayansu yasa ƙafa, ya taka ruwan cikinta, tare da cewa.
“Shegun FULANI ku mutu, mu huta, da ganinku a garinmu, gonakinku da dabobbin ku duk sun zama namu.
Mu ɗauke yaranku mata mu maidasu karuwanmu, muyi musu ciki su haihu mu bawa dodo.
Muji daɗi dasu.

Ganin kamar ta mutune yasa suka tattakata suka wuce suka fita daga gidan.

Junainah kuwa da Junaidun, suna gab da shigowa garin suka fara jiyo ihun mutanen garin.
Cikin azaban firgici Junaidu ya wurgar da kondon ƴaƴan itatuwan dake hannunshi,
da gudu yabi bayan Junainah data ruga a guje sabida hango, anata kashe mutane a gabansu.
Cikin kuka da tarin kiɗima da fita haiyacinta take cewa.
“Wayyo Ummiy Wayyo Inna Wayyo Bappa, zasu kashemu.
Wayyoooooooo Adda Shatu zasu kashemu”.
Riƙo hannunta yayi da ƙarfi cikin rawan jiki da murya yace.
“Junainah bazasu kashekiba, zan kareki da izinin ubangiji, zaki rayu, Shatu bazata rasa kowa duniya ba.
Junainah zan zame miki Garkuwa zan fanshi ranki da nawa ran.
Ki zama tamkar yar tsira, Shatu ta zama tamkar yar jarida, ta rubutawa mutanen duniya su karanta, kisan gillan da akeyiwa Fulani mazauna daji.
Da ƙarfi yasa hannu ya zaro wukar dake ƙugunshi wanda da ita ya yayyanki nonunan ayaba dasu inabi.
Wayarshi ya kuma zarowa
Ya Salmanu ya kira,
Salmanu kuma dake, kwance a gadon asibitin nan Genaral Hospital Numan.
Wanda bai workeba tun dukan shaɗi da ba’ana ya mishi.
A hankali yasa hannunshin ya amsa kiran wayarshi ganin Junaidu ke kiranshi.
Cikin kiɗima da firgici Junaidu yace.
“Ya Salmanu, mayaƙan ƙabilar ɓachama sun shigo Rugar mu, sunata kashemu, mazanmu da matanmu.
Ya Salmanu Junainah ina son ta tsira, ko dan ran Junainah ka kira mana hukumar yan sandan cikin Adamawa, ina son su iso su ceci Junainah kada Shatu ta rasa kowa a duniya.
Ban saniba ko zan gazawa bawa Junainah tsaro”.
Gaba ɗaya jikin Salmanu rawa da tsuma yakeyi, katse kiran yayi da sauri ya kira.
“A.S.P Kabiru Nasir. Wanda yake, Hetkotan Adamawa.
Koda ya mishi jawabin abinda ke faruwa, a take. A.S.P ya kira.
S.P Daniyel dake Numan ya bashi doka da oda maza-maza su bawa fulanin Rugar Kikan tsaro gaggawa, shima yana nan tafe da rundunar sa. Ya bashi umarni mai ƙarfi ya ƙara da cewa, muddin yazo ya samu ba dai-dai ba ta ɓanƙaren tsaro, to akan aikinshi.

Wannan abun na umarni daga samane, yasa mugun kafurin nan. Firgita gudun rasa aikinsa, da tonuwar asirinsu da gudun kada a cireshi asa musulmi a kujerarsa, yasa cikin gaggawa ya haɗa kan rundunar sa ya nufi.
Cikin Rugar Kikan.

Junainah kuwa wani irin karkarwa takeyi wanda, tuni fitsari ke tsiyaya yana bin sawunta.
Wani irin ihu tayi, ganin wani kafurin ya kaiwa Junaidun sara a bayanshi.
Wani irin juyi Junaidun yayi ya farma kafurin da da wuƙarsa dan kare kansa da Junainah.
Duk da su biyar suka zagayesu, basuyi nasara a kanshiba, yana kare kanshi da Junainah, har saida suka tsira daga waɗannan.
Sai kuma wasu, mutun takwas suka cimmusu.
Da ƙarfi suka banƙaren Junaidun, suka fara kiciniyar zare Junainah da ya ruggumeta da azaban ƙarfi da yayi.
Wani irin ihu yasa jin an caka mishi.
Wuka a gadon baya.
Still bai saketaba, sai yaƙin kareta da ya farayi, da iya ƙarfinshi.
Ita kuwa Junainah ganin an caka mishi wuƙane yasa ta sume.
Dai-dai lokacin kuma rundunar yan sandan suka iso.

Kamar bazasu guduba, dan sun san da bakin hukumar sukeyin aikin, to sai dai ganin musulman cikin yan sandan suna sakin harbine yasa.
Suka ari ta kare.

Daga nan suka rinƙa gudu sunayiwa yan uwansu fito alamun su gudu.
Cikin ƙanƙanin lokaci duk suka gudu.

Su kuwa yan sandan, suka shiga cikin Rugar Kikan ɗin.
Hankalin musulman cikinsu yayi masifar tashi ganin irin kisan gillar da akayiwa bayin Allah’n nan, kisa na rashin imani.
Nan take suka kira motocin asibiti.
Suka rinƙa jidon masu sauran rai suna sawa a motar ambulance suna kai cikin Genaral Hospital Numan.
Kana suna harhaɗa gawakin kuma a tsakiyar garin.
Cikin mintuna talatin rundunar A.S.P ta iso.
Tare da yan jaridu.

Su Bappa kuwa. Koda suka gama tattaunawa da Maimartaba, sai ya umarci Waziri daya hanasu tafiya a bisa adalcinsa.
Yace su tsaya suci abincin rana, kana suyi sallan azahar kafin su tafi.
To haka yasa suka zauna.
Waziri yasa akayi musu duk ihsanin da Maimartaba ya bada umarnin ayi musu.
Sukaci abinci sukasha, Sannan sukayi sallan azahar.
Daga nan aka sallesu suka tafi.

Tuni cikin gari kuwa gidajen rediyo sun ɗauka, batun faɗan FULANI makiyaya da Ɓachamawa manoma, wanda akaso a juya rahoton da cewa makiyayan ne sukayiwa manomanne ɓarna.

Bayan. Tafiyan su Bappa da kamar 30 minutes ne. Labari abinda ya faru ya riski Maimartaba.
Nan take yasa Waziri da Galadima da hadimai mutun ashirin suka nufi cikin Numan dan suje su tabbar da abinda akace ɗin.

Su Bappa kuwa, sam basuji lbrinba saida suka isa cikin Numan.
Ganin garin a hargitse ne yasa Arɗo Bani ya kalli Bappa da Alhaji Haro da suke gefenshi cikin mmki yace.
“Lafiya kuwa? Meke faruwane a garin nan?”.
Cikin kaɗuwa suka haɗa baki wurin cewa.
“Allahu alamu”.
Drivern nasune, ya kallesu a tsorace yace.
“Anya kuwa yau ba faɗa akeyiba a garin nan ba”.

“Kai ba lfy ba kam!”.
Cewar Alhaji Umaru
Shi kuwa Drivern, bakin titi ya ɗan gangara ya tsaya, ya tambayi wasu yan agaji daketa.
Shiga cikin wani babban Pharmacy da alamun magunguna suke saya,
koda suka mishi bayanin abinda ya faru.
Jiki na rawa yazo ya sanarwa su Arɗo Bani.
Lokaci ɗaya hankalinsu. Yayi masifar tashi.
Nan sukace ya wuce dasu.
Asibitin.

Koda sukaje hanasu shiga akayi.
Hakane yasa, sukace to ya wuce dasu Rugarsu.
Suga ko canma akwai uban da zai hanasu zuwa.

Nan ya nufi cikin Rugar tasu dasu.

Su Wazirima tuni, sun iso.

A can cikin masarautar kuwa,
Sosai hankalin Maimartaba ya tashi.

A can ƙasa mai tsarki kuwa.

Sitti ce tsaye gefen Sheykh lokacin da yake mgna da kakanshi.
Zama tayi gefenshi, tare da tsareshi da ido.
Baibi ta kantaba, ya ci gaba da sarrafa wayarshi.
Wata number, ya dannawa kira kana ya kara wayar a kunne, jim kaɗan aka amsa kiran.
Bayan sun gaisane, ya ɗan gyara zamanshi tare da ɗan kallon Sitti ta gefen ido
Cikin harshen fillanci yace.
“A haɗa min zama da Ƙungiyar TABITAL POOLAKU”.
Sai kuma ya ɗan shaƙi sanyi da ƙamshin ɗauki ido ya lumshe cikin kamala da nitsuwa yaci gaba da cewa.
“A kira min Ƙungiyar MIYETTI ALLAH, da gaggawa, ina da zama dasu.
Ranar Jumma’a in sha Allah”.
Hannun damanshi yasa yana shafa sajenshi, tare da sauraron mgmar da. Arɗon Arɗaɓe keyi.
“Ranar jumma’a kuma? Ka dawone?”.
A takaice yace.
“Zan dawo!”.
Cikin gamsuwa da mgnarshi sanin in yace eh, eh ɗince in kuma yace a a, tofa a ance.
Muddin kuma yace zaiyi abu to da izinin ubangiji sai yayi shi.
Cikin jin daɗi adalci da kulawarshi ga shugabanci da aka bashi yace.
“To Allah ya dawo da kai lfy”.
Yatsun ƙafarshi ya sunkuyar saida suka ɗan bada sautin ƙaras, kana yace.
“Amin ya rabbil izzati”.
Daga nan ya katse kiran.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button