GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Uhummm wani kayan sai amale, wani littafin yafi ƙarfin a baka lbri ka iya haƙura baka karantaba. GARKUWA YA WUCE ZATON MAI ZATO

                         By
              *GARKUWAR FULANI*

????????????????????????????????????????????

   ????️????????????????????????????

             *GARKUWA*

                    PAGE 5

                            NA
              *AYSHA ALIYU GARKUWA*

????????????️????????????????????????????

LITTAFIN GARKUWA na kuɗine ga masu buƙatar biyan kuɗin samun damar karantawa al’ummar Niger da kewaye ga number da zakuyiwa mgn +22799460151 biya ɗari uku, ko dubunki ɗaya kacal un saki a group. Gareku mutanena mutanen ƙasata in kina buƙatar GARKUWA ga hankaɗo min ɗari uku kacal! ko dubu ɗaya rak! Ta asusuna na Jaiz bank, 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyan ki ta number ta 09097853276. Mutanen Ayyah SP Group bana son KATI. Kuma al’ummar 300 in ba dole ba yaseen bana son KATI, to amman in babu yadda zakiyi, nasan akwai irina ƴan ƙauye, ba POS. Kuma kuna son karantawa, to hankaɗo katin mtn ɗinki na darinki uku kisha karatu. Allah ya nuna mana ƙarshensa lfy kamar yadda ya nuna mana forkonsa lfy. ALLAH ya bamu haƙurin zama da juna

Fans 1&2 sarakan surutu, Ina gaidaku ina ji daku har cikin ƙoƙon raina. SP Group, inai muku jinjina dubu-dubu.Fans 3 Allah ya rayamu ku cika maƙil. Group ɗin kurame kuma ina sane duku ina kuma jin daɗin nitsuwarku ba surutu. i love all my fan's irin lodi-lodin nan mafa

Gyaran amare uwar gidaye masu jego da masu tada komaɗa da sabunta dararen satin forko na amarci. Ku garzayo gani gareku da tsaraba kamarsu, tsumin Tsartai, sa buzu kuwa, garin babambaɗe, garin maɗi mai maɗemaɗin ni'imomi, bunbar ke ɗaya, gumbar Mali mai taken kolli mai sheƙi sai dai gsky ita tanada tsada, gumbar Uku csrmazaƙoi, gumbar haɗin inabi dabino kwakwa riɗi. Akwai haɗin ilan waddi, duk ba fula tani in yaji ilan waddi uhumm, akwai garin Belɗam yel, akwai tsumin ta baje, akwai kwanon ƙasaitacciyar mace, akwai kirɓeɓɓen tsumin domin mutanen nesa, akwai mgnin sanyi Infection, akwai butar sirri mai. abubuwan dai da yawa, gani ya kori ji, in kina buƙata kiyi min mgn ta wannan number 09097853276 kada ki kira dan ban fiye daga kiraba, gwara kimin mgn ta whatsapp in kinga bana kusa Turo min text message ta in-box

A hankali ya ɗan ɗago ƙwayan idanunshi ya kalleta.
Kanta a sunkuye hannunta biyu duka na kan mararta cikin wani, irin yanayi take wanda yake nuni da tana cikin wahala.
A hankali ya maimaita sunan cikin zuciyarshi.
“AYSHA ALIYU GARKUWA! To GARKUWAN ina? GARKUWAN meye?.”
A fili kuma kauda idonshi yayi daga kanta ya maida idanunshi kan tarin foldan dake gabanshi, wanda sunanta ke rubuce akan na samanshi yaja da yatsu biyu.

Shafin forko ya buɗe a folder kana, yasa hannu cikin wani ɗan abu mai kama da kofi wanda yake cike da biro masu kyau da tsadar gaske.

Tsiraran idanunshi ya lumshe sabida wani irin bugu da yakeji zuciyarshi nayi tun sanda ya hango yarinyar har zuwa yanzun nan da take gabanshi a zaune.
Rubuce-rubuce yayi a ciki irin nasu na Doctors masu kama da tafiyar wahainiya.
Kanshi ya kuma ɗagowa ya kalleta a fizge da gefen idonshi,
sunkuyar da kanshi yayi tare da cewa.
“Meke damunki?”.
Cikin shessheƙan wahala da son danne kukan da ke son kabce mata tace.
“Marata, da bayana”.
Kai ya ɗan jujjuya tare da kallon shekarunta dake rubuce a cikin folder din,
Yar shekara ashirin kuma da ƙorafin ciwon baya, cikin dakekken sauti yace.
“Yaushe ya fara miki ciwo?”.
Hannu tasa ta cikin niƙabin da yayiwa fuskarta ƙawanya ta share hwayenta a hankali tace.
“Shekara uku da suka wuce”.

“Meyasa bakije asibitiba tun lokacin?”. Ya tambayeta a daƙile.

“Ina zuwa asibiti duk sanda ya tashi”.

“Kamar yaushe da yaushe yake tashi?”. Ya jefo mata tambayar kamar yadda zuciyarshi ke harbawa da ƙarfin tsiya da kuma sauri-sauri,
Kai ta sunkuyar tare da cewa.
“Duk ƙarshen wata daga 21 zuwa 25”. Shiru yayi kamar bai jitaba sai wasu rubuce-rubucen ya kumayi.
Saida ya gama sannan ya tura mata folder ɗin gabanta.
Jikinta na rawa tasa hannu ta ɗauki folder ɗin, ta yunƙura zata tashine, ya basu damar samun kusanci da juna,
da sauri ya rumtse idanunshi sabida wani irin azabebben bugu da zuciyarshi keyi tamkar zaiyi tsalle ya faɗo woje,
cikin zuciyarshi yake maimaita.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun.”
A hankali ya buɗe kyawar kyawan idanunshi jin bugun zuciyarshin ya fara yin ƙasa-ƙasa, ido ya zubawa mata ganin ta juya tana tafiya,
wani abin al’ajabin a gareshi shine duk taku ɗaya da zatayi tana nesanta dashi sai yaji zuciyarshi na tsinkewa yana bada wani mugun bugun ras-ras, yayinda bugun tsinkewanta kuwa yaketa dai-dai-ta,
Cikin mamaki ya sunkiyar da kanshi yana kallon yadda takeyin taku, tana riƙe da mararta, taje gab bakin fofar fitane,
Taji wani irin murɗa da kartan da mararta ya farane yasa ta sakin wani sauti mai cike da wuya.
“Wayyoooooooo Allah na, Wayyo Ummeyna cikina”.
Da sauri nurse ɗin nan yayi kanta tare da cewa.
“Isah Allah rena joɗu”.
Ya ƙarishe mgnar da nuna mata kujerun farin ƙarfe dake gab da bakin ƙofar.
Bata da zaɓin daya wuce ta zauna ɗin, domin gaba ɗaya ƙafafuwan ta rawa sukeyi alamun bazasu iya ɗaukar nauyinta ba ga duhun daya rufe mata ido.
Sunkuyowa Nos ɗin yayi ya amshi folder kana yace.
“Zauna bari inje Pharmacy in amso miki magungunan da alluran sai ayi miki”.
Kai kawai ta iya gyaɗa mishi tare da bashi.

Har ya fita sai kuma ya dawo yace.
“Ok sir”. Jin Sheykh Jabeer yace mishi ya turo ta gaba
Da sauri ya fita.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, tasbihinshi yaketayi da yankan yatsunshi yake ƙidayar, sabida, suma yatsun su kasance cikin bautar Allah shiyasa yake ƙidayar amman ba don wai yasan adadin salati da hailala da istigifarin da yakeyiba, wannan ubangijine kawai masanin adadinsu.

Bayan fitar Nos ɗin da kamar 1 minute wata,
Kekyawar budurwa ta shigo, cikin yauƙi da ƙasaita, sai wani irin masifeffen ƙamshin da take zubawa.

Ƙarasowa tayi gaban table ɗin nashi ta zauna,
cikin yauƙi da korkosa tace.
“Barka da rana Al’ Sheykh”.
Ko inda take bai ɗaga ido ya kallaba, ya lura ya gane akwai wani abu tattere da yarinyar, dan mafi akasarin ranaku sai tazo, wai bata da lfy, kuma takan zo da ciwuka mabanbanta ne.
Sanin ba musulma bace yasashi ƙara tsuke fuskarsa tamkar zatayi aman wuta, a zafafe yace.
“Name”. Cikin yauƙi da son isar da aikin da aka bata tasa hannu ta jawo foldan ta dake sama tura mishi gabanshi tayi,
Cikin harshen hausa da tasan bai fiye son English language ba a rayuwarshi a hankali tace.
“Breast ɗina kemin ciwo, har bana iya sa bra.”
Sai kuma tayi ƙasa da mayafinta dake jikinta, hannu tasa kan zip ɗin gaban rigarta tana ƙoƙarin zugeshi ƙasa tare da cewa.
“Kalli Nipples ɗin sun….
Cikin tsananin firgita da tsoro, ta miƙe da azaban ƙarfi, jin yadda yasa hannunshi ya bugi table ɗin da azaban ƙarfi wani irin gigitaccen tsawa mai firgitarwa ya daka mata tare da cewa.
“Tashi, daga gabana”.
Karkar jikinta ke tsuma sabida kwarjinshi da tsoronshi sun daki zuciyarta da take cike da fajirci dama dan bata kallon fuskarshi ne ta iya faɗin waɗannan kalaman ma.
Dai-dai lokacin kuma, Nos ɗin nan ya shigo,
ganin yadda AYSHA ta gigice taketa karkarwa, alamun tana son ta miƙe kuma ta kasa tashi.

Shi kuwa Sheykh foldan ɗin Rabeca ya jawo wani rubutu yayi saman foldan ɗin kana ya tura matashi gabanta cikin zafi da tsauri ya nunata mata hanyar fita tare da cewa.
“Fice min daga Office daga yau in kina buƙatar ganin Dr kije gun Dr Ute, shi zakiyiwa duk sakarcinku na al’jihun baya. Ba niba, sannan daga nan ki wuce Zaria kije asibitin Shika domin ina zaton breast cancer kike dashi”.
Da sauri tasa hannu ta ɗauki foldan ɗin, gaba ɗaya jikinta na rawa, juyawa tayi ta fice tare da yin magana can ƙasa yadda bazai jitaba tace.
“Allah ya sauwaƙa Ni bani da breast cancer, mugun bakin kawai.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button