GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Kitchen ta wuce. Ummi na biye da ita a baya.

Juyo naman tayi a roba, ta wonkeshi Sannan tasa wuƙa ta fara yankashi dogo-dogon yanka sala-sala.
Kara lallaɓesu tayi, kana ta tasashi a wata robar, al’basa ta yanka mai yawa, dai-dai yadda zaji mata, citta kanamfari Curry da maggi da ɗan gishiri ɗan mitsilili ta tarfa a ciki.
Ta gaggaureyasu.
Kana ta juye a tukunya sannan ta ɗauka a kan gas, tasa wutan dai-dai misali.

Ummi kuwa al’basan taketa gyarawa tana yankawa a wata roba. Attaru da basufa takwas ba ta, gyara kana ta jajjaga matasu.

Tuni naman kuwa yana tsilala yanata ƙamshi ya tsastsafo ruwan jikinshi, ya haɗe da kayan ɗan-ɗano dana ƙamshi.

Jajjageggen Attaruhu da al’basan da Ummi ta miƙa mata, ta amsa. Kana ta buɗe tukunyar, ta juyeshi ciki ta ɗan motsa naman.
Haɗin duk ya shiga ciki.
maggi da Curry ta ɗan ƙara.
Sannan ta rufe tukunyar nan take tafa bararraka bul-bul sai wani irin ƙamshi yake fesorwa.

Jamil da ya shigo da bayi uku ko wanne da roban kayan ciki a ciki an wonkesu fes, hanji an kitsesu gwanin kyau.
Shima ajiye robar hannunshi yayi tare da cewa.
“Wannan ƙamshi shine ƙungiyar yunwa.”

“Allah ko Jamil”. Ummi ta faɗa tana kallonshi.
Shi kuwa, kanshi ya jinjina tare da cewa.
“Sosai ma Ummi, gashi wannan nakune Sheyky Aunty Ayshan, Mamey ke, Jalal ya kwautar da nashi wa abokinshi”.

“To yayi kyau, bari mu fara aikin.”
Cewar Ummi juyawa yayi ya fita yana cewa.
“Afa ajemin wannan gashi na Sheykh da yake ta zuba ƙamshi”.

“Kaɗan ba”. Cewar Aysha dariya yayi tare da cewa.
“Kai Aunty Aysha rowa ba kyau fa”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Yoh naji Affan yace Hammanku zai dawo a yunwace”.

Dariya yayi ya fita.

Ummi kuwa tukwane ta ɗauka kana ta kalli Saratu da yanzu ta shigo tace.
“Yanka min al’basan da yawa.
Ke kuma Larai zoki riƙe min mu yayyanka tunda a gyare suke”.
To sukace kana duk suka fara aiyukan da tasasu.

Aysha kuwa buɗe tukunyar tayi ganin. Yadda yayi kauri romon yayi yadda takeso. Yanata ƙamshi sai ta ɗauko wani kekkeyan ɗan Foodflaks karamin.
Ludeyi tasa ta rinƙa korfe romon tana sashi a kular da zafin shi.
Saida ta korfeshi kab.

Kana ta rufe kular sannan.
Ta matso kusa da tukunyar ta fara, motsa naman wuta yanaci daki-daki tana motsashi tana gaurayashi.
Yana ɗan kame jikinshi yana ɗan zama kamar gashi wuta.
saida taga ya tsane yadda takeso.
Ta kwasheshi da zafinshi tasashi a kula kana tasa wani a ɗan madaidaicin kula mai ɗan karen kyau.
Rufeshi tayi sannan ta raba romon biyu, a ƙananan kulan.

A tray’n ta jera Foodflaks masu ɗan karen kyau ɗin kana tasa plate spoon and fork, sannan ta ajiyesu gefe.
Kana ta ajiye mai yawan shima gefe.

Inda Ummi take ta matso kana ta fara taya wonkewa tana tsaneshi tana zubawa a tukunya.
Tare da turbuɗeshi da al’basan da citta kanamfari Curry da maggi tafarnuwa da a dai sauran kayan ƙamshi dana ɗanɗano, saida suka gama komai cikin ƙanƙanin lokaci kana.
Su Sara suka kullace wuri.
Sannan Ummi tace to suma suje suyi nasu aikin.
Ta basu duk wani kayan haɗin da zasu buƙata duk da tasan ana kaimusu.

Falon suka dawo suka zauna.
Bayan Ummi ta zubo musu hanta gashin tukunyar ta yarfa musu romon a samanshi.

Plate ta miƙa Aysha.
Da sauri ta jujjuya mata kai tare da cewa.
“Bana cin kayan ciki”.
Cikin mamaki tace.
“Allah sarki Aysha am na manta, da ban haɗaki da aikinshiba”.
Shiru tayi ganin ta rumtse idanunta tare dasa hannunta ta kama mararta.
“Sannu baki da lfy ko?”.
Ummi ta tabayeta cikin kulawa.
Kai ta jinjina tare da cewa.
“A a ba komai ai da sauƙin”.

Jalal, Jamil, Affan, Imran, Sulaiman, Y Jafar ne suka shigo a jere.
Kai tsaye Dinning area suka wuce.
Da sauri Ummi tabi bayansu tana cewa.
“Sannunku an gama yankan ne?”.
Baki Jalal ya tsuke tare da cewa.
“Inafa aka gama gajiya kawai mukayi muka gudo .
ALLAH ko Hamma Jabeer har tausayi ya bani mutun kusan awa biyu a sunkuye, ba hutu, fuskarshi kayanshi duk sun cika da jini”.

Jamil ne yace.
“Ummi da Allah zubo mana abin ci”.

To tace tare da shiga kitchen ɗin gaseshen naman ta ɗauko musu.
Ta zuzzuba musu kana Special Arish ta saka musu da haɗin naman da kabejin da Aysha tayi musu.
Sannan ta ɗauko Drinks ta jera musu, nan suka faraci.

A hankali Aysha tace.
“Shine kuka gudo kuka barshi shi ɗaya a can ko?”.
Murmushi Affan yayi tare da cewa.
“No Madam Jabeer ba gudowa mukayi ba shi yace mu dawo da Ya Jafar”.

Sulaiman ne yayi dariya tare da cewa.
“Yo gskyanta taga an bar mata miji shi ɗaya duk mun gudo”.

Dariya sukayi duka.

Sha ɗaya da rabi. Dai-dai ya shigo, cikin tarin gajiya.

Da sallama a bakinshi, da sauri ta buɗe idonta dake rumtse dan ciwon da cikinta keyi.

Su Jalal kuwa daketa hira suna cin abinci da korawa da Drinks mai sanyi ne suka juyo suka kalleshi tare da cewa.
“Sannu Hamma Jabeer sai yanzu kanshi ya ɗan jinjina kana ya wuce.
Cikin kula Ummi ke ce mishi sannu.
” Sheykh sannu da aiki Allah ya maimaita mana”.

“Amin Amin”. yace kana ya wuce.
Ita kuwa da ido ta rakashi.
Ɗan juyowa yayi ya kalli bayanshi ko ta biyoshi
Ɗan gajeren tsaki yaja tare da kallon duk jikinshi jini ya tsastsalu ga riƙewa da bayanshi yayi sabida dogon sunkuyo.

A falon kuwa cikin kula Ummi tace.
“Sannu ko Aysha dauki tray’n ki tafin masa dashi”.
To tace kana ta miƙe a hankali ta nufi cikin kitchen tana jin mararta na kartawa.

Shi kuwa Ɗan juyowa yayi tare da ɗan buɗe muryarshi a gajiye yace.
“Aish! Aish!!”.
Juyowa su Affan duk sukayi suna kallon hanyar falonshi, salon yadda ya kira sunan a kan harshenshi da yadda ya fitar da ƙal-ƙalan yasa amon sunan ya fito da daɗin sauraro da armashi na musamman”.

Murmushi Sukayi baki ɗayansu,
wannan salo na manya ne.

Ummi kuwa murmushi tayi tana sunkuyar da kanta.
Affan da Jamil kuwa kallon juna sukayi tare da yin Murmushi.

Ita kuwa Aysha a hankali ta fito da tray’n a hannunta ta nufi falon nashi.
Tanasa ƙafarta kan steps ɗin da zai sadata da corridor’n taji muryarshi ta ratsa mata kunne a karo na ukku yace.
“Ahh’ishhhhh”.
Cikin sauri ta haura tare da cewa.
“Na’am Yah Sheykh”.

Kai Affan ya jinjina tare yin dariya yace.
“Zuwa gidannan yanzu ɗaukan darasi ne kan sarrafa salon so mai zurfi da inƙanci irin na masana ilimin addini, nasu ba irin namu bane na turawa”.

Dariya yayi ganin Ummi ta mishi daƙuwa.

Shi kuwa Sheykh a hankali ya kwaɓe fuskarshi.
Tana shiga ya bita da ido sosai shigar da tayi. Yayi masifar amsarta.

Kan dinning table taje ta ajiye tray’n kana ta juyo.
Gabanshi ta zo tare da cewa.
“Gani”.
Zo yace a taƙaice ya nufi bedroom tana biye dashi a baya.

Kai tsaye ƙofar Bathroom ya tura ya shiga.
Juyowa ya ɗanyi ganin ta tsaya tare da ce mata.
“Dan Allah kizo nan”.

A hankali tabiyoshi.

Tana shiga ya maida ƙofar ya rufe.

Sai kuma yazo ya tsaya gabanta,
tare da cewa.
“Cire min al’kyabbar”.
Cike da mamaki ta kalleshi ganin ya tsuke mata fuska ya kuma buɗe hannayeshi ne yasa ta ɗan matso.
A hankali tasa hannunta ta buɗe al’kyabbar.
Juya mata baya yayi.
Ta zare rigar.
Sake juyowa yayi ya fuskanceta sunkuyowa ya ɗanyi tare da cewa.
“Cire min jallabiyar”.
Kauda kanta tayi tare dasa hannun ta kan wuyanshi inda masaƙalin jallabiyar suke.
Boturan ta ɓalle kana ta janye hannunta.
Tsaki ya kuma ja tare da kwaɓe fuskarsa da cewa.
“Kiyi sauri ki cire minsu ƙarni nakeji zasu sani amai kuma fitsari nakeji.
Bana son hannuna ya sake taɓa jinin.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button