GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Rage kayan jikinshi yayi kana yasa hannunshi ya jawo pillow’nshi ya wurgar can gefe gaban gadon inda babu carpet,
a hankali ya kwanta a wurin,
Gudun kada daɗi gado yasashi yayi baccin da zai makara sallan la’asar, Yana konciya ba jimawa yayi bacci.

Ita kuwa cikin jin daɗin amincewar da yayi, tacewa Ummi.
“Ummi ya yarda yace muyi”.
Miƙewa Ummi tayi tare da nufar kitchen a tare suka shiga.
Tana cewa.
“Yauwa to taho mu gayawa Saratu abinda za’ayi.

A tsaye suka sameta a tsakiyar kitchen ɗin kusa da kitchen table, tana gyara ganyen.
“Yauwa Saratu kin wonke shinkarfa masan ne?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh na wonke,kuma mafa tun ɗazu da nazo kuna kuma bacci na jiƙa wani, sai dai hannuna ya zarce yayi yawa, yanzu ina gama tsinkar ganyen zan kai markaɗen ne in na dawo an kwaɓashin sai in fara firan Arish ɗin”.
Ajiyan zuciya Ummi tayi tare da cewa.
“Mugamshin”.
Babbar robar dake gefenta ta jawo tare da cewa.
“Gashi kinga yayi yawa wlh mancewa nai sai naga kamar na gidan Gimbiya Aminatu zan jiƙa shiyasa, kinga da na haɗa da wanda kika jiƙan yayi yawa sosai, ko zamu rabashi biyu”.
Murmushi Shatu tayi ganin shinkafar tanada yawa, kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Ba matsala hakanma yayi dama mai yawan akeso”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Ga kuma ƙullun na dafa tun ɗazu har yayi sanyi, shiyasa nake sauri in kai markaɗen naga lokacin yayi nisa”.
Motsowa tayi inda take tare da cewa.
“Ɗauki markaɗen ki kai bari in ƙarisa wannan aikin”.
Cikin mamaki tace.
“A a bar”.
Da sauri ta katseta da cewa, jeki”.
To tace cikin mamakin sauƙin halinta ta ɗauki robar jiƙeƙƙiyar shinkafar da ta kai mudu biyar har ta ɗaura a kai,
Ta kuma sauke jin Shatu na cewa.
“Yauwa naga akwai murjejjiyar gyaɗa, ɗebo, da wata shinkafar kizo ga dabino da kwakwa a nan ki haɗa ki jikasasu ki tafi dasu, na kunune kafin a markaɗa wannan na masan shinma ya jiƙa sai a markaɗa miki shi.
Da sauri ta juya tayi yadda tace ɗin tanayi tana nuna mata dai-dai yadda takeso, saida ta gama kana rufe babban roban da marfinshi sannan ta ɗaura ƙaramin a kai ta tafi.

Ita kuwa Shatu matsowa tayi taci gaba da tsinkan ganyen, ita kuma Ummi freezer’n ta buɗe tare da ɗebo kayan ciki mai yawa, tazo.
Ta wonƙeshi fes, kana ta watsa al’basa mai yawa a ciki, Sannan tasa citta,kanamfari, cory tare da sauran kayan ɗanɗanon.
Gas ta kunna ta ɗaura tukunyar, sannan ta dai-dai-ta wutar.

Wani babban roba ta ɗauko kana ta nufi Store Arish ta ɗebo mai ɗan yawa tazo tana fereshi cikin ɗan injin ɗin firar lokaci ɗaya tayi nisa a fitar.
Ita kuwa Shatu tana gana gyaran ganyen ta ɗebo kayan miya tazo ta jajjagasu yadda takeso.
Kusan a tare suka gama da Ummi.
Wankeshi Ummi tayi bayan ta yishi tsillk-tsillk kana ta sashi a tukunya, tare ɗan yaryaɗa gishiri, ta rufeshi.
Ta ajiye gefe.
Ita kuwa Shatu cikin kula ta kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi me za’ayi da ganyen?”.
“Miyan da za’aci masar dashi”.
To bata amsa tana komawa cikin Freezer’n fruits ta ɗebo.
Tazo tana wonkesu tare da shiryasu cikin tray mai girma, kana ta shirya wasu kuma a wani ɗan madaidaicin tray mai masifar kyau.
rufesu tayi kana taje tasasu cikin Fridge.

It’s kuwa Shatu can nama ta ɗebo dai-dai misali wonƙeshi tayi tasa a tukunya tare dasa kayan ƙamshi dana ɗanɗano.
ta ɗaura a wuta. Ummi kuwa ruwan tea ta ɗaura a ɗaya murhun dake gas ɗin babbane.

Naman na sulaluwa ta kwasheshi tasa mai saida yayi zafi tasa al’basa,
ya soyu yana ƙamshi kafin tasa jajjagen kayan miyar ta,
Ya soyu kana ta ƙara wonƙe ganyen miyar yazo tasa, ta soyashi da kyau.
kana ta zuba naman da sauran ruwan miyan.
Tasa duk sauran kayan hadin ta rufe tukunyar.
Sosai Ummi tayi mamakin yadda ta haɗa miyar, to sai dai bata damuba sabida sanin ko wacce mace da yadda take sarrafa girkinta, kai yadda kakeyi daban in wani ya gani yayi mamaki, yadda wani keyi da ban in ka gani kayi mamaki.

Cikin ƙanƙanin lokaci dai suka haɗa duk aiyukan da zasu iya ajiyesu ba tare da sun samu matsalaba.
Ita tayi miyar masan, ta kuma ƙarisa ferfesun kayan cikin da Ummi ta fara.
Ummi kuwa ta tafasa musu tea ta ɗuɗɗura a flaks,
Kana ta tafasa Arish ɗin.
Dai-dai lokacin kuma Saratu ta dawo.
Ita Ummi ce ta ɗan amshi ƙullun masar tare da cewa.
“Gskya mun ɗan makara aikin Masar nan gashi ni hannuna baya tashi da wuri”.
Da sauri Shatu ta matso tare da miƙawa Ummi roban markaɗen kunun.
Tace.
“Ba matsala Ummi ni hannuna na tashi da wuri.
Yanzu tace mana marƙaden kunun bari in kwaɓa mana Masar.”
Haka kuwa akayi Ummi ta fara tacewa.
Ita kuwa kulun dafaffiyar ɗanyar shinkafar ta murmusa cikin marƙaden Masar,
Kana tasa fulawa tare da yis kaɗan sannan ta tarfa gishiri kaɗan.
Kana ta rufeshi a robar dan babbace, motso da robar tayi kusa da Gas ɗin yana ɗan jin ɗumin wuta.
Gefen Ummi ta dawo wacce ta gama tace markaɗen
A babbar tukunta ta zuba shi kana ta ɗaura kan wuta tare da dai-dai-ta wutar tanayi tana motsa kunun.
tare da ɗan tarfa wanda ta rage, da surkin lemun tsami.
Cikin Sa’a ɗaya ta dama kunun shinkafar fari ƙal tamkar madara.
Sugar tasa ta juye a a ƙatuwar kula kana tasa a maidaciyar kula, Sannan tasa a flaks ɗaya, sai kuma tasa a Mug mai marfi duk ta kimtsasu gefe.
Tuni Side ɗin ya ɗin ke da ƙamshi miyar masan da ferfesun nan.
Buɗewa tayi ganin miyar tayine ta sauƙe ta maida gefe.
Kana ta kalli Ummi tace.
“Ummi je kiyi salla la’asar tayi, in kin dawo sai inje inyi”.
To Ummi tace ta fita tana mamakin saurin aikin Shatu.
Koda taje tayi sallan ta dawo ta sameta tana sauƙe tukunyar ferfesun.
ganin Ummi yasa tace. “Yauwa Ummi komai yayi dai-dai yanzu kaskon tuya zamu daura kinga kullun ya tashi”.
Cikin mamaki Ummi ta kalli Robar da taga har kullun na shirin zubewa.
Ita kuma ɗiba tayi a wata roba kana duk tasa yankekken al’basane a ciki Sannan tasa sugar ta gauraya,
sannan ta matso da kasko biyu,
juyowa tayi ta kalli Saratu tace.
“Yauwa Sara matso. Ke ki rinƙa yi kina sawa a wannan babban kulan in ya cika kisa a wannan shima.
Ummi ke kuma kisa mana namu anan suyanki mukeson ci”.
Murmushi Ummi tayi kana tace.
“To jekiyi salla”.
To tace kana ta fita.
Ita kuma Ummi ta juya ta kalli Sara tare da cewa.
“Kema kije kiyi salla”.
Cikin ci gaba da aikinta tace.
“Ai nima nayi”.
“To shike nan”. Ummi tace kana sukaci gaba da tuyan.

A falo ta haɗu da Hibba da Jamil, sai dariya yakeyi cikin dariyar yace.
“Yauwa Aunty Shatu dama idonki nazo in gani, dan ga Hibba kam ta kusa kasawa”.
Murmushi tayi dan bata da sauran ƙarfin yin dariya.
Cikin ɗan fito da idanunta da suka ɗan faɗa tace.
“Gani ras dani”.
Dariyar ƙeta mai cike da alamun yunwa da ƙishi yayi tare da cewa.
“Inafa ras kalli yadda idonki ya fito kamar kinyi azumi goma”.
Murmushi tayi kana tace.
“Um bari inje inyi salla”.
Sai ta kuma kalli Hibba dake lankwabe tace.
“Sannu Hibba kwanta ki huta”.
Jalal da yanzu ya shigone ya ɗan taɓe baki tare da cewa.
“To me tayi da zata huta tunda fa gari ya waya in anga ta tashi dai yin salla ne, tun tuni birgima take a tayis wai sanyi take nema”.
Dariya sukayi mata baki ɗayansu,
Ita dai Shatu ciki ta wuce.
Salla tayi kana ta fito. Koda tazo kitchen ta samu Hibba na suya musu Arish ɗin, tayi mamaki.
Cikin wasa tace.
“Kawo in karɓeki jeki kwanta”.
Cikin sanyi tace.
“Ai Hamma Jabeer ne yace min in ina aiki bazanji wuya ba, zanfi ganin lokaci ya gudu”.
Dariya sukayi mata kana kowa yaci gaba da aikinshi.
Ita Shatu miyar sahur na asuba ta ɗaura musu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button