GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Nan suka tafi.
Washe gari aka tashi da azumi na talatin.
Allah cikin ikonshi aka kaishi lfy.
Watan Shawwal ya baiyana Ramadan ya tafi kuma sai mai nisan kwana.

Shatu kuwa a wunin ranar Yar aikin Aunty Juwairiyya Sato, ta zana mata jan lalle mai ɗan karen kyau.

Koda ta dawo kuma jarakuna madarar shanu data gayawa Gimbiya Aminatu tanaso
Aka kawo mata ta tafasashi kana tasashi a manyan kware da ƙananan kwore da kyawawan robobi tasa tsami kaɗan a ko wanne kwarya da roba.
Ta rufesh ta jerasu a Fridge a ƙalla sunfi kore goma madaidaitan ƙananan sun kai kore takwas sai robobin su kuma sun kai goma suma.

Bayan sallan magriba ansha ruwa anyi nak.
Hibba sai tsalle da farin ciki da kiraye-kirayen ƙawaye da yan uwa da abokai sai tsiya Jamil ke mata.

Bayan sun gama shirya komai na aikin da zasuyi gobene.
Suna zaune a falo Ummi ta kalli Jamil tare da cewa.
“Jamil wai sai yaushe zaka share Side ɗin Sheykh ne, munyi waya da Umaymah ɗazu tace min gobe fa zasu dawo.
Anayi sallan idi a can zasu taso”.
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
“To naga mutun ga matarsa ace Ni in mishi shara”.
Ko inda suke Shatu bata kalla ba.
Ummi kuwa jingina tayi da jikin kujera tace.
“Ai bazata san ƙaidar yadda yakeson a gyara mishi ɗakinshi ba.
Dole sai ka nuna mata.”
Cikin gamsuwa da hakan yace.
“To ba matsala sai gobe da sasafe mu hau kan aikin abinda ɗakin ba wani ƙura da tarukucene da shiba”.
Eh hakane Ummi tace tare da kallon Shatu tace.
“Gobe in Allah ya kaimu Shatu ku gyara mishi ɗakin nashi”.
“To Allah ya kaimu. tace ba tare da ta kalli inda sukeba.

A can ƙasa mai tsarki kuwa.
Ana idar da sallan isha’i da yawa suka fara ɗawafi.
A cikinsu kuwa harda Sheykh Jabeer da mai sunanshi kana da Haroon
A nitse bisa tsari suke ɗawafin sunje ƙafa biyu ana uku sun isa dai-dai. Maƙama Ibrahim.
Sheykh Jabeer ya juyo kanshi ya kalli gefen damanshi da sauri cikin tarin mamaki al’ajabin Fuskar mutumin da ya ga ya wulgawa a idonshi…!

Littafin GARKUWA na kuɗine idan kina buƙatar saya ga number 09097853276 katin mtn na ɗari uku. Normal group in kuma special Group kikeso 1k zakiyi min TRANSFER ta ac ɗina 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.

                    By
          *GARKUWAR FULANI*

????????????????????????????????????????????

             *GARKUWA*
                            NA

        *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     ????????????????️????????????????????????

ASSALAMU ALAIKUM. MASOYA NA MAKARANTA LITTAFIN GARKUWA, WAƊANDA SUKA BIYA DA WAƊANDA KE KARANTA NA SATA, INA MUKU FATA ALKYAIRI da fatan muna lfy, kana kuma ina mai bawa dubban mutanen da sukayi min mgn ta kafafan sadarwa kamarsu, WHATSAPP, FACEBOOK, INSTAGRAM, WATTPAD, BAKANƊAMIYA, WASUMA A TIKTOK daga jiya da yamma zuwa safiyar yau haƙurin rashin basu amsar tambaya ɗaya dai da aketa memeta min. GARKUWA WAI KIN SAIDAWA ƳAN HAUSA FILM LBRIN GARKUWA? WAI DA GASKENE BAZAKI ƘARASA MANA LITTAFINBA? TO DUK GA AMSARKU NAN. Alhamdulillah, ngd matuƙa da kulawarku. Kana ina mai baku tabbacin EHHH TABBAS NA SAIDA LITTAFIN GARKUWA GA ƳAN HAUSA FILM KAMAR DAI YADDA KUKAGA YAKETA YAWO, TABBAS NA SAIDASHI WA ƊAYA DAGA CIKIN MANYAN INDOSTIRI. DA IZININ UBANGIJI ZASU JUYASHI ZUWA FILM MAI ZAMAN KANSHI, IN LOKACIN YAYI KUMA ZAN SANAR MUKU. DA FARI NASO IN SIRRANTA ZANCEN NE, SABIDA SEDA MUSU DA NAYI BAWAI YANA NUFIN BAZAN ƘARASA LBRIN GARKUWA BANE, ZAN ƘARASA MUKUSHI HAR ƘARSHE DA IZININ UBANGIJI. TO SAI DAI NAYI MATUƘAR MAMAKIN YADDA AKAYI MGNAR TA FITO FILI TA BAIYANA HAR TA BAZU, domin naso barinta sirrin kai da kaina sabida gudun kada hankalin makaranta na ya tashi. To amman ba komi ku kwantar da hankalinku masoya na zan ƙarasa GARKUWA lfy lau. Kana suma ƴan film zasuyi abunsu lfy lau. Duk wacce ta/ya sayi littafin GARKUWA sun san uzurina da yasa kwana biyu bana Update, so ku kwantar da hankali ku, in sha Allah ni AYSHA ɗiyar ALIYU GARKUWA, Jikar Malam Muhammad Babayo mai Murare. Zan ƙarasa mukushi lafiya in Allah ya aramin rai da lfyar.
KUYI HAƘURI WAƊANDA SUKAYI MIN MGN TA PC BABU TABBACIN ZAN BIKU ƊAYA BAYAN ƊAYA IN BAKU AMSA.

FATAN AL’KHAIRI MASOYANA MAKARANTA LITTAFIN GARKUWA WAƊANDA SUKA BIYA DA WAƊANDA KE KARANTA NA SATA????????????????????????????. Dan naga masu karanta na satan ƙarfin halinsu yawa gareshi, har ƴar guntuwar nasiha sukemin wai kada in zalinci mutane na fara musu ban ƙarasa ba????????????. Ɗan Adam kayan Allah ana ɗauke damu muna ɗauke da halayenmu????????????????.Cikin sassarfa bisa tsarin addinin yaci gaba da ɗawafin.
Yana mai bin bayan tawagar mutanen da yaga fuskar wannan mutumin a cikinsu.
Idonshi yaketa karkasawa amman ina ya kasa sake ganinshi.
Zuciyarshi nike da mamaki.
Haka yaci gaba da ɗawafin.
Saida sukayi. Kana suka fito.
A hanyarsu ta komawa gidane ya haɗu dasu Jannart da Jazrah da Umaymah da Sitti da kuma Aunty Hafsat ƙanwar Umaymah dake ƙasar Masco.
nan Aunty Hafsat tayi ta sayan kayan tsaraba tana bawa Sheykh wai a kaiwa surkarta.
Dan dole ya amsa sai kuma Aunty Rahma ƴar autar Sitti itama a gaban Aunty Hafsat ta girma.
Kuma sa’ar Sheykh Jabeer ce shiyasa akwai yar tsama a tsakaninsu.
Cikin hausarsu data fara basu wuya tace.
“Ba dai kayi auren sirri ba, in sha Allah zanzo zamuzo auren Haroon zamuga amaryar, inga surkar tawa ya take”

Taɓe baki yayi tare da cewa.
“Ke tafi daga nan da Allah ki bar manya suyi mgna ba irinki ba”.
Murmushi Umaymah da Aunty Hafsat sukayi dan sun san tsamarsu.
Kuma suna masifar shiri.
Ammi suke kiranta ita Aunty Rahman.

Jazrah kuwa hakanan take jin daɗi in ta ganshi.
Shiyasa taketa murmushi.
Haroon kuwa girarshi ya ɗagawa Jannart tare da cewa.
“Wai auren ya kusa ko?”.
Cikin jin kunyar Umaymah tace.
“Ban saniba.”
Haka dai sukaci gaba da tafiya.

Washe gari da safiya.
Duk kan al’amur musulmai na duniya suna farin ciki da ranar salla.
Manya da yara tsoffi maza da mata duk anata shirin zuwa idi. A dukkan ƙasashen duniya a ko wani saƙon da suke da musulmai.

Hakace ta kasance a ƙasashen Afrika ma.
Wanda ciki ƙasar Nigeria yake.
Tun daga idar da sallan asuba.
Saratu da Larai sukazo.
Nan suka samu Ummi da Shatu suna kitchen.
Its Ummi fura take kirɓawa mai ɗan karen laushi da ƙamshi yaji sugar.
Ita kuwa Shatu dakkeren Couscous tayi, dambu inji hausawa.
Bayan sun gamane suka killace shi gefe.

Kana ita Shatu. Ta haɗa kajin nan tayi Pepper Checken mai ɗan karen kyau yaji jajjagen taruhu da al’basa mai yawa ga kayan ɗan-ɗano dana ƙamshi sunji komai yayi maɗau.
Su Sara kuwa robobi ta miƙo musu, suka rinƙa mulmula gumbar nan manya manyan mulmulellen masu kyau sai sheƙi da ƙamshi gumbar keyi, dakkeren kuma a robobi Ummi ta rinƙa zubasu.
Hibba ce data shigo tare da kuloli a hannunta tace.
“Wow Aunty Shatu lallai yau masarautar Joɗa zata amsa sunanta masarautar Fulɓe zata kuma gane an auro mata cikekkiyar ba fulata, gsky tsarin yayi kyau”.
Cikin jin daɗi Ummi tace.
“Gsky nima naji daɗin wannan abu.
Dama ace ko wanne yare ranar salla tayi abincin da yarenta keyi ta rabawa maƙota.
Hakan zaisa asan cimar juna, kuma yasa aci abincin salla da marmari, amman kayan haushi duk sai a tafi kan shinkafa taliya masa, da dai ire-iresu.
Su kuma akeci kullum”.
Murmushi Shatu tayi tare da cewa.
“Ha Ummi ai yanzuma sai nayiwa su Jalal koda dafadukan taliyace, nasan zasuce wannan ai sai mu”.
Da sauri Hibba tace.
“Tab wlh Aunty Shatu karkiyi komai, kinga yanzuma an kawo abincin gidan Barrister Kamal.
Ga kuma na gidan Aunty Juwairiyya.
Sannan kuma Gimbiya Aminatu ma zata aiko”.
Cikin sauri tace.
“Allah ko Ummi mu huta kawai kenan?”.
Da sauri tace sosaima.
Dan duk yawanci sai an kawo abinci nan wai tunda ke baƙuwace, wannan karamawar masarautar Joɗa akan bago.
Kuma koda kin dade ana aikawa juna abincin salla part 2 part”.
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa.
“Shike nan mu haɗa wannan a kai ko wanne sashin”.
Ta ƙarishe mgnar tana rufe ƙatuwar Foodflaks ɗin da ta juye Pepper Checken ɗin.
Bayan ta ɗebawa sashin Ya Jafar da kuma Lamiɗo da Hajia Mama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button