GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ita kuwa Aysha zaman jiran ya ida addu’o’in sa ne ya fassara mata surar take jira.
Kallonta ya ɗanyi, kana yace.
“Tashi muyi nafila”.
A hankali tace.
“Nayi ai”.
Gyara tsayuwarsa yayi ba tare da ya kalleta ba yace.
“Na sani ai ƙarawa zamuyi ko bakya son ƙarin lada”.
Kai ta jujjuya tare da cewa.
“Ina so mana”.
“To taso muyi ba yawa raka’a biyu ne”.
Yace yana kallonta.
To tace kana ta miƙa tsaye.

Nafilan sukayi raka’a biyu kamar yadda yace ɗin kana sukayi zaman tahiya.
Bayan sun sallame ne, duk suka gyara zamansu.
Tasbihi ya ɗanyi kana a hankali yace.
“Zo nan”.
Ya faɗi yana nuna mata gabanshi.
A hankali ta ɗan musukata sai dai bata iso inda ya nuna matan ba.
Kanshi ya kauda kana ya juyo ya fuskanceta da kyau.
da sauri ta ɗan sunkuyar da kanta.
ƙara matsota yayi har guiwowinshi na gogan nata.
Da sauri yasa hannunsa ya riƙe nata ganin ta yunƙura zata ɗanyi baya.
Cikin juya fuska ba wasa kuma ba tsanani yace.
“Tsaya mana”.
Ido kawai ta zuba mishi.
Shi kuwa a hankali ya ware tafin hannunsa na dama ya buɗa yatsunshi kana ya kife tafin hannun kan goshinta.
“Uhhhmmm”. Haka ta fidda wani ɗan sauti na tsoron jin yadda tafin hannunshi ya sauƙa a goshinta.
Sama kaɗan yayi da hannun ya zama rabi na kanta rabi na kan goshinta.
Babbar yatsarshi na kan babbar jijiyar kanta na gefen dama.
Doguwar yatsarsa ta tsakiya tana kan jijiyar kanta na gefen hagu.
Cikin ɗan ɗaga sauti kaɗan ya fara karanto addu’ar marabtar amarya ga ango.
Addu’ar Neman Zaman lfy ce.
“Allahumma inni As’aluka min khairi ha wa khaira ma jabaltaha alaihi, wa a uuzu bika min sharri ha wa sharra ma jabaltaha alaihi”.
Ma’ana
“Ya Allah ina roƙon ka Al’khairin ta, da Al’khairin da ka Halicce ta akan shi.
Kuma ina neman tsarin ka daga Sharrin ta, da kuma sharrin da ka Halicce ta da shi ko akan shi.
Amfanin Addu’ar
Idan ka yi ta.
Allah zai cike Soyayyar da ke tsakanin ku 100%. Zai tsare Shaiɗanu da Miyagu daga cutar da zaman Auren ka da ita da sauran su…

Wani irin nauyinshi mai yawa ta rufeta.
Shi kuwa a hankali ya janye tafin hannunsa daga kanta, kana a hankali yaja ba ya koma mazauninsa.
Jingina kansa yayi da jikin gado kana murya can ƙasa yace.
“Ɗauko min abinci a can falo Ummi ta ajiyeshi bisa Dinning table ki kawo min shi nan ɗinan!”.
Da sauri ta miƙe kamar dama umarnisa take jira.

Ƙofar fita ta nufa. A hankali ya bita da idanu har ta ɓacewa ganinsa.

Meda idon yayi ya lumshesu.
Yana mai jin zuciyarsa na bugawa.
“Meyasa lokaci ɗaya rana ɗaya, zuciyashi da jikisa suka amince da ta zamo sutura a gareshi, shima ya zama sutura a gareta kamar yadda Allah maɗaukakin sarki yace.
Ya akayi yakejin yau zai iya haɗa shimfiɗa da ita, meyasa ya yanke wannan hukuncin na tabbatar da ita matsayin matarshi ta sunna suturarsa?”.
Wani dogon numfashi mai sanyi yaja ya fesar, yana mai jin yadda iska mai sanyi ke ratsa fatarshi.

Ita kuwa Aysha a tray’n ta ɗauka ta nufi falonshi da nufin tana ajiye mishi zata juyo.

Tana shiga ta sameshi yadda barshi haka ta sameshi.
Zaune,
ta jiye tray’n a hankali, shi kuwa tuni ya miƙe tsaye.
bakin ƙofar ya nufa, tsayawa tayi ta jira ya fita kafin ta fita.

Can babban falon ya nufa, tana biye dashi a baya.
Ƙofar falon ya rufe, tare da addu’a kamar kullum.
Ya juyo kenan sai ya ganta tana ƙoƙarin shiga falonta,
Yafitota yayi da hannunsa tare da cewa.
“Zo”. Yayi mgnar a hankali.
juyowa tayi ta nufi inda yake a zatonta ko wani abun zai sa tayi mishi.
Tana isa wurin yasa hannunsa a hankali ya kamo nata.
Kana ya juya ya nufi Side ɗinsa bayan ya kashe wutan ko ina.
Ita dai tana biye dashi kamar raƙumi da akala sai tsoronshi dake ƙara tsananta a zuciyarta.

Suna shiga falonshi ma ya meda ƙofar ya rufe, nanne ta kalleshi a hankali tace.
“Zanje in kwanta ne bacci nakeji”.
Kanshi ya gyaɗa mata alamar to.
Wutan ya kashe da komi na wuta kana ya nufi bedroom ɗinsa da ita.
suna shiga ya meda ƙofar ya rufe da key a hankali tace.
“Zan tafi ɗakina”.
jawo hannunta yayi suka iso gaban tray’n kana a ya zaunar da ita shima ya zauna suka sa tray’n a tsakiya cikin hikima da ɗan sakin fuska yace.
“Nawa kika sayi ɗakin ya zama naki?”.
Cikin kwaɓe fuska tace.
“Ban saya ba”.
Kanshi ya ɗan sunkuyar kana yace.
“Shine kuma kike cewa ɗakinki.
Rau-rau tayi da ida nunta. Tuni sun ciko da ruwa.
Ganin haka ne yasashi ɗan matsowa ta inda take kana a hankali yasa hannunshin ya jaw…!

Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300 babbancinsu a yawan posting ne. In special Group kikeso kiyi min TRANSFER ɗin 1k ɗin a asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, in kin tura sai kiyi screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta whatsapp 09097853276. Kuma yan 300 ta nan accutan ɗin zaku turo, ku turo shaidar biyanku ta whatsapp. In baki da halin turawa ta Account ki sayi katin Mtn na ɗari uku ki copy numbers ɗin ki turo min ta whatsApp 09097853276 bana son VTU ko transfer’n kati, in kinyi ba ruwana.
Yan special Group Please bandaku a kati mtn ɗin ma. Ku ku bada a POS a tura.

                       By
      *GARKUWAR FULANI*

[3/17, 9:03 PM] +234 806 559 0880: Ya jawo hannunta na hagu ya haɗe da nashi hannun.
Kana a hankali yace.
“Kici abinci sai muje in rakaki, tunda bakya tsoron kwana ke ɗaya ko?”.
Da sauri tace.
“Eh bana tsoro”.
Foodflaks ɗin ya buɗe tare da cewa.
“To kici abinci tukun, ba kyau kwanci da yunwa”.
A hankali tace.
“Na ƙoshi ɗazu da muka gama girki naci abinci”.
Plate ya ɗauka.
Kana ya buɗe kular,
yasa Fork ya soko zabuwar ya ɗaura kan plate ɗin kana yace.
“Me kuka dafa?”.

“Tuwo ne”. Ta bashi amsa a gajarce da kuma yanayin tsoronshi.

“Miyar me”. Yace mata yana mai kallon ƙwayar idanunta.

“Miyar kase ne”.
Kanshi ya ɗan juyo ya kalleta kana yace.
“Uhumm shine ko ki kawo min”.
Shiru tayi, shi kuwa ƙaramar kular ya buɗe.
romon ya ɗan sa a gefen plate ɗin.
Kana yace.
“Uhumm duk wanda yaci shi ɗaya shi ɗaya zai mutu ai”.
Ya ƙare mgnar yana murmushin gefen baki”.
Still shiru tayi.
shi kuwa, cikin son sama mata nitsuwa dan ya lura ta firgita da shi.
A nitse yace.
“Rowa ba kyau”.
Cikin sanyi tace.
“Ai nasa maka, yanzuma na sameshi a can, in kawo maka in kana so?”.
Kanshi ya jujjuya kana yace.
“A a, saida na roƙa meyasa tun ɗazu baki kawo min ba”.
Ɗan kallonshi tayi a fakaice kana tace.
“To ai naji kace Ummi ta gasama zabuwa”.
Kai ya jinjina alamun gamsuwa kana yaci gaba dasa Fork yana saɓule kasusuwan zabuwar yana turesu gefe sai tururi da ƙamshi naman yakeyi.
Ruwa kuma har yanzu tsugashi akeyi.
Saida ya gama saɓule sokokin ya zare ƙasusuwan ya medasu gefe, kana ya tura mata plate ɗin gabanta, sannan yace.
“To muci, sai ki tafi tunda bakya tsoron Jahan yazo ya sameki a ɗakinki ke ɗaya.”
Cikin sanyi tace na ƙoshi”.
Kanshi ya ɗan kauda kana, ya fara cin naman da sauri-sauri kuma yana taunan da ɗan ƙarfi kamar dai yadda ko yaushe inda fushi a zuciyarsa haka yake komai.
Ta fuskar ibadace kawai fushinsa baya tasiri bare ya sashi yin abu da gaggawa ko da karfi.
Duk fushin da yake ciki, in dai ya fuskanci abu na ibada ne to a take nitsuwarsa ke dawowa.

Kaɗan yaci kana ya tsiyayi sassanyan madara da zumar nan, cikin kofi, ya kafa kai bai ajiye ba saida ya shanye.
Kana ya sake tura mata plate ɗin gabanta, sannan ya cika mata kofin da madarar zuma, kana ya miƙe tsaye tare da cewa.
“Zan shiga wonka in kin cinye kafin in fito to na miki al’ƙawarin zan buɗe miki ƙofar ki koma ɗakin naki, in kuma kinƙi cinyewa to dole a nan zaki kwana”.
Yana faɗin haka ya shiga bathroom.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button