GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

A hankali Dottijon yaci gaba da cewa.
“Kanshi akwai wani abu mai girma a tare dashi, yanada manyan baiwowi a jikinshi, sai dai kuma akwai tarin ƙalubale, zai ɗauki nauyi da yawa a kanshi”.
Ya ƙarishe mgnar yana shafa tattausan suman Sheykh.
Shiru sukayi baki ɗayansu Sitti kuwa Hannu tasa bisa haɓar Sheykh tana share masa hawaye, Haroon kuwa Umaymah ya kira tun shigarsu tana jin duk kalaman kakan nasu haka yasa taketa kuka.

Sosai yayi jawabai masu ratsa zuciya kafin daga bisani, ma’aikatan gidan suka shigo suka rinƙa gabatar musu da abubuwan ci da sha a nan suka zauna ana ɗan ciye-ciye da taɓa hira,
Ganin lokacin salla yayine kab kowa ya miƙe dan yin al’wala su tafi harami.

Kamar koda yaushe Sashin Sitti suka wuce wanda yake a gyare, Jannart da Sitti side ɗaya suka shiga.
Haroon da Sheykh kuwa Side ɗaya suka shiga.
Ruwa suka ɗan watsa sannan duk sukayi al’wala suka fito suka kimtsa cikin manyan alkyebbars masu taushi da masifar kyau wanda sabbine dal akazo aka shirya musu a drower’n. Koda suka gama a tare duk mazan suku tafi Harami.

Haka dai rayuwa tai ta gudana a cikin kwanakin nan.

Randa suka cika kwana uku da zuwa a ranar ne Sitti ta samu mahaifinta da ƙaninta a kan batun tana son kafin tabar ƙasar nan ayiwa Sheykh aure, ta kuma bada zaɓin yaran yan uwa wanda suke larabawa, nan take kuma Sheykh Aliyu da kanshi yace ya bawa Sheykh Jabeer auren diyarsa Jazrah…

Rugar Bani Ɓadamaya state.

Yau kusan kwanan Shatu biyar da dawowa hutu, kuma kullum da salon da Ba’ana yake zuwar mata dashi, wannan abu shine abinda yafi tada hankalin Malam Liman Bappa kenan, wanda yana yawan tattauna matsalar da Ardo Bani kamar yadda yanzuma haka suke tare su daddatawa biyar,
Cikin kamala da harshen fillanci Arɗo Bani yayi gyaran murya tare da cewa.
“Koda Hashimu ya rasu, in sha Allahu bazamu zuba ido a aurawa Shatu wannan fasiƙi fajiri mushirkin yaron nanba, Salmanu zai fito zai nemi aurenta,in Allah ya yarda kuma zamu cire batun shaɗi tunda, mun sani cewa, bulalin da Ba’ana yake amfanin dasu wurin shaɗi da manema auren Shatu bulalin sihirine wanda duk wanda ya daka dasu ƙarshe mutuwa yakeyi ko ya haukace, to a karon nan zamuce babu shaɗi domin ai shi shaɗi al’adace ba shariya ba.
Zamu kuma bawa salmanu dakarun tsaro masu bibiyar lamuranshi a sirri dan gudun kada ayi mishi yankan rago kamar yadda akayiwa Hashimu duk da dai bamu da sanin shin Ba’ana ne koko kafuran Ɓachamawa ne”.
Da sauri ɗaya daga cikin dottawan yace.
“Yo ai shima Ba’ana kusan kafurin ne, tunda baya salla kuma matsafine”.
Bappa ne ya nisa tare da jan dogon numfashi mai tsawo sannan yace.
“Bazai yardaba duk yadda za’ayi sai yace dole ayi bulalin Shaɗi, kana kuma muddin akace baza’ayi Shaɗi ba to haƙƙun zai kashe Salmanu kisan da bazamu samu huja ko madafaba”.
Shiru sukayi baki ɗayansu cikin kamala da nitsuwa da rauni Bappa yace.
“Kaɗan kenan daga illar riƙo da Al’adar daba addini ne ya tanadar dashi ba”.
Ardonne yayi gyaran murya cikin sanyi yace.
“Ya Allah ka kawo mana mafita kan wannan bawa naka Ba’ana daya zame mana masifa a rayuwarmu”.
Ɗaya daga cikinsu wanda tunda suka zauna baiyi mgna bane ya gyara zama tare da cewa.
“Gashi shi kamar ibilis yake, ya rigada ya gama dafa kanshi wuƙa ko bindiga basa shigarsa bare banzan abu shi bulalan Shaɗi shiyasa kullum shine da nasara a rayuwarsa”.
Shiru sukayi suna kallon ɗaya daga cikinsu wanda ya kasance malamin da suke sawa yana bincikar musu jikin Ba’ana wato Chubaɗo yana cewa.
“Akwai bulalin da zasu shigeshi su kuma karya duk wasu manyan sirrukan dake jikinshi, ta kuma sashi yayi kuka,cur-cur da hawayenshi, to amman bazasu taɓa samuwaba bamu da hanya ko damar samunsu, domin bulaline da a ƙalla sun shekara ɗari biyu a murde kuma suna cikin tsumin ma’jiya mai cikar tarihi da girma bulaline da tsawon shekara ɗari da ashirin da biyar kenan rabon da ayi amfani dasu, kuma an killacesu, killacewa mai tsauri, shi kanshi Ba’ana yana neman bulalin ruwa a jillo domin babban dodon tsafin Bonon ya sanar mishi saida bulalin zai samu nasarar da yake so, to amman bai san bulalin ina bane baisan a ina sukeba bai kuma san ta ina yake nemansuba an dai bashi yaƙini a hannun Fulani yake wannan dalilin ne yasa ya baza jakadunshi duk ƙasar da takeda Fulani.”
Da sauri Suka zuba mushi idanu baki ɗayansu cikin zaƙuwa sukace.
“To Chuɓaɗo kai kasan inda bulalin suke e?”.
Kanshi ya jinjina musu tare dayin ƙasa da murya yace.
“Eh na sani”.
Cikin sauri sukace.
“Bulalin inane a wacce ƙasar suke?”.
Cikin tsoro yace.
“Bazan fadaba bazaiyiwu in faɗaba”.
Magiya suka fara yi mishi amman fir yaƙi yace mutanen jikinshi sun hanashi faɗa, dole haka suka haƙura suka tashi daga taron ganin dare ya raba tsakiya kowa ya koma gidanshi.

Washe gari da Asuban fari Rasuwar Chubaɗo ya zagaya garin Rugar Bani wanda akayi hira dashi lfy lau kawai washe gari aka riski ya rasu da alamun kuma ɗaure mishi wuya akayi ya rasu har lahira.
Wannan rasuwa ya jijjiga zuƙatan dottawan nan huɗu da suka rage Arɗo Yabani da Bappa, da kuma Alhaji Ja’eh da kuma Malam Umaru.
Sun shiga jimami mai yawa.
A haka dai akayi mishi sutura aka binneshi akayi zaman makoki na tsawon kwana uku, randa akayi sadan uku duk hankali mutane huɗun nan ya ɗan konta ganin ba’a sake kashe wani ba a cikinsu.

Yau tun da yamma Ba’ana ya matsa aka kira mishi Shatu wacce dolece tasa taje, inda yake har rugar shanunsu bata damuba sanin bai taɓa koda yunƙurin cewa zai taɓa koda ƴar yatsartace,
Cikin sanyin jiki ta sallami aminiyarta Bintu ƴar gidan malam Umaru, sannan ta tafi bakin rugagen.

Zaune ta sameshi cikin ƴar bukkarshi da yayi a cikin tsakiyar turken garken nasu,
A hankali ta ƙaraso wurin ta sunkuya zata zauna ne a saman farin yashin dake wurin yayi maza yace.
“Mata a ƙasa kuma? A a gskiya kada ki zauna a ƙasa.
Ga buzuna zauna a kai”.
Kanta kawai ta jinjina shi kuwa shimfiɗa mata buzun yayi, a hankali ta zauna tana fuskantar cikin ƴar bukkar da yake zaune a cikinta ɗin.
Shima gyara zama yayi tare da fuskantarta,
Kwaryar dake gabanshi ta zubawa ido, shi kuwa. Cikin yin murmushi ya sa hannunshi yana gauraye magungunan dake ciki tare da cewa.
“Matar dafaki nakeso inyi, irin dafar da muddin mutun ya tuna zai miki sihiri, misali ya miƙa hannu zai amshi mgnanin da zai samiki to zai kuturce in kuma baki ya buɗe zaiyi mgna kan a miki sihiri to zai kuramce”.
Cikin sanyi ta kwaɓe fuska tare da cewa.
“To ni kuma wa zaimin sihiri a duniya wayama damu dani?”.
Murmushi mai kama da dariya yayi kana yace.
“In an nemi mijinki ba’a sameshiba dole kanki za’a dawo shiyasa nake shiryaki sabida kar Ni in an jefeni bai sameniba ya sauƙa kanki”.
Ya ƙarishe mgnar da miƙo mata ɗan ƙaramin korya yace.
“Ingo ki fara shan wannan”.
Kai ta gyaɗa ganin madarar shanuce da aka tatsa da ɗuminta.
Cikin takaicin halinsa tace.
“Me wannan kuma?”. dariya yayi tare da cewa.
“Baki da yarda ki yarda dani wata rana zaki tuna nayi miki gata, wlh bazan taɓa cutar da keba mata, kisha madarace da zuma nasan kinaso”.
Cikin sanyi tace.
“Sai dai in na koma gida zansha”.
Murmushi yayi tare da zuba mata ido kana a hankali yace.
“Fulaku ko? Nasanku fulanin da kunya wato irin bazakici abu a gabana ba, to ai kafin ki koma gida zaiyi sanyi, bari in tafi can bayan bishiya in barki ke ɗaya kisha abunki da ɗuminshi”.
Ido kawai ta zuba mishi domin tabbas badon halin banza da Ya Ba’ana yake dashiba ya cancanci ta soshi tabbas tasan ko ba yayi mata alherin da bazata taɓa mancewa ba a rayuwarta.
Ko komai nashi na duniya mara kyau ne to soyayyarta kekkyawace a zuciyarshi ya sota tun tana yar mitsitsiyarta kuma bai taɓa yunƙurin cutar da itaba ya kuma yi mata halacci.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Mata nayi miki kyau ne?”.
Kanta ta gyaɗa mishi alamar eh, cikin jin daɗi ya juya ya tafi, can nesa ya ɓuya, ita kuwa a hankali ta fara shan madarar nonon da yaji zuma mai daɗi, kasan cewar nonon ɗan kaɗanne a take ta shanye.
Saida ta goge bakinta tace mishi.
“Na shanye kazo”. Da sauri ya fito ya dawo gareta cikin bukkar ya koma ya zauna wani nonon ya ɗibo ya miƙa mata amsa tayi cikin sanyi yace.
“Me kika gani a ciki?”.
Murmushi ta ɗanyi tare da cewa.
“Nono fari ƙal mana”.
Amsar ƙoryar yayi ya koma cikin bukkar dashi, jin kaɗan ya kuma fitowa ya miƙa mata tare da cewa.
“Me kika gani?”. Tura baki tayi tace.
“Farin nono mana”. Kanshi ya jinjina tare da cewa.
“Da kyau, yanzu kiyi kamar zakisha ki gani”.
Ido ta zuba mishi tare da cewa.
“Sha kuma?”.
Kai ya jijina mata kana yace.
“Eh amman ba shan zakiyiba kiyi dai kamar zaki kaishi bakinki da niyar sha zakiga wani abu”.
Jim kaɗan tayi jin yana ce mata sha mana, yasa ta ɗan ɗago kwaryar ta nufi bakinda kamar zata sha.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button