GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Nan take ko ina ya ɗauka.

Suna zaune a falon suna cikin hira.
Sukaji wani irin ƙara mai firgitarwa da bada tsoro.
darararam-dam sautin ƙarar bindigar toka mai ƙarfin amo.
Wani irin tsalle Shatu tayi tare da motsowa jikin Ummi, tare da toshe kunnuwanta, sabida sake jin ƙaran.
Gaba ɗaya jikinta kerma da kerketa yakeyi,
Cikin tsoro take cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun, hasbunallahiwani’imanwakil!”.
Da sauri Ummi ta riƙon hannunta datasa ta toshe kunnuwanta cikin ɗaga sauti take cewa.
“Shatu ba komaifa, kada ki razana bindigar sanarda ganin watane! Shaidar gobe zamu tashi da azumi”.
Cikin tsinkewar zuciya tace zamo daga kan kujerar ta zauna a ƙasa kusa da sawun Ummi, wani irin duka ƙirjinta keyi didib didib, didib.
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
“Aunty Aysha tsoro haka”.
Cikin yamutsa fuska tace.
“Ya kamata ku gayawa duk wani baƙo wannan bahugawar al’adar taku in ba hakaba wata rana tsoro zai kashe irina”.
Sheykh da tun ihunta na forko yana bakin corridor yana kallon yadda take karkarwa,
wani irin murmushin muguntane ya tsubce mishi.
Sai kuma ya tsuke fuskarsa kamar bashi yayi gajeren murmushi ba, cikin faɗa yace.
“Nifa bana son sakarci sam bafa na son anamin ihu a ka da hargowa a gida”.
Cikin tura baki ta bishi da ido.
Shi kuwa fita yayi yana murmushi a cikin zuciyarshi tare da magar zuci.
“Ga rashin ta ido ga tsoro, ga tsiwa da fitsara ga makirin karaya.
Ai da anyi ta sakin sautin bindigar har sai tayi fitsari a zani”.
Da haka ya wuce ya nufi fada,
nan suka fara tattauna yadda lamuran zasu tafi.

Ummi kuwa murmushi tayi ganin irin kallon harara da Shatu ta raka Sheykh dashi.
Cikin murmushi tace.
“Taso ki zauna muyi mgna”.
A hankali ta miƙa ta hau bisa kujerar da Ummi take ta zauna, Hibba kuwa, tuni ta nufi Side ɗin Aunty Juwairiyya.

Gyara zama Ummi tayi tana fuskantar ta da kyau,
Cikin nitsuwa tace.
“To Alhamdulillah kinga anga wata gobe zamu tashi da azumi in Allah ya kaimu, akwai ƙarin aiyuka a Side ɗin nan wanda ko da can baya ko Sheykh bayanan yana ajiye komai na buƙatar rayuwa akanyi girki a nan kamar akwai mace, sabida anan su Jalal, Jamil, Hashim Sulaiman Imran Affan in yana nan suke shan ruwa.”
To yanzu bana Sheykh ba inda zaije sabida a jerin jadawalin malaman tabsir da ake turawa jihohi bana ba’a turashi ko inaba tunda ya girma ya fara tabsir sau ɗaya yayi azumi a nan shekarar da ciwon Jafar ya tsananta, to anane naga zahirin yadda yake gudanar da al’amuran rayuwarshi cikin Ramadan.
To bana ma. Anan cikin Ɓadamaya zaiyi tabsir ɗin shi.
To aiyukan mu sunada yawa.
Dole kisan yadda tsarin komai ke tafiya.”
Cikin sauƙe numfashin ta gyara zama ta fuskanci Ummi da kyau kana a hankali tace.
“To”.
Itama gyara zama tayi da kyau kana tace.
“Azumi goma sha biyar zaiyi a nan, ƙarishen 15 ɗin a ƙasa mai tsarki zaiyi su.
Ma’ana zai tafi Umrah.
Sannan yanada masallatai uku da yake tabsir a kullum.
Da safe misalin karfe sha ɗaya na safe zai tafi masallacin jumma’a na cikin kasuwa, a can zaiyi tabsir sai ƙarfe shabiyu saura mintuna goma zai taso.
Daga nan kafin ya iso masarautar Joɗa tafiyar mintuna goma ne.
sha biyu dai-dai, zai zauna tabsir masallacin Masarautar Joɗa.
Sai ƙarfe ɗaya na rana zai tashi.
Daga nan bazai dawo gidaba, sai anyi sallan azahar.

To ana idar da salla zai shigo, gida al’adar rayuwarsace tun yana yaro.
Zaiyi baccin awa ɗaya tsakanin azahar da la’asar.
Ƙarfe uku dai-dai na yamma zai tashi zaiyi wonka, ya canza shiga, kafin ya gama an kira salla.
Yana fitowa zai wuce masallacin Masarautar Joɗa, inda yake limanci ana idar da salla zai tafi masallacin jumma’ar dake jami’ar Joɗa. Inda zaiyi tabsir daga ƙarfe huɗu zuwa biyar na yamma zai taso.

Akan hanyar shi ta dawowa yana tsayuwa wurin mashigar laleko zai sayo kayan buɗa baki ƴaƴan itatuwa.
Yana dawowa zai ajiyesu.
Ya wuce Side ɗinsa, wonka zaiyi kana yasa sauƙaƙƙun kaya, ya dawo falonshi ko ya wuce cikin Garden acan zaiyi ta karatun al’ƙur’ani ko kuma wani lokacin ya ɗan konta ya huta.

Kafin lokacin shan ruwa, Ni kuma da hadimar da Gimbiya Aminatu ke bani duk Ramadan ta tayani aiki.
Tuni mun gama aikin buɗa baki. An shirya komai a dinning table, nasu Jalal kenan.
Suma kuma gab da magriba zasu zo.
Shi ma zai fito yakan zauna tsakiyar Jalal da Jamil ko kuma tsakiyar Jalal da Jafar.

Baya cin abu mai nauyi iya karshi dabino da inabi da tuppa, sai ruwan zam-zam wanda dashi yakeyin buɗa baki.
Daga nan zai wuce masallacin Masarautar Joɗa wani lokacin zai fita dasu wani lokacin zai rigasu fita.

Ana shirya mishi abincinsa na musamman a ajiye mishi a dinning table ɗin dake can falonshi a Foodflaks ɗin shi na musamman, wani lokacin Gimbiya Aminatu ke aiko mishi.

In ya fita bazai dawoba sai anyi sallan isha’i Dana asham.
Amman su Jalal su zasu dawo suci abinci kafin isha’i sai su koma masallacin.

Idan ya tashi daga Masallacin kai tsaye zai wuce.
Gidan radiyo ABC Ɓadamaya, inda yake gabatar da shirin.
“Fatawa. Za’a ayi mishi tambaya kan Ramadan dama sauran abinda ya shafi addini yana amsawa, wasu kan tura tambayoyin wasu kuma kira sukeyi a da number da ga suke badawa, suyi tambaya ya bada amsa.
Ƙarfe takwas da rabi ake fara shirin tara dai-dai ake gamawa.
Tara da mintuna ashirin yake isowa gida”.
Ɗan tsagaitawa tayi ta kalli Shatu dake cewa.
“Tab agogo sarkin aiki to shi baya gajiya ne, ga azumi ga zirga-zirga ga kuma duk inda yaje dole ba shiru zaiba mgna zaiyi ai ƙishi zai mishi illa”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“To ai in yaje gidan radiyo tarba ta musamman akeyi mishi, sai dai shi ba ko ina yake cin abinci ba tunma yana yaro.
Ko a gida nan ba abincin kowa yake ciba.
To shiyasa tara da rabin nan zai dawo a gajiye cikin yunwa,
to nan zaici abinci sosai.
Kana yayi wonka zuwa sha ɗaya dai yayi bacci.

To ƙarfe biyu kuma zai tashi, wani lokacin ma biyu bayayi zai tashi yayi ta nafilfilinshi da karatun Alqur’ani.

Daga nan kuma baya komawa bacci.
Har ayi sahur ayi sallan asuba.
In ya dawo yayi Azkar, to nanne yake samun yayi bacci mai tsawo dan tun bakwai da rabi ko takwas na safen zaiyi bacci sai goma zai tashi ya fara shirin tafiya masallacin jumma’a na kasuwa.”
Kallonta ta ɗan yi tare da cewa.
“Kin gane lokutan da yake aiki Dana hutuwa dana bacci ko dana cin abinci ko?”.
Cikin murmushi tace na gane.
“Da safe zai sha bacci son ranshi, daga takwas zuwa goma kafin ya tashi ya shirya.
Yaje masalacin jumma’a na kasuwa sha ɗaya tayi yayi tabsir ɗin awa ɗaya, daga nan ya dawo masallacin Masarautar Joɗa,
shabiyu ya fara tabsir sai ƙarfe ɗaya ya gama, ayi salla ya dawo.
Ya sake shan baccin awa ɗaya.
Kafin kuma ayi la’asar ya tafi masallacin Joɗa state University. Yaje yayi tabsir in ya dawo, kuma ya lokacin hutawane har magriba.
Daga nan kuma ayi buɗa baki a wuce masallacin daga can a wuce ABC.
Sai tara a dawo.
To yaseen wataran yunwa zata kadashi a hanya, ƙattin rigunan nan da yake sawa sune zasu jashi su kaishi ƙasa.
To ma wai Ummi to yaushe yake zuwa aiki kuma?”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“To in baya garin an turashi wani state ɗin yana zuwa aikin ne?”.
Kai ta girgiza alamun a a.
Cikin murmushin Ummi tace.
“Shiyasa ko yana nan in dai a Ramadan ne baida lokacin zuwa Valli Hospital, bare Genaral Hospital ko kuma Asibitin jami’ar Ɓadamaya.
Shine dalilinshi na ƙin yin aiki a asibitin gwamnati sai ƙarshen sati-sati yake zuwa sau ɗaya, duk wanda zai duba kyautane aiki”.
Naɗa hannunta tayi tare da cewa.
“Batun yunwa ta kadashi kuma, yanzu aikin kine, kula da abinda zaici”.
Taɓe baki tayi tare da cewa.
“To shi wannan da tsarabe-tsaraben falsafa nasan irin abinda zai cine ma.
Mutun fuska a haɗe kullum kamar mai damuwar rashin jigo”.
Miƙewa Ummi tayi tare da cewa.
“To kika sani ko hakanne.
Kuma ai gani duk abinda kike son sani a kanshi tambayeni.
Abincin da yafiso kuma yafi son ganyayyaki, fruits and vegetables sai kuma kayan ruwa, kana yana son nama da kifi in an mishi irin sarrafawar da yakeso.
Sannan yana son abincin gargajiya wasu lokutan musamman a wurin yin sahur.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button