GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Dai-dai lokacin kuma Sitti ta fito daga falon Jadda tazo falonta, nan ta samu su Goggo Mairo duk sun tafi sai Ibrahim da Safiyyah da ƙannen iyayensu.
So bayan sun gaisa da Ibrahim ne take tambayar.
“Ibrahima ina Jazlaan ban ganshi ba tunda kukazo, bai shigoba, ga can jadda ma yace kuje yana nemanku”.
Shi dai Ibrahim murmushi kawai yayi yaci gaba da wasa da yaronshi.
Safiyyah ce tace.
“Yana bedroom ɗinki tun ɗazu ma shi muke jira duk kowa ya tafi saura mu.
Su Azeema ma sun tafi da abokan Ya Haroon”.
Da sauri ta miƙe ta nufi special Side ɗinta kai saye bakin ƙofar Bedroom ɗinta ta nufa.

Tana isa tasa hannu tana ƙoƙarin buɗewa tare da cewa.
“Jazlaan! Jazlaan!! Jazlaan!!!”.
Kamar a wata duniya ko cikin mafarki haka yake jiyo muryar Sitti.
cikin sauyawar tsari ya fara ƙoƙarin janye harshenshi daga gareta, amman ina ta riƙe gam. Cikin sauri ya buɗe idonshi ya zubasu kan fuskarta,
wani irin sanyi yaji yana ratsa zuciyarshi.
Jin motsin turo ƙofarne ya sashi yunƙurawa da ƙarfi ya janye harshenshi tare da janye jikinshi ya miƙe tsaye cikin tsananin kunyar kada Sitti ta shigo ta sameshi a wannan yanayin.
Al’kyabbar ajikinshi ya fara bazawa yana buɗata yana gyarawa.
Ita kuwa Aysha jin yadda ya zare harshenshi da yadda ya miƙene yasata dawowa cikin haiyacinta daga gigitar da ya sakata.
Jiki na rawa ta mike zaune tare dasa tafin hannunta tana goge damshin bakinta cikin tarin azabebiyar kunyarsa.

Sitti kuwa tana shigowa ganinshi tsaye yana murmushi yasata isowa gareshi ruggumeshi tayi cikin tsananin jin daɗi tace.
“Masha Allah. Marhababika ya Habibi, ana Uhubbuk”.
Murmushi yayi tare da janye jikinshi gareta kana yace.
“Ana uh hibbuki hubban azeem ya Sitti”.
Hannunta tasa ta shafa kansa fuska cike da annurin ganin jika mafi soyuwa a gareta tace.
“Jazlaan me zan kawo maka? me zakaci? me kake da buƙata?”.
Murmushi ya kumayi kana ya zauna bisa kujerar sarautar dage gefenshi tare da cewa.
“Sitti na samu komai”.
Sai kuma ya ɗan kalli Aysha ta wutsiyar idonshi.
Har yanzu jikinta na tsuma.
Safiyyah ce ta shigo da sallama tare da cewa.
“Ya Sheykh mu tafi darefa nayi”.
Kai ya gyaɗa mata alamar to.
Ita kuwa juyowa tayi ta kalli Aysha tare da cewa.
“Kin gama shiryawa ko”.
Itama kai ta gyaɗa mata.
har ta buɗi baki zata kuma yin mgna sai tayi shiru jin Sitti na cewa.
“Yauwa to kuzo taso muje Jadda na son ganinku mu tafi ko”.
Ta faɗa tana miƙewa tsaye.
Safiyyah ce ta fara binta a baya kana Sheykh.
Har sunje bakin ƙofar fita ya ɗan juyo ya kalleta a fakaice.
Mayafinta take yafawa tare da biyo bayansu.
A falon suka samu Ibrahim, nan ya miƙe yabi bayansu.

Kai tsaye Side ɗin Jadda suka nufa.

Shi kaɗai yake zaune a falon nashi dan ya bar fada yace zai gana da jikokinsa.

Cikin murmushi mai cike da kamala da dattaku, yake kallonsu tare da cewa.
“Lale marhabin da jikokin Sitti da Jadda.”
Ya ƙare mgnar yana miƙawa Sheykh da Ibrahim hannunshi, Sheykh ne ya riƙe hannunshi na dama kana Ibrahim ya riƙe na hagu suka zauna suka sashi a tsakiya.
Safiyyah ce ta matso gefen mijinta ta zauna.
Ita kuwa Aysha a hankali ta rusuna zata zauna a gefe, da sauri Sitti tasa hannunta ta kamo nata tare da cewa.
“Matso nan kusa zauna kusa da mijinki shine farin cikinmu.
Yau gamu Allah ya nuna mana matar Sheykh.”
Ta ƙare mgnar tana ajiyeta kusa da Sheykh har jikinsu na gogar na juna.

Murmushi mai cike da so da tsammani da zato Jadda yayi tare da cewa.
“Amaryar Sheykh jikar Sitti da Jadda”.
Cikin murmushin tace.
“Allah rene Jadda Allah nɓeddu sabbugo”.
Wani irin murmushi mai cike da masha hurin daɗi Jadda da Sitti sukayi tare da haɗa baki wurin cewa.
“Amin Amin, tare dake da mijinki”.
Cikin tura baki Safiyyah tace.
“Ikon Allah wato banda mu”.
Da sauri Sitti tace.
“Wa lakum”.
murmushi sukayi dukansu, kana Jadda yasa tafin hannunshi bisa tsakiyar kan Sheykh da Ibrahim tare da cewa.
“Wannan kawuna biyu duk masu ɗaukan rawanin girmane, hakama na ukunku Haroona shima akwai nauyin rawanin bisa kansa.
Ibrahim da Haroon bani da fargaba a kanku.
Amman shi Muhammad Jabeer akwai ruɗu a al’amarinsa akwai firgitarwa, yana tsakiyar Magauta.
Sun kuma rigayemu sanin rawani na bisa kanshi.
Shiyasa sukeyi mishi zagon ƙasa tun yana ƙaramin yaro.”
Shiru sukayi dukansu suna jin zantu kanshi, shi kuwa ɗan tsagaitawa yayi kana ya kalli Aysha yafi tota yayi da hannu alamun ta ƙara matsoshi.
A hankali ta rarrafa ta matsoshi, kanta ya dafa kana yace.
“Wata rana kina iya zama a matsayin da Gimbiya Aminatu take a yau.
Ban saniba ko kafin lokacin ina raye, ko na amsa kiran Ubangiji na.
Ga Muhammad Jabeer mijinki ne, kuma uban ƴaƴan kine, in sha Allah, sannan GARKUWArki. Dan Allah Aysha na baki amanarsa ki zame mishi GARKUWA ki kula da damuwarsa tun kan ta riskeshi.
Yanada nauyi a cikin zuciyarshi mafataucine a faɗin duniya yana neman wani abu nasa mafi, ƙololuwar daraja ga ɗan adam daya ɓace matsa tsowon shekaru masu yawa, a hasashen da akayi mana zaki iya haska mishi hanyar da zaibi ya ganoshi”.
Kai kawai take gyaɗa Dattijan tanajin hawaye na cika mata ido.
Da kalmarshi ta ko yana raye ko ya amsa kiran Ubangiji.
Shi kuwa Sheykh lokaci ɗaya yanayin fuskarshi ta sauya cikin muryar dake nuna dafin zafi da tiririn da ke cikin zuciyarsa yace.
“Uhummm Jadda taimakon Ubangiji na mahaliccina masanin zahiri da baɗini kawai nake nema, shi zai haskamin hanya in riski haskena.
Zanyi ta roƙonshi kuma da fatan ya baku aron rai da lfy har sanda burinmu zai cika.
Ina addu’o’in Allah ya bawa magautanmu lfy da rai har zuwa lokacin da gsky zatayi halinta”.
Tuni Safiyyah da Sitti sun fara sakin Shessheƙan kuka.
Wanda sam Aysha ta gaza gane dalilinsa kalaman Jadda da Sheykh kuwa sunyi mata ɗaurin talala a ƙoƙolwarta, ta gaza gane bakin zaren haka yasa ta tattare yawun bakinta cikin kukan da taji yana son kubce mata tace.
“In sha Allah Jadda zan kula da amanarka iyakar iyawata.
Zan kuma tayashi da addu’a koda bana yankin da yake.
Tabbas watan-wata-rana gsky zatayi halinta”.
Sai ta kuma kalli Sitti da Safiyyah tare da cewa.
“Sitti kiyi haƙuri du ban san zafin me kikeji a zuciyarki ba, amman kukanki yamin kama da kukan uwar data rasa ɗanta, kiyi haƙuri”.
Da sauri Sheykh ya miƙe ya fita, hakama Ibrahim.

Safiyyah kuwa hawayenta ta share kana ta kamo hannun Aysha tace.
“Jadda mu zamu tafi kada dare yayi mana”.
A hankali Yace.
“Bazaku tsaya kuyi sallan la’asar ba”.
Sitti ce tace.
“Sai dai suyi a hanya naga yadda Sheykh ya fita bazai dawo cikiba”.
Kai ya jinjina kana yace.
“To Allah ya kaiku lfy ya tsare hanya.
Aysha Allah yayiwa aurenku al’barka”.
Kusan a tare sukace Amin.
Kana suka miƙe suka fita.
Shi kuwa Jadda ya kira Sarkin dogarai ya bashi umarnin a haɗa motar dogarai hudu suyiwa jikokinsa rakiya.

Biyu a gaba biyu a baya tasu Sheykh a tsakiya.

Wacce Sheykh da Aysha suna baya.
Ibrahim da Safiyyah suna gaba, Ibrahim ke jan motar.

A haka suka bar masarautar Jalaluddin suka nufi jihar Tsinako.

Tafiyar mai yar tazara ce.

Shiru cikin motar Ba maiyin mgn, Sai sautin Radio da suka kunna.

Jingine yake da kujerar yayi shiru, idonshi a lumshe sai lips ɗin shi da yake motsawa alamun yana tasbihi kamar ko yaushe.

Ita kuwa Aysha sosai ta faɗa duniyar nazari.

Ibrahim kuwa ya maida hankali kan tuƙin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button