GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

A haka suka fito, suna tafe hadimansu na biye dasu a baya.
A hankali ya ɗan juyo ya kalli Jamil da yasan yanada rauni dan Jamil yanada tausayin ɗan uwanshi duk da yanada shekiyanci amman yanada rauni a kansu abu kaɗan ke sashi kuka,
Sashin dake tsakanin sashin su Jamil dana Ya Jafar suka wuce wanda nanne sashin Sheykh, sashin su Jamil ɗin suka shiga.
Kai tsaye suka wuce har cikin bedroom.
Tsaye suka sameshi yana taje suman kanshi mai yawa ga wondo iya ƙugu duk rabin boxes ɗinshi a woje ga wondon da rabin jiki duk woje waishi kirezi ko? da alamun fita zaiyi.
“Meya hanaka zuwa masallacin jumma’a da wuri jiya?
Waɗannan kolaben barasar na waye ne?”.
Sheykh ne ya jero mishi tambaya biyu a lokaci guda,
A hankali Jalal ya juyo cikin shakku da shayi da kwarjin Hamma nasu ke sasu ji yace.
“Mamace ta aikeni, jiya shiyasa na dawo a ƙurerren lokaci.
Kolaben barasar kuma nasu Ashid ne, na kwace ne lokacin da suka saya, dan karsu sha”.
Kanshi ya gyaɗa dan ya gamsu ya kuma yarda dan yasan duk rintsi ƙanennshi basa mishi ƙarya.
Cikin faɗa yace.
“Ka kula da salla, ka tsaida ita kan lokacinta, kasan irin abokan da zakayi yawo dasu, ka tabbatar kaikeyi nasara akan juya halaiyarsu daga mummuna i zuwa kekkyawa. Shiyasa ban hanaka mu’amala da suba, domin manzon Allah yace.
“Mutun ɗaya ya shiryu ta dalilinka, tarin ladan yafi a baka tarin jajayen raƙumi.
Kada ka bari suyi nasarar juya rayuwarka daga kekkyawan i zuwa mummunan.

Kanshi ya gyaɗa cikin ladabi yace.
“In sha Allah”.
Daga nan suka juya baki ɗayansu,
Kai tsaye sashin Hajia Mama suka wuce.
Inda hadimanta sukayi musu iso,
Har cikin bedroom ɗinta suka shiga,
A bakin gado suka sameta, zaune, yayinda baiyawarta Mansura keyi mata tausa.
Murmushi tayi tare da kallonsu yadda suke a jere, koda maƙiyinsu ne sai sun burgeshi sun bashi sha’awa yayi fatan inama da ƴaƴansa ne.
Kan dantsatsetsen shimfiɗar kilisa mai kyau da zanen tsuntsuwar ɗawisu, suka zauna,
Cikin kula tace.
“GARKUWAN FULANI, Jamil, Jalal, Allah yayi muku al’barka”.
Amin Amin, Sheykh da Jamil suka amsa,
Jalal kuwa shiru yayi,
Ita kuwa Hajia Mama murmushi tayi tare da cewa.
“Babanmu mai Al’farma Sarkin Musulmai Jalaluddin meya farune naga fuskarka a haɗe?”.
Kanshi ya girgiza alamar.
“Babu”.
Shi kuwa Sheykh ido kawai ya zuba kan wayarshi,
Jamil ne ya ɗan gyara zama, tare da cewa.
“Mama Abba fa”.
Kai ta ɗan jinjina tare da cewa.
“Abinda yasani nemanku kenan, Abbanku ya tafi Abuja jiya da dare, yanzu kuma Gimbiya Samira zatabi bayanshi”.
Shiru Sheykh yayi a ranshi yake jinjina al’amarin mahaifinsu.
Babusu a cikin dukkan sabgogin rayuwarsa komai nashi saidai suji a bakin Hajia Mama ko kuma a jaridu ko gidajen Radio ceɗi meɗinshi da amaryarshi Gimbiya Samira ƴar sarkin Nokan ce ita kuwa mijinta shine rayuwarta babu ruwanta da sabgar kowa.
Sam Abba bai shaƙu dasuba da wuya ka ganshi zaune dasu yana hira dasu kamar uba da ƴaƴan shi.
Saɓanin Maimartaba ko meye zaiyi Sheykh zai sani shine mutumin da yake shawara dashi akan duk abinda ya shafi addini.
Kanshi ya ɗan kauda tare da cewa.
“Allah ya dawo dashi lfy”.
Amin Amin sukace baki ɗayansu,
Cikin kula yace.
“Hajia Mama Affan fa sai yaushe zai dawo?.”

“Next month?”. Ta bashi amsa a gajarce.

A gogon hannunshi ya ɗan kalla kana a hankali ya miƙe tare da cewa.
“Zan wuce Hospital shugaban ɗaliban makarantar ya kirani cewa sunada mara lafiyar da take buƙatar kulawar gaggawa”.

Kai ta ɗan rausayar tare da cewa.
“A dawo lfy”.
Amin Amin sukace kana suka fita suka tafi.

Daga nan kai tsaye FADA suka nufa.
Inda sarkin fada yayi musu iso zuwa ga Maimartaba kakansu.

Suna shiga suka samu fada na cike da dattawa karsu Waziri, Matawalle, Galadima, Wambai, Ɗan isa, ɗanm’ buram, sairkin Dogarai sarkin Gida, da kuma Duba gari, kana, sai kuma hadiman dake tsaye bayan sarki sunayi mishi fifitar sarauta da maficin fiffigen Ɗawisu.

Farin dattijo bafulatani, mai cikar haiba.
Yana cikin manyan kaya na sarakai, wanda al’kyabbarsa kaɗai ta kai kuɗin mallakar wani gidan,
A gabanshi suka zauna gaba ɗayansu uku,
A hankali Sheykh yasa tafin hannunshi kan rumfar sawun kakan nashi da suke kan wani tim-tim mai girma da masifar taushi.
taɓa sawun kakan nashi yayi tare da cewa.
“Barka da hantsi Maimartaba, ya sawun naka?”.
Duk maganar nan da yayita a hankali yake yinta ko Jamil da Jalal dake gefenshi basujiba.
Shi kuwa Maimartaba hannunshi ya ɗaura kan tsakiyar kan Sheykh wanda tun kafin ya zauna ya tura hulanshi ya koma baya, dafa tsakiyar kanshi yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah”.
Sai kuma ya kalli Jamil da Jalal da suke gaidashi,
dan su sai yanzu suka haɗu dashi tunda gari ya waye,
Tsaɓanin Sheykh da kullum tare suke dawowa masallaci sallan asuba daga nan kuma ɗakin hutunshi suke shiga kakarsu mace ta kawo musu abin taɓawa.

Bayan sun gaggaisa ne da mutanen fada, suka fita suka tafi.

Sashin kakarsu Gimbiya Aminatu suka nufa.
Basu da hijabi da sashin kakar tasu shiyasa kai tsaye suka shiga a falo, suka sameta,
Da alamun yanzu ta fitito Dan ga al’kyebba a jikinta ga kuma hadimanta a zagaye da ita.

Cikin tarin so da ƙaunar Jazlaan ɗin nata take kallon su,
Murmushi tayi tare da cewa.
“Miskili kafi mahaukaci ban haushi, kai dai kaji abinda malam zaice kada kace zaka binciki aikin malam”.

Shiru Jamil da Jalal sukayi, shi kuwa Sheykh ido ya zuba mata.
Ita kuwa rausayar da kai tayi tare da cewa.
“Eh mana kaji abin da malam yace kada ka duba aikinshi, dazu na gama jin wani wa’azin ka da kayi kan falala da ni’imomin dake cikin aure, kana bayani duk maluntar mutun darajarsa bata cikaba in bashi da aure.
Sai najima wa’azin kamar da kanka kakeyi.
Meyasa ne Jabeer kayi niyar yin aure mana ka cikata nasabarka da kamalarka da martaba da darajar ka data masarautar Joɗa”.
Jalal ne ya miƙe tare da cewa.
“Ke in anzo gaisheki sai ƙaƙale-ƙaƙalen zance tsiya kika iya ni na tafi dan inada aikin yi”.
Haratanshi tayi tare da cewa.
“Tafi daga nan mai ƙugu kamar buzuzu hegiyar masifa”.
Hararanta yayi kana ya juya ya fita.
Ita kuwa Gimbiya Aminatu.
Jamil ta kalla wanda shima ya miƙe yabi bayan Jalal.

Shi kuwa Sheykh numfashin ya fesar tare da cewa.
“Maganinki ya kare koda saura?.”
Da sauri tace.
“Yauwa magani ya ƙare a kawo min wani”.
To yace kana ya mike ya fita.

Daga bakin harabar sashin kakar tasu,
Fadawanshi ke biye dashi a baya har parking lot ɗinsu mai ɗan karen girma da kyau, duk zagaye suke da fulawowi masu kyau.
Wasu tsala-tsalan motocine da a ƙalla sun kai su takwas sai sheƙi sukeyi.

Da sauri Ado drevernshi ya buɗe mushi ƙofar wata mota mai ɗan karen kyau wacce bada ita ya fita jiyaba, dan ita sai ranakun jumma’a-jumma’a yake hawanta,
wannan ta yau mai kalar ruwan tokace sai sheƙi takeyi,
yana shiga sauran fadawanshi suka yi yunƙurin shiga motocin dake jere a wurin a gefen wurin wanda dasu akeyi mishi rakiya.

Da sauri ya ɗaga musu hannu, cikin in in narsa da in yana saurin mgna yake fitowa yace.
“Kkku ba bari ba’a bukatar rakiya”.
Da sauri suka ɗan rusuna tare da haɗa baki wurin cewa.
“Aje lafiya a dawo lfy Allah ya kiyaye gabanka da bayanka Sheykh”.
Amin Amin yace a taƙaice kana ya shiga motar, sarkin ƙofa ya rufe mishi marfin sannan Ado yaja suka tafi.

Suna fita kai tsaye Babbar jami’ar dake cikin babban birnin Ɓadamaya suka nufa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button