GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

A can Saudia kuma, komai na dawowarsu Sheykh ya kammala, cikin kwana uku, domin hankalinshi yayi matuƙar tashi, jin irin kisan gillar da akeyiwa makiyaya, wanda Maimartaba ne, ya gaya mishi komai, ya ƙara da cewa.
Yayi maza ya dawofa, don yana jiranshi suje tare yaje ya danni fulanin ya basu hakuri ya kuma taushesu kada su ɗauki mataki da sunan ramuwa ko ɗaukar fansa.

Hakane yasa, Sheykh ya uzzurawa Haroon dole ya gama musu komai.
A kwanaki ukun.
Ranar Jumma’a da azahar jirginsu ya sauƙa, a birnin Shehu Sokoto.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi yaso. Jikan nashi ya kwana, sai dai ina ya tike dole a lokacin Haroon ya kuma saɓan mota suka fara kita hanyan kawoshi Adamawa.
Wanda sai ƙarfe uku da rabi suka isa.
Kasamcewar dama basu taso da wuriba.
Kasancewar isar dare sukayi babu wanda yasan Sheykh ya dawo.
Ƙasar sai Lamiɗo da kuma hadimanshi, uku kacal da sune suka tarbesu.

Sai washe gari da. Asuba, sautin muryarsa yana karatun limancin Sallah asuba ne ya shaidawa mutanen masarautar Joɗa dawowanshi.

Gaba ɗaya kowa ya cika da mamakin, kana da farin cikin dawowanshi.

Duk da kasancewar sa, mai larurar da wasu ke mishi kollo ko kiranshi majanuni, yasan kiyaye lokacin salla dama yinta cikin kushu’i.
Wannan shine ya hanashi sallame sallar, da akeyi yana cikin sahu na tara,
wanda jin muryar ɗan uwanshi ƙaninshi, ya sashi zubda hawaye masu ɗumi.
Ya Jafar kenan.
Jalal kuwa dake gefenshi wata irin sassanyan ajiyan zuciya ya sauƙe tare da lumshe kekyawan ƙwayar idanunsa da suke iri ɗaya dana Sheykh, ga kuma bacci daya cikasu, domin daren jiya, Ya Jafar ɗinsu ya hanashi bacci.
Jin muryar ɗan uwansu da shi kaɗai ke iya sarrafa babban yayan nasune ya sashi sauƙe, numfashin.
Jamil da Affan kuwa, wani irin yalwataccen murmushi ya sake jin muryar ɗan uwansun.

Abbansu kuwa, shi dai har yau yana rasa me yakeji a kan ƴaƴan nashi, Especially Sheykh, yana jin zuciyarshi na mishi nauyi duk sanda yaron baya kusa dashi, sai dai kuma in yana kusa dashi sai yaji tamkar bai taɓa wani farin cikiba a rayuwarsa.
Ya sani tabbas su abun tausayawa ne, suna buƙatar kulawarshi fiye data kowa a duniya, to amman ya rasa meyasa yake jin kamar baya son kusancisa dasu.

Maimartaba kuwa, suna cikin sahun na forko bayan liman,
Sai da sauran malaman fada.

A cikin gida kuwa, jin sautin zazzaƙar miryarshi yana rere karatun al’ƙur’ani, ya ida fatiha, kana ya ɗaura, Arrahama,
daga bisani ya rufe da lakadja’akum, kafin ya tafi zuwa ruku’uh.

Haka nan Juwairiyya ta tsinci kanta da zubda wasu zafafan hawaye, masu ƙuna a rai, tabbas ta sani.
Kasan cewar Sheykh a masarautar nanne kaɗai yasa, suke a ciki.
Ta sani in badon daraja da al’farmarsa ba, da tun tuni, an tabbatar da sunan mijinta mahaukaci.
Hannu tasa ta share hawayenta cikin sanyi ta miƙe dan gabatar da sallan asuba, a zahiri tace.
“Allah ne gatanmu, kaine GARKUWAR mu, Sheykh in baka nan gidan kanyi mana duhu, ƙasar tanayi mana zafi.”
Daga nan ta tada kabbara.

Ummi Jakadiyarsu kuwa,
Tana bayan gida, tana al’wala ta jiyo muryarshi, wani irin murmushi tayi tare da yin mgna a baiyane.
“Dan Halak kaƙi ambato, ɗa ɗaya tamkar dubu, maƙiyanka fadawanka, sunyi sake ɗan zaki ya girma, in sha Allah zaka dawo da farin cikin masarautarnan, sunyi sake, sun bar kari tun ran tubani,
Muhammad Jabeer bawan Allah”.

Haka ta fito tana wasu irin kalamai masu wuyar fahimta.
A can sashin Hajia Mama kuwa,
Wata kekyawar budurwa, ce.
Konce kan gado gefen Mama, datake zaune bisa sallaya.
jiyo muryashine ya sasu saurin juyowa, suka kalli juna,
Cikin tsananin farin ciki da tarin shauƙi budurwar ta diro daga kan gadon gaban Mama ta zauna cikin zaƙuwa tace.
“Lah Mama, yaushe ya dawo! Muryar Sheykh Jabeer nake jifa! Mama ko dai dama yana nanne?”.
Wani irin kallo Mama tayi mata cikin sanyi da murmushi a fuskarta tace.
“Batul shine, ya dawo!.”
Wani irin sassanyan numfashi ta sauƙe cikin tarin shauƙi tace.
“Yes Mama, farin cikina ya dawo, kamar yasan, nazo.
Alhamdulillah, Mama Allah yana sona, ki gani ina zuwa, na samu baya nan, naji baƙin ciki kamar in mutu jiya kafin inyi bacci, sai gashi Allah ya turo minshi cikin dare ɗaya.”
Murmushi Mama tayi, tana mai jin mmkin yadda Batul ke masifar son Sheykh har take gaza ɓoyewa.
cikin haɗe fuska tace.
“To yanzu dai, sai ki tashi kiyi salla, tunda kinji muryar da kikafi so a duniya, kin sauƙo kan gadon, sau nawa ina tadake, sai kiyi miƙa ki kuma konciya”.
Cikin jin dadi tace,
“Wayyo Mama baccinne bai isheniba Allah ko jiya kwana nai ina zulumi, sai 3:44 na asuba na samu bacci.”
Murmushi Mama tayi kana ta miƙe ta kabbarta sallan.
Ita kuwa Batul, miƙewa tayi da sauri ta shige, bathroom tana cewa.
“Bari inyi wonka inyi salla, in shiga kitchin yau nida kaina zan mishi breakfast.”
Tana faɗin haka ta shige ciki.

A masallaci kuwa, ana idar da salla kamar koda yaushe, da yawa basu fitaba saida sunata lazumi.
Yayinda Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero da kuma Sarki Nuruddeen Bubayero, da Habibullah Nuruddeen Bubayero, suka jero, suka fito a jere, domin su kullum ana idar da sallan asuba, suke fitowa su koma cikin masarautar, inda kowa zai wuce Side ɗinsa,
Yayi karatun qur’ani da kuma, Dua Azkar, inda har sai rana ta fito, kana suke ɗan maida bacci, to kuma sudayin breakfast sai 11.
Suna isowa tsakiyar masallaci, Sheykh yaji an ruggumeshi ta baya, yasan mutun ɗaya ne rak zai mishi haka a cikin masallacin,
Ya Jafar ɗinsu.
Yana juyowa kuwa yaga shiɗin ne.
Ruggumeshi yayi gam-gam Jalal, kuwa ido ya zuba musu,
shi kuwa Sheykh hannu yasa shima ya ruggume ɗan uwan nashi.
Yayinda ya zubawa Jalal kwayar idanunshi, ya rame sosai, hancinsa ya ƙara fitowa, sai sajenshi daya ƙara yin lib, da uban gashin daya tara, yayi wani kafurin aski.
Ramar da Jalal yayi ta daki zuciyarsa sosai baya son ganin ƙannen nashi cikin halin matsala,
a hankali ya janye kwayar idanunshi ya maidasu kan Jamil da Affan dake gefen damanshi,
Calikan ƙanenneshi kenan ba,
sheƙiyancinsu ɗaya, baki suka haɗa wurin cewa.
“Sabahul Noor Al’Sheykh”.
A hankali ya ɗan motsa laɓɓansa, yana mai kallonsu yace.
“Sabahul khair ya Uktih”.
murmushi sukayi, suna mai jin son ɗan uwan nasu,
Abbs da Maimartaba kuwa, kai suka ɗan jinjina kana sukayi gaba,
Ganin hakane suma suka bisu, a baya,
shi kuwa Sheykh hannu yasa ya shafa kan Imran da yanzu ya iso gabanshi cikin sanyi yace.
“Hamma Jabeer barka da safiya”.
jin yana shafa kanshine ya sashi lumshe ido, inama ace yadda Hammanshi ke nuna mishi so haka zai shirya da Mom ɗin shi, yana masifar son ɗan uwanshi baya jin daɗin yadda yake ganin wata iriyar mu’amala tsakanin Mom da yayunshi.

Ganin Sheykh yaja hannun Ya Jafar sun tafine yasashi bin bayansu.

Ƙofar dake cikin masallacin wacce zata ɓulla cikin masarautarsu sukabi.

Suna shiga, kowa yayi sashinsa sabida sun sani ko sunbi Sheykh yanzu ba lokacin mgna bane, karatu zaije yayi.
Shi kuwa Sheykh yana riƙe da hannun Ya Jafar ɗinsa suka shiga side ɗinsa,
inda ya samu hadimai masu tsaron ƙofar, suna tsaye.

Suna shiga, tamtsetsen falon nashi kai tsaye ya nufi wannan babbar kusurwar da zata sadashi da.
Big part ɗin shi,
Suna shiga suka ɓulla cikin wani mashahurin, falo, wanda yaketa tashin ƙamshi mai masifar sanyi da daɗin shaƙa,
a hankali ya zauna bisa kujerar 3 str kana yaja hannun Ya Jafar ɗin suka zauna, tare.
A hankali ya juyo kanshi ya zuwa ɗan uwanshi idonu,
Karatu yakeyi kamar koda yaushe, yanayi cikin tsantsar lugga da tajwid, kana ga kushu’i,
Suratul yaseen yake karanta,
bisa alamu kenan ya kusa yayi sauƙa, domin step by step yake bin surorin, in yayi sauƙa sai ya sako daga sama, baya mancewa, kuma baya birkitashi,
Wannan rahamar da Allah yayi mishi, duk da anso a maidashi majanuni, sai Allah yayi mishi muwafaƙa da littafinsa maisarki, yazama sihirin yayi mishi tasiri tako ina, amman banda gefen addininshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button