GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Juyowa yayi ya ɗan kalleta tare da cewa.
“Sai kici kada ki cinyeni ɗanye”. Ya ƙarashe mgnar yana kallon gefen fuskarta
Gyara zamanta tayi kana ta buɗe ladar ta fara cin abinda ya mata.
Shi kuma yaci gaba da wayar da yakeyi da Umaymah.

Haka dai wunin ranarma suka wuni, sunje rugagen Arɗon Arɗaɓen uku a ranar.
Yayinda Duniya ke ganin ziyar GARKUWAN FULANI, zuwa ga dajukan da fulanin ke rayuwa, ta sanadin ɗaukar Laminu da Jamil.

Suna turawa ma aikatarsu a jaridu da kuma tv da gidajen rediyo.

Yau kwanansu hudu yau wunin na biyar kenan.

Tunda sanyin safiyar suka tashi daga masauƙinsu na Barata state.
Wanda yanzu sun zagoyo.
Sun dawo kusa da gida daga Barata zuwa jihar Ɓadamaya ba wani State ɗin.
Sai dai tafiyar mai nisace sosai hakane yasa.
suka tashi da wuri dan gefe zasu kuma nufa kafin su dawo hanyarsu.
Ƙarfe takwas dai-dai suka isa Rugar Arɗon Arɗaɓen na Rugar Bugem .
Dai-dai lokacin kuma makiyayan wurin keta sake dabobbi su dan tafiya kiwo.

Cike da mamaki gaba ɗaya su Sheykh suke kallon dabobbin mutanen wannan yanki da suke masu jajayen shanu babu shanu ko ɗaya da zaka gani mai farar fata.
Duk jajaye ne gaba ɗaya iya ganinka.

Koda suka isa, bayan sun gaisa Sheykh ya musu bayani kamar yadda suka san da zuwansu.
Buɗan bakin Arɗon Arɗaɓen sai cewa yayi.
“To in bamu ciyar da dabbobinmu da ciyawar manoba to da mi zamu cidasu?.
Ai dole mu shiga muyi kiwo du inda mukaga dama, dan aradun Allah da dabbobinmu su kwana da yunwa gwara mu bamuci ba”.
Ya ƙareshe mgnar da gurɓata ciyar hausarshi.
“Cikin fushi Sheykh yace.
“To ku gwada ku gani”.
Cikin tijara ta wasu daga cikin ƙabilun fulanin daji Arɗo yace.
“Ba mu gwada ba zakaceba GARKUWA. ai munayi, mu ƙara dai mu gani zakashe!
Kuma babu abinda zamu gani, mu ko ina garinmu ne”.

Jamil ne yayi dariya tare da ɗaukar duk wani motsinsu yana turawa kai, tsaye.

Jalal kuwa tuni ya kira het kotan Sojoji na jihar ya sanar musu.
Dasu zo su binciki mutanen.
Domin gaba ɗaya kowa ka gani da wuka ko arda a jikinsu.
Sun tara wani shegen gashin da babu gyara.

Daga nan suka miƙe suka nufi inda motocinsu suke.

Ƙarfe biyar suka fito cikin dajin suka dawo cikin birnin Barata.
Nan sukayi salla.
Kana sukaci abinci kafin suka kama hanyar jihar Ɓadamaya.
Wanda zasuyi isan dare duk gudun da zasuyi.

Suna shiga Mota sukaci gaba da tafiya.

Ta gefen idonshi ya kalli Aysha,
da tayi shiru tana kallon gefen titi tana murmushi.
Hankalinshi ya ɗan maida kan System ɗinshi dake kan cinyarsa.
“Murmushin me kikeyi?”.
Yayi mgnar tamkar ba shi yayi mgnar ba.
Juyowa tayi ta ɗan kalleshi tare da cewa.
“Ba murmushi nakeyi ba!”.
Cike da mamaki ya juyo ya ɗan kalleta a fizge kana yace.
“Kuka kikeyi kenan?”.

Kanta ta ɗan sunkuyar cikin tura baki tace.
“A a kam”.

Ajiyan zuciya mai tsawo ya sauƙe tare da lumshe idonsa.
Kana ya koma ya jingina bayanshi da kujerar yana lissafi yau sallan layya saura kwana takwas.

Ita kuwa Aysha shiru tayi tana nazarin.
Toshi wannan wanne irin mutum ne?
Taya zata iya fahimtar harshensa?
Yanada iya sarrafa harshe duk dagiyarka sai ya kureka.
Ba’a gane ina alƙibilarsa ta dosa.
Cikin sanyi ta juyo ta kalleshi.
Jin ya matso kusa da ita sosai.
Kanshi ya ɗan juyo ya kalleta.
Sannan ya kalli madubin motar Ado bazai ganshiba kuma bazai jisuba.
Cikin fidda sassanyan numfashi yasa hannunshi ya kamo hannun ta.
Zamewa yayi susai bisa kujerar ya zama tsawonsa dai-dai dana juna sajenshi ya manna a fuskarta.
A hankali ya ɗan goga mata sajen.
Tare dasa hannun shi. Ya ɗan tallabo haɓarta ya ɗan juyo fuskarta kusa da tashi fuskarshin.
Al’amarin Yah Sheykh na dabanne komai nashi na dabanne.
Shiyasa gaba ɗaya ta gaza yin komai sai zuciyarta dake harbawa.

Shi kuwa Yah Sheykh hannunshi na kusa da ita yasa ya zagayo ƙugunta.
Kana hannunshi ɗayan kuma.
Ya kamo ɗaya hannun ta. Ya matse a kafaɗarshi.

Ita kam Aysha shiru tayi, tana ji da ganin ikon Allah.
jikinta kuma karkarwa yakeyi a hankali amman can cikin naman jikinta takejin rawan.
Tattausan lips ɗinshi ya manna da kunnenta, a hankali murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Aish!”.
Cikin sanyi taji sautin muryarsa.
Idonta ta juya tana.
maimaita sunan a bakinta.
“Aish!”. Taji ya kuma kiranta, a hankali tace.
“Na’am”.
Hannunta ya murza a wuyanshi tare da cewa.
“In tambayeki wani abu mana?”.
Kanta ta gyaɗa a hankali al’amar eh.
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
“Naga fulanin nan duk ko wani yanki da sashin da mukaje yanayinsu zai banbanta dana saura.
Wasuma basa fulataci.
Wasu kuma hausa sukeyi wasuma wani yare sukeyi.
Kuma duk fulanine?”.

Cikin sanyi tace.
“A a ba duka fulani bane, akwai ƙabilu mabanbanta a cikin daji da dabobbin a gabansu.
Yayinda in mutane gama gari suka gansu sukeyi musu kuɗin gorowa wato sai ace duk fulanin ne”.

Lips ɗinshi ya ɗan goga a kunnenta.
Yana shaƙar daddaɗan ƙamshin jikinta.
ita kuwa da sauri ta ɗan maƙe kafaɗarta jin yadda ya goga mata tattausan laɓɓansa.
kana ya hura mata isa a kunnenta.
A hankali yace.
“To menene babbancin gayamin inji”.

Haka nan taji kasala tarufeta.
Shi kuwa cire tafin hannunta yayi a wuyanshi ya manneshi da nashi tafin hannun.
Kana ya sauƙeshi kan System ɗinshi.

A hankali yace.
“Ina jinki gaya min a hankali, kada kimin ihu a kunne kinji ko Aish kiyi hankali”.

Numfashin ta fesar a hankali kana tace.

“Ka tuna Rugar forko da mukaje?”.
Dan matse hannunta yayi tare da cewa.
“Muhammad Jabeer baya mantuwa, gaya min kawai, kaina ba irin naki bane, da wasu ke birki tashi”.
Ɗan hararanshi tayi tare da tura bakinta kaɗan.
“Karon forko a iya tsawon watannin da ta zauna dashi da taga yayi murmushi, kuma murmushi yayi masifar mishi kyau.
Cikin murmushin yace.
“To ni dai gaya min ba tsiwa nace kimin ba”.
Ya ƙarashe mgnar yana haɗe fuskarshi da gefen fuskarta.
A hankali tace.
“To a cikin fulanin ko ince makiyayan dake cikin daji da kiwon dabobbi akwaisu daban-daban.
Akwai.
1 JAFUNAWA, 2 UDAWA, AKWAI 3 KASINAWA, AKWAI KUMA 4 KASINALLE, AKWAI 5 SULLUƁAWA, AKWAI 6 DAƊA WOGGA, AKWAI 7 YAN JAJAYE, AKWAI 8 JOTTAN MA’EN AKWAI 9 TEMA’EN akwai Kuma 10 ƳAN BOKOLOJI.”
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
“To menene babbancinsu.”
Kanta ta ɗan ɗago ta kalleshi, tattausan gemunshi na gogan goshinta.
Shi kuwa idonshi ya ɗan rage tare da cewa.
“Na’am Yah Aish”.
A hankali taci gaba da cewa.
“JAFUNAWA, sune masu sa manyan kaya jomfofinsu masu faɗi da zurfi.
Asalin fulanine basa son fitina ko kaɗan, sune wanda muka fara zuwa wurinsu.

Akwai Katsinalle su kuma sune masuyin kitso mazansu da matansu Hausawa ne makiyaya ashar a bakinsu kamar ruwa.
Basu da kunya sai dai sunada tsoro, yanzu zasu fetsare ido zuwa mutun rashin kunya barazana kaɗan zaka musu su tsorita.

Kana sai SULLUƁAWA sune, masu yin kitso da man shanu.
In Suka wuceka zakaji suna ƙarni kaga maiƙon man shanu na bin wuyansu, basu fiye yin fillanci ba sai hausa.

Sai kuma UDAWA sune masu tasowa daga wata ƙasar su zo nan sunfi zama ƙasar Chadi.
Sam ma ba funin ƙasarnan bane, kuma bama Fulani bane, su kashe mutun bai zame musu abin tsoroba, mugayen.

Sai kuma BOƊEJIN masu Ƴan JAJAYEN shunu.
Suma zuwa sukeyi mafi akasari daga kasashen Arewa suke zuwa.
Shanayensu duk jajayene, babu wata ƙabila cikin masu bin daji da suka kaisu jaraba da son mata.
Mazansu basa gajiya da mata.
Matansu basa gajiya da maza.
Suna iya tare mace a daji suyi mata fyaɗe su wuce ta ba damuwarsu bane mafi akasari daga Senegal, Chadi, suke tahowa duk sanda suka san damuna ta ɗauke anyi amfanin gona ba’a gama tattateshi ba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button