GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Wasu irin hawa masu ƙunu yaji suna tsatstsafo mishi, cikin jijiyoyin kekyawan idanunshi,
sabida ganin yadda Ya Jafar ɗinshi ke karatu yana, kuka ya za’ayi ya sama mushi farin ciki a rayuwarsa ta ina, zai san me ke cin zuciyar ɗan uwan nashi.
Jin yadda ransa ke ƙuna da tafasa ne, yasashi. Komawa ya jingina bayanshi da jikin kujer, kamar yadda Jafar yake mahaddacin haka shima settin kab tana kanshi,
Ido ya lumshe tare da yin bisimilla kana ya fara karu inda ya ɗauko daga forkon suratul. Noor ya farayin ƙasa.

Saida sukayi awa ɗaya cur kana,
Suka fara Azkar, wanda sai da sukayi 23 minutes suna, jero addu’o’in cikin harshen dake nuni da cikekkiyar jimla ta larabci da lugga.
Koda suka shafa, sai ya ɗan kalli ɗan uwanshi dake riƙe da hannunshi gam.
Ya lura Ya Jafar na tsoron kada ya kuma tafiya ya barshine, yasan duk sanda yayi doguwar tafiya ya dawo, haka yake liƙe mishi.
Hannunshi yasa, ya share mishi hawayenshi kana,
ya miƙa tare da jawo hannunshi,
yasani yanzu lokacin yin baccinsa ne,
Side ɗinsu, ya nufa dashi, ta wata ƴar siririyar hanyar dake tsakanin sashukansu.

A babban falon suka samu Juwairiyya.
Tana ganinsu, ta miƙe da sauri, fuska ɗauke da murmushi kana ido na tsatsafo da hawaye tace.
“Barka da dawowa, Sheykh, Alhamdulillah zamu samu nitsuwar Ya Jafar”.
Kanshi ya sunkuyar sabida bai son ganin hawayenta,
Hannunshi ɗaya yasa yana shafa, kam Mimi data ruggumeshi ta ƙafafunshi,
cikin murmushi ta nitsuwa yace.
“Mimina anyi sallako?”.
Cikin sauri ta gyaɗa kanta alamar eh,
Shi kuwa kanta ya kuma shafawa tare da cewa.
“Kinyiwa Ya Jafar ɗina Addu’o’in Allah ya bashi lfy ko?”.
Kanta ta kuma gyaɗawa tare da cewa.
“Eh nayi mishi”.
A fakaice ya ɗan kalli Juwairiyya dake rugume da yarsu karamar, cikin sanyi yace.
“Kukan bashi da wani amfani, muyi ta mishi addu’a, in sha Allah dukkan tsanani yana tare da sauƙi.
Ina roƙon Ubangijina mahaliccina a cikin dukkan Ayyukana, daya aramin rai da lfy, kada ya ɗauki raina ko na ɗaya daga, cikinmu, har sai ya nuna mana lfyar ya Jafar, ya faɗa mana abinda ya maidashi haka a dare ɗaya, nasani shine ɗaya rak yasan meya faru, a dare mai duhu da muni na rayuwarmu”.
Cikin sanyi tasa tafin hannunta ta share hawayenta.
Shi kuwa Sheykh, wucewa yayi da Ya Jafar ɗin har cikin ɗakinshi,
bisa gado ya zaunar dashi, kana yacewa Juwairiyya dake biye dasu a baya.
“Yasha mgninshi ne?”.
Miƙo mishi gorar ruwa da magungunan tayi tare da cewa.
“Yaƙi sha, dan daren jiya kwana yayi, baiyi bacciba,
Jalal nan abin tausayi, ko nanda can bai isa ya fitaba,
sai ya bishi,
Kullum sai Jalal yayi kuka”.
Wasu tafasassun hawaye ne suka cika masa ido,
A duniya shi baya son yaga ko yaji na miji na kuka, domin shi ya sani, duk abinda kaga yasa na miji kuka to abun ya tsananta musamman maza irin Jalal yasan ba ƙaramin raunine zaisa Jalal zubda hawayeba.
Shiyasa, shi kukan mace bai taɓa damunshi ba a zuciyarshi, domin mutane sunce in kaga mace na kuka to kayi dariya kafin ka tambayi meya sata kukan. In kuma kaga namiji na kuka to kaima ka fara kukan kafin ka tambayeshi meya sashi kuka.
Shiyasa shi kukan mace, bai shiga ranshi, sabida yanaga mata sun iya kukan munafurci da kukan gulma dana ha’inci da yaudara,
shiyasa in yaga mace na kuka haushinta yakeji a ransa.

Maganin ya bashi sannan ya kontar dashi kafin ya wuce, ya koma sashinsa.

Yana shiga, falon, ya samu, Haroon ma zaune, shida Jakadiyarsu,
tana ganinshi ta faɗaɗa fara’arta cikin kula da so mai zurfi tace.
“Farin gani, Garkuwa, Sheykh, Limamin Masallacin Moddibo Joɗa Jikan sarki mai hatimin sarauta.”
Gefen Haroon ya zauna tare da rumtse idonshi cikin nitsuwarshi yace.
“Ummi ki bari mana, babu wani sarkifa sai Allah, Ummi nace ki dena min irin waɗannan zantukan masu sa kan ɗan adam girma”.
Murmushi mai cike da tarin so, sabida ita dai jinshi take tamkar ɗan da raina a cikinta ta kuma haifeshi,
Koda yake hakan baya rasa nasaba, da cewar itace jakadiya gareshi tun randa aka haishi bacci kawai ke haɗashi da Mamanshi. Sai dai takanzo inda suke su sashi a tsakiya sunai mishi wasa da kallo mai cike daso.”
Ganin tayi kasake tana kallonshi ne ya sashi ɗan gyara zama, cikin girmamawa yace.
“Ina kwana Ummi, ya su Jalal?”.
Murmushi ta kumayi tare da cewa.
“Lfy lau Alhamdulillah, Jalal ya zama mazaunin gida, tunda ka tafi sabida, duk inda yaje , Jafar zai bishi,
sai dai kuma abokanshi masu shigar banza har gida suke biyoshi,
wani sa’in kwana kiɗe-kiɗe da rawa sukeyi a sashinsu, suna shan sigari.
Wasu lokutan dole, Jamil yake gudowa ya bar musu can yazo wurina yake kwana, ko ya shigo nan wurinka”.
Kanshi ya ɗan maida baya, a hankali yace.
“Ummi Jamil da mata?”.
Kai ta ɗan kauda kana a hankali tace.
“Tafiyar bata sauya zaniba, kwanaki uku da suka wuce wata tazo daga, Kano wai ita ƙawarshi ce, kwananta biyu, a sashin Juwairiyya, da Abbanku ya samu lbrine ya korata”.
Cikin sanyi yace.
“Ummi waya gayawa Abba?”.
Kai ta jujjuya tare da cewa.
“Allahu alamu, yadai ji har yace zai kori Jamil ya bar mishi gidanshi, to da yake Jafar yana wojen ne, sai ya riƙe hannun Jamil yayi ta kuka, hakane yasa ya barshi, Mamanku kuwa kuka tayi- tayi”.
Wani irin zazzafan numfashi ya fesar kana, ya juyo ya kalli Haroon a hankali ya kuma kalli, Jakadiyarsu, cikin sanyi yace.
“Basaji Ummi suna samin tunani a raina, ga wannan kuma shima ƙato dashi, sai ya ruggumi waya yayi ta chatting ko waya Da waccar yar mitsitsiyar yarinya Jannart ɗin.
Da asuba nayi ta tadashi yafi sau uku baya tashi, sabida bai bacci da wuriba, gashi ko cikekken jam’i bai samuba”.
Ido Haroon ya lumshe tare da cewa.
“Jiya dai ba chatting ko waya da Jannart bane, ya hanani baccin da yasani makara, Ummi ƙarshen darefa muka iso sabida ya sani dole sai mun taho nan.”
Murmushi Ummi tayi kana tace.
“To Haroona ka kiyaye batun tsaida salla kan lokacin ta, kaji ko?.”
Hararan Sheykh yayi tare da cewa.
“To Ummi”.
Ita kuwa Jakadiyarsu cikin muryar kula tace.
“Haroona yaushene bikin naku kam?”.
Kanshi ya ɗan shafa kana yace.
“Uhum Ummi saura watanni bakwai in Allah ya yarda, Ni dai zanyi aure in bar babban tuzurun”.
Bai kulashiba saima tashi yayi ya nufi bedroom.
Ita kuwa Jakadiyarsu cikin yin ƙasa da murya tace.
“Yauwa ya dai-dai ta da Jazrah ko?”.
Baki ya ɗan turo tare da cewa.
“Uhum Ummi gudowafa yayi, kuma wlh in ba dagewa kukayiba, wannan bauɗeɗɗen ɗan naku, ustazu bazaiyi aureba, mutun duk yadda akayi dashi sai ya kauce”.
Kai ta ɗan juya ta kalli ƙofar ɗakin daya shigan,
cikin yin ƙasa da murya tace.
“Uhum ga zahiri ko mgnar aure akayi sai ya bar wurin.”
Haka sukayi ta hira da yake akwai sabo tsakaninta dashi.

A sashin Hajia Mama kuwa, ita da kanta da kuma, Batul suka shiga kitchin sai kuma yardaddun hadimanta mutun biyu.
Breakfast mai kyau suka, haɗawa Sheykh.

Yayinda Aunty Juwairiyya ma ta shiga kitchin da kanta, ta haɗa mishi breakfast.

Jakadiyarsu kuwa da Jamil da Jalal da Affan Haroon suna falon sunata hirarsu.

A tare hadiman Mama dana Juwairiyya suka kawo, abin kari.
Suna fita ba da ɗewa, hadiman Gimbiya Aminatu kakarsu kenan.
Suka shigo suma da abun kari.

Suka jera komai kan babban dinning table dake dinning area’n dake falon.
Bayan sun fitane.

Suna cikin hira, sarƙin ƙofa, ya shigo, ya shaida musu, ga saƙo an kuma kawowa.
Jamil ne ya bada daman a shigo.
Nan ya juya ya fita,
jim kaɗan, aka turo ƙofar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button