GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Kai ta jinjina tare da cewa.
“Uhumm lallai kam, wannan ai yafi Lamiɗo ma iya ƙasaita”.
Dariya tayi tare da cewa.
Zo muje store kiga kayayyakin da yasa aka kawo ɗazu.”

To tace tare da miƙewa tabi bayanta.
Suna shiga kitchen ɗin suka ɗan haura suka taka steps ɗin da zai sadasu da ƙofar store wanda wani ƙaton freezer ke konce a wurin sai ma dai daicin Fridge.

Hannu Ummi tasa ta buɗe freezer’n.
Motsowa tayi tare da zaro ido ganin yadda aka cika freezer’n maƙil dasu Kabej Karas kokumba green beans, masu kyau sabbi.
Ɗaya sashin kuma nama ne jibge sai kifi a gefe,

Sai ɗaya Fridge ɗin kuma cike yake da ababen sha na ya’yan itatuwa dana kwalba.

Rufewa tayi kana ta buɗe mata drower’n kitchen cabinets ɗin.
Kiret-kiret ɗin kwaine kusa goma suke jere a wurin ɗaya gefen kuma katon ɗin manyan gongonayen madara da millo ne.
Sai katon ɗin sugar irin mai ƴaƴan nan. Sai katon ɗin Lipton. Da ganyen na’ana. Sai can gefe kuma su maggine da sauran kayan ɗanɗano.
dasu kanan fari citta da dai sauransu.
Cikin yin hamma tace.
“Ummi duk yaushe aka kawosu?”.
Juyawa tayi suka nufi cikin cikin store tace.
“Ɗazu da yamma kina bacci ya dawo, suda Jalal da Jamil”.
Kai ta gyaɗa tare da bin bayan Ummi. store ɗin cike yake da kayan masarufi na buƙatar rayuwa.
Danginsu shinkafa, gero, waken suya, wake ƙosai dasu alale, sugar katon-katon na taliyar manya data yara, da dai sauransu.

Sai kuma doya da dankali dake jibge a gefe, kana sai al’basa da sauransu.

Fitowa sukayi kana suka dawo kitchen.
tukunya Ummi ta ɗaura tare da ɗebo nama tazo ta wonke sabida an yanka wasu dai-dai misalin na miya, wasu kuma anyisu dogo-dogon yanka.
a tukunyar ta zuba shi, kana ta ɗauko al’basa mai girma ta yayyanka a ciki.
Sannan tasa tafarnuwa kaɗan kana tasa garin citta da kanamfari.
Tare da maggi da kori da sauran kayan ɗan-ɗano.

Kana ta kunna Gas ɗin ta ɗaura tukunyar,
ɗanyen kuɓewa ta ɗebo ta miƙawa Shatu tare da cewa.
“Wonke ki yanka min shi”.
To tace tare da amsa ta wonke kana ta fara yankawa, ita kuma Ummi al’basa da tattasai da tatuhu kaɗan ta ɗiba ta wonkesu kana ta markaɗesu dai-dai yadda takeso.

Zuwa lokacin kuma gaba ɗaya kitchen ɗin dama Side ɗin gaba ɗaya ya cika da ƙamshin tafashen naman.

Juyeshi tayi a wani kwano.
Kana tasa mai kaɗan tasa manja kaɗan. Tare da watsa jajjagen kayan miyar,
ta soyasu. Kana tasa naman da sauran ruwan tafashen.
ta kuma ɗauko bandan kifin tarwaɗa bandanshi, ta gyara ta wonƙeshi da ruwan ɗumi.
ta watsa a ciki. Sannan tasa ɗan dakekken yajin daddawa kaɗan.”
sannan ta rufe tukunyar.
ta amshi kuɓewar tana ƙarisa yankan. Tukunyar data ɗaura ruwan tuwo ta ɗan kalla ganin yana tafasane tace.
“Gacan garin semo na tankaɗeshi ɗibi kiyi mana talge.”
To tace tare da juyawa ta ɗebo tayi talgen.
Ita kuwa kuɓewar ta saka, kana ta tsalli ɗan toka ta saka.

Bayan wasu yan daƙiƙu miyar tayi lugub tayi kyau tayi kalar kore mai kyau. sabke tukunyar tayi kana tasa,
man shanu a ciki.
Sannan ta meda tukunyar gefe.
Tuwon ta tuƙa ya ɗan turara kafin ta kwasheshi tana yin mal’mala tana sawa a leda.
Saida ta cika wani madaidaicin Foodflaks mai ɗan girma.
Kana ta ɗauka ruwan zafi.
Ta tafasa tea ta ɗura a flaks tare da tarfa kanumfari da citta sai na’am.
Sannan ta rufe, ta kimtsa komai a kitchen ɗin.
Ganin Shatu nata Hamma ne tace.
“Jeki kwanta tunda mun gama aikin. Sai kuma da asuba.”
Cikin alamun bacci tace.
“To Ummi saida safe”.
Ta fita tana haɗiye minyau dan ƙamshin da miyar keyi.

A falo taci karo da Hibba Aunty Juwairiyya ta rakota, da Foodflaks a hannunsu alamun abincin sahur ne a ciki.
Cikin baccin da takeji tace.
“Mun yi girki ma, Aunty Juwairiyya”.
Kai Juwairiyya ta ɗan gyaɗa tare da cewa.
“A lallai kam sannu da aiki”.
Ta ƙarishe mgnar tana ajiye kulolin bisa dinning table.
Ita kuwa Shatu harara ta watsawa kulolin tare da wucewa tayi ciki.
Hibba ce ta biyo bayanta bayan tayiwa Aunty Juwairiyya Saida safe.

Har sun shiga Ummi ta kira wosu.
Falo suka dawo duk suna hamma alamun bacci, ganin Hamma Jabeer na zaune ne, gasu Jalal gaba ɗaya yasa suma suka ƙarasu cikin falon.
Gyara zanshi yayi tare da kallon Hibba da Aysha da duk alamun bacci ya cikasu, cikin sakekkiyar murya yace.
“T….!

Uhummm Ramadan da daɗi, Ya Allah ka nuna mana ka kaimu watan lfy ka nuna mana ƙarshensa lfy ka maimata mana.

Rayuwar Masarautar Joɗa a Ramadan yanada tsari da masifar daɗi da burge duk musulmi.

Kabcen Shatu da Sheykh a kwanakin Ramadan da bikin salla yana sani murmushi da shauƙi.????????????????

                    By
             *GARKUWAR FULANI*

“To Alhamdulillah. Allah ya kawomu watan Ramadan, wata mai tarin al’farma da al’barkatu da tarin ni’imomi. Mutane da dama Allah bai basu wannan damarba, da yawa sun rasu.
Wasu kuma basu da lfy, basu san me sukeyi ba ko a ina suke, bare su ribaci wannan dama da Allah ya bamu.
An ga wata wanda haka keda tabbacin gobe zamu tashi da azumi.
Duk kuyi niya, ɗaukar azumi talatin ko talatin ba ɗaya.”
Sai ya kuma ya ɗan tsagaita tare da kallonsu Jalal da Jamil cikin sanyi yace.
“Dan Allah Jalal Jamil ku nitsu kunsan halin da muke ciki. Kun san matsalar rayuwarmu kunsan damuwarmu, wannan dama ce da zamu yi amfani da ita wurin tsananta addu’o’in ba dare ba rana.
In sha Allah, Wata rana komai zai dai-dai-ta domin Allahu sami’uddu’a ne.
Jamil kaji tsoron Allah ka ribaci wannan watar, ka raba kanka da zuwa club, ka yayewa kanka masifar nacin liƙewa mata da waya.”
Juyowa yayi ya ɗan kalli Jalal kana yaci gaba da cewa.
“Jalal yawon bin yan iska da wani shegen shiga mara kan gado ba tsarine na Musulmin ƙwarai ba.
Aunty Juwairiyya Hibba Ummi Ke uwar bacci”.
Ya ƙarishe mgnar da kallon gefenda Shatu da take zaune tana ɗan lullumshe ido,
da sauri ta waresu don a sama taji muryar tasa. Baki ta tura tare da sunkuyar da kanta, shi kuma jenye idonshi yayi daga gefen da take cikin ɗan ɗaga sauti yace.
“Watan Ramadan ya bambanta da sauran watanni.
Domin a cikin watanne daren laylatul Ƙadir yake, kuma a cikin watanne Allah ya sauƙe al’ƙur’ani mai girma.
Kana a cikin watar akwai ranakun da malamai sukeyi hasashen a daren laylatul Ƙadir yake, Daren 21, 23, 25, 27, 29. Sai dai ba’a tabbatar, da sahihin rana ɗaya tsayeyye ba ƙauli mafi rinjaye shine ranar 27.
Abi mafi kyau shine kada mutun ya sake koda dare ɗaya na Ramadan ya wuceshi.
Mu raya dararen da ibada da ambaton Allah, wajibine mutum ya tsare bakinsa, da munanan zantuka walau a baki walau a rubuce a social media,
Domin mu ribanci watar da ambaton Allah da samun ruɓanyar lada, wannan abubuwane da kullum nake gaya muku su, sai dai aiki dasu ya gagareku.”
Kusan haɗa baki sukayi wurin cewa.
“In Sha Allah zamuyi ƙoƙarin kiyayewa”.
“Allah yasa yace, tare da sallanmansu duk suka fita sai Ya Jafar da Ummi.

Ganin yadda Hibba keta zuba hamma ne ya sashi cewa.
“Muhibbat tashi
Kije ki kwanta”.
Kusan a tare ta mike ita da Shatu.
da sauri yace.
“Banda ke”. Cikin bacci ta turo baki tare da cewa.
“Ayyah dan Allah fa”.
Murmushi Ya Jafar yayi tare da zuba mata ido.
Wanda koda baya mgna ana iya gano yadda yake sonta a ranshi, so kuma irin son da yakeyiwa su Hibba.
Ummi ce ta ɗan kalleta tare da cewa.
“A barta tai bacci aiki mukeyi tun ɗazu”.
Shiru bai kulasuba, ganin haka ita kuma tabi bayan Hibba.
A zatonta bai saniba, har sunje bakin ƙofar taji yace.
“Saura ki binƙire kiyi ta bacci, kada ki tashi ki raya daren. Sai gari ya waye ki buwayi mutane da ife-ife da rashin kunya”.
Ya ƙarishe mgnar cikin jin haushinta tare da Binta da kallon fitinenneyar yarinya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button