GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Wani irin kuka Hajia Mama tasaka tana faɗin “wayyo Allah na waishin meke faruwa damune kam”.
sai kawai ta yanke jiki tafaɗi ta kakkafe idanunta kamar wacce ta suma.

Ranar Hajia Mama haka tawuni tana kuka ta rungume Jamil da Jalal dasuke keta kuka kamar ransu zai fita.

Jadda da Sitti da Umaymah da Aunty Juwairiyya da babanta duk a ranar sukazo.
An kamo tsuntsuwar Boleru suna killaceta, yayinda aketa tururuwan zuwa ganin tsuntsuwar.

Ido da ido da Gimbiya Saudatu tazo da yake sokuwace.
Sai cewa tayi.
“Allah sarki wato al’haƙi kuikuyo ko sharrinta ya dawo kanta, ohoho larabawa an zama tsuntsuwar Boleru”.
Toh fa daga nanne Magautan su Sheykh duk suka samu suka fake suka laɓe a bayanta.

Su kuwa haka sukaci gaba da kukan Hajia Mama ko uwartace ta mutu sai haka, duk wanda yaganta sai ta bashi tausayi akasin Lamiɗo da Galadima da suka sa zargi a kanta duk abin da take shirine da zallar iya tuggu munafurci da makirci.

Tun daga lokacin tsuntsuwar nan ko ince Mamey ko yaushe sai ana kamata ita kuwa tana firewa tana komawa cikin tsuntsaye ƴan uwanta.
Al’amarin ya magaga ya tada hankalin kowa.
Ana kamata zata zille ta fire ta koma cikin Garden ta zauna cikin tsuntsayen cikin masarautar Joɗa.

Duk wannan tashin hankali da ake ciki Sheykh Jabeer bashida labari dan lokacin yana karatu a jami’ar Madina sai dai kwata-kwata a lokacin hankalinsa yakasa ƙwanciya idan yakira wayar Mamey’n sai asa Aunty Rahma ta ɗauka tayi mishi mgn wanda ita kuma dama lokacin sun zo suna nan da Mamma.
Yadda Hajia Mama ke nuna tashin hankali tane yasa suka yarda da ita.

Wannan juyewar Mamey shine.
Sanadin da Jadda ya samu hawan jini kenan.

A ranar da dare Umaymah Mamma Aunty Rahma Aunty Juwairiyya Sitti duk sun gaza bacci, sun sa tsuntsuwar Boleru a gaba Magauta na musu dariya.

Sai da asubane sun kabbarta yin salla asuba, tsuntsuwar ta tashi ta fire, Bata tsaya cikin masararutar Joɗa bama ta fuskanci ƙasar Cameroon ta nausa tayi can yankin Yahunde.

Ɓacewar tsuntsuwar nan shi yafi tada musu hankali.
Anyi neman duniya har an gaji.
Ba ita ba dalilinta har dai aka ruggumi ƙaddara.

Sai dai Lamiɗo da Galadima da Jadda da Umaymah sunci gaba da bincikawa da neman mafita.

Lokacin da Sheykh ya kammala digirin sa na farko yazo.
Nigeria nan ne ake faɗa masa abin da ya faru a lokacin tashin hankalin da kiɗimar rayuwar daya faɗa ciki baya misaltuwa wani babban tashin hankalin kuwa shine daya iske ya Jafar baya magana sai addu’o’in da yin karatun al’ƙur’ani mai girma da kuka, dakuma ya buƙaci yaje yaga Mamey’n shi a yadda take ɗin a tsuntsuwar ta ɗin, nan ake faɗa masa ai tun lokacin da abun yafaru da kwana ɗaya rak ta fire tabar cikin masarautar Joɗa.

Ranar Sheykh kuka kamar karamin yaro ya rungume Jamil Jalal Yah Jafar da tun isowarsa Jafar ɗin ke ƙanƙame da hannun sa yana karatun yana kuka haka sukayi ta kuka Hajia Mama na tayasu.
Ranar tazamo musu tamkar sabuwa.

Tun daga wannan lokacin kuma sai yazamo kamar an cire hankalin Abba’n su a kansu madadin a lokacin ya janyosu jikinshi yazame musu Garkuwa dan suɗan sami sassaucin kunar dake cikin zuciyarsu sai yariƙa nisanta kanshi dasu.
Shi kansa bai san dalilin hakan ba,
duk wannan kuma acikin shirin Hajia Mama ce, kwana ɗayan da tsuntsuwar tayi tafire ma ita takoma gun bokanta tace tanaso tsuntsuwar tabar cikin masarautar gaba ɗaya dan taga sun dage da magungunan.
Dariya bokan nata yayi tare da cewa.
“Ke shar-shar banza da kika samu ma ba Addu’o’inku na musulmai sukeyiba ai da tuni sun karya sihirin”.
Cikin jin daɗi tace.
“Aini gaba ta kaini da hankalin su baije ga canba”.

Lamiɗo kuwa lokacin ya ƙara jan Sheykh a jiki sosai.
Sabida bayanin da Malam Musa yayi musu na cewar a sanadin aurensa da ba fulatanar daji mahaifiyarsu zata dawo.
Haka yasa part in da a ka bashi kusa da Garden inda tsuntsayen suke.
aka buɗe mishi wata kofa taciki in da daga cikin part ɗin direct zai sadashi da cikin Garden ɗin.

Bai wani jima sosai a Nigeria ba yakoma Madina sabida jin yakeyi ya tsani ƙasar Nigeria Especially Masarautar Joɗa.
Koda ya koma sosai ƴan uwan Sitti suka ga canji a rayuwarsa saida aka dage da addu’a kafin ya dawo hayyacinsa.
Daga nan suka ƙara kula ta musamman a kanshi suka zame mishi uwa uba ƙanne yayu sukeyi mishi komai.
Yakanyi shekara uku huɗu bai zoba.
Sai dai yana yawan sawa Jadda yazo mishi da Jamil Jalal Yah Jafar da Affan yawanci duk shekara zasu zo sau biyu hajji da umra wani shekaranma sau uku.
Ya maida hankali sa kan karatunsa da addu’a Allah ya baiya mishi Mameynshi a duk inda take ko a tsuntsuwar Boleru shi zaici gaba da rainonta da kula da ita iya rai da mutuwa.

Daga nan yayi master’s madadin ya dawo ya haɗe. PHD ɗinsa. daga nan yadawo Nigeria’n bisa tirsasawar Lamiɗo da Jadda da Galadima da Umaymah dake matsayin Uwa.
Dole ya yarda ya dawo ya sanyawa ƙannensa ido wajen kula da su dakuma tarbiyyan su dakuma neman hamaifiyar su da kula da yayansa yakuma zame musu Garkuwa Da kuma bincikar Magautansu wanda dalilin haka ya samu matakin SS wanda dama shine burinsa to kuma Alhamdulillah ya gane komai Especially da ya samu damar aikin SS wanda dama burinshi kenan a dole Lamiɗo ya sashi karantan likitancin.

A kwai sabo ƙauna tausayi da shaƙuwa da tsama tsakaninshi da kakanun nashi sosai.

Hajia Mama kuwa da gayya ya barta da wayonta ita tanayi mishi kallon biri shi yana mata kallon ayaba.

Dama kuma malam Musa.
Ya faɗa musu cewa sanadin Sheykh ɗin ne Mamey’n zata dawo yabasu lbrin iya abinda Allah ya sanar mishi cewa bata rasuba tana raye kuma tajuye daga tsuntsuwar dasuke tunani tadawo mutum tuntuni tun bayan tafiyarta da watanni.

(Rayuwa kenan takan iya sauyawa a duk san da Allah yaso domin shi yake juya daƙuƙu i zuwa sa’a wuni zuwa dare kwana zuwa shekara ya fidda matacce a cikin rayayye ko ya fidda rayayye a cikin matacciya)

Ajiyan zuciya mai nauyi suka sauƙe baki ɗayansu da suke cikin falon.
Bayan ya Jafar yagama basu labarin yadda akayi da abinda ya sani har Mamey’n su ta juye ta zama tsuntsuwa da kuma yadda akayi shima yakoma baya magana sai kuka da karatu.

Gabaki ɗaya parlour’n ya kaure da ambaton sunan Allah da yiwa uban giji tasbihi.
Ita kam Mamey sai murmushi takeyi tare da maimata.
“Alhamdulillah! Alhamdulillah alakulli halin”.

Affan kuwa kuka yakeyi tamkar ransa zai bar gangar jikinsa.
Cike da rauni Sheykh ya jawoshi jikinshi ya ruggumeshi suna masu zubda hawaye baki ɗayansu.
Cikin rauni da tausayin irin kukan ƙuncin da Affan keyi Lamiɗo ya gyara zama tare da yin gyaran murya kana ya juyo ya kalli Bappa tare da cewa.
“Ka bamu labarin yadda akayi.
Aishatu tashigo hannun ku”.

Ai kuwa kaf hankalin jamar parlour’n yadawo kan Bappa dan kowa nason jin yadda akayi Mamey’n tashigo hannunsa gaba ɗaya shi suka zuba ido.

A hankali yayi Bappa gyaran murya tare da gyara zamanshi kana ya ɗago hannunshi ya nuna Shatu da yatsarsa manuniya kana yace.

“Shatu itace sanadin.
Dan a lokacin da tashigo hannun mu mu muna mata kallon tsuntsuwar Boleru ne tsawon kusan wata bakwai muna tare da ita muna ganinta Giɗi yarona shike kula da ita saida ya zama tare suke cin abinci.

To Shatu itace ta fara ce mana ba tsuntsuwar Boleru bace mutunce ita a ranar wata jumma’a da tazo tare da mahaifin ta Alhaji Abboi wanda ni makiyayinsa ne.
Nan taga tsuntsuwar yara na son kamata su yaran damu manyan duk muna cewa tsuntsuwa ce.
Ita kuma tana cewa mutum ce.
Wanda haka yasa dole basu koma cikin birnin Yahunde a ranarba ita da mahaifinta suka kwana a gidana a Rugar Arɗo Babayo wanda nanne asalin mahaifata.
haka ta kwana tana gaɗin tsuntsuwar har dai Allah yanuna mana ikon sa da asuba tajuya ta dawo mutum a gaban idonmu,
Sai dai tana cikin larurar naƙuda.
Cikin ikon Allah ta haifu ta sauƙa lfy ta haifi ɗiyarta mace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button