GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ruggume ta yayi tare da lumshe idonsa sabida, wani irin fitinenne zazzaɓi mai masifar zafi da suka ƙasusuwan jikin daya rufeshi a take a lokacin ɗaya gaba ɗaya jikinsa karkarwa ya fara.
har tanajin hakan, so yake ya tashi da ita a jikinsa ya nufi Bathroom Amman ya kasa sabida abin sai ƙaruwa yakeyi, ji yakeyi tamkar kansa zai rabe gida biyu.
Cikin rawan jiki ya jawo blanket ɗin ya rufesu da kyau.
sama take jinshi yana sambatu irin na marasa lfy dake jin azabar ciwo da kuma raki.
“Mamey! Hahhhhh Mamey kaina, Mamey kaina zai fashe Mamey jikina zazzaɓi Mammeyyyyy”.
Ya ƙare kiran kamar zaiyi kuka.
Itama kukan takeyi gashi taji shima kukan yakeyi da samɓatun da batasan na menene ba.

Shi kuwa Sheykh wasu irin abubuwa yakeji suna tafiya cikin jikinshi suna haurawa saman tamkar dafin…!

Littafin GARKUWA na kuɗine in kinason ki karanta ba tare da haƙki ba ga number ta 09097853276 special Group 1k ne shi anfi yawan posting ta Account ɗina zaki turo 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa sai kiyi screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta whatsapp 09097853276. Normal group Kuma 300 ne, kema ta ac no ɗin zaku turo, in ba halin biya ta ac kuma ki sayi katin Mtn na ɗari uku ki copy numbers ɗin katin ki turo min ta whatsapp 09097853276, kada kiyi min VTU ko transfer’n kati bana so.

                          By
             *GARKUWAR FULANI*

[3/18, 12:40 AM] +234 806 559 0880: Kamar dafin maciji, gaba ɗaya tsikar jikinshi ta fara mimmiƙewa tsaye.
Yanajin wasu abubuwa na bin dukkanin sasan jikinsa gaba ɗaya.
Matseta yayi gam-gam a jikinshi tare da jawo blanket ya rufesu rib, cikin rawan murya mai baiyana yanayin wahalar zazzafan zazzaɓi da ya rufeshi da yake ji yake cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani’imanwakil. Mamey, Abba, Jadda, Lamiɗo, Umaymah Sitti Ummi.”
Sai kuma ya kuma ci gaba da Addu’o’in.

Cikin abinda bai gaza 2 minute ba yaji abubuwan da yakeji suna sauƙa ƙasa a madadin sama da suke ta haurawa, duk inda yakejin suka da sari sai ya farajin sanyi mai ƙarfi yana ratsashi ciwon na gushewa kasala mai mai tsanani tana rufeshi.
Lakaci ɗaya yaji jikinsa na sakewa yana mutuwa ciwon na gushe. Al’farmar Annabi da al’ƙur’ani kenan, sabida dama addu’a’u saiful muminin.

Luƙus ya kwantar da kanshi, kana hannayenshi dake bisa bayanta suka sake sukayi nauyi.

Karkarwan da jikinsa keyi ya bari a take, sai wani masha’hurin zazzaɓi mai zafi ya mishi rabkar ƙarfi.

Ita kuwa Aysha hawaye taketa kwaranyarwa.
Tare da Shessheƙan kuka mai cike da rauni da wahala da raɗaɗin ciwon da ko wacce diya mace ke riska yayin rabuwa da tantani wato budurci.

A haka tana kukan baccin wuya ya saceta.
Ko a baccen shessheƙan kuka takeyi tare da wasu surutai na magayi.

A hankali ya juya kwayar idanunsa dake lumshe wanda ko buɗe su ya gaza, muryarta yakeji a hankali tana cewa.
“Yah Sheykhhhh na tuba ka barni haka zafi.
Ummey zafi,
Innayi Yah Sheykh yaji min ciwo, Yeyyeh ciwo”.
Duk da yanayi da yake ciki.
Bai hanashi tafiya duniyar nazartan sunayen da take kira tana kukan wuya haɗida shogoɓa ba.
Tabbas akwai ababen dake sarƙafe a kan Aysha.

A haka suke kwance cikin borgon ana tsula ruwa kamar da bakin kwarya.
Ita dai tayi bacci amman ina shifa zazzaɓi ya hanashi rumtsawa.

Yanaji a jikinsa lokacin tashi yayi nafilarshi yayi amman ya gaza koda motsa yatsarsa.

Numfashi yake fiddawa hankali yana mai jin fargabar kada fa, har gari ya waye masa a haka.
To wai dama duk na miji in ya kusanci iyalanshi haka yakeji, ko dai shine yaji haka?.
To ko dai dan bai taɓa yi bane?.
Wannan shine nazarin da zuciyarshi keta nazarta masa.

Wani nannauyan ajiyan zuciya ya sauƙe mai ƙarfi lokacin da yaji an kwaɗa kiran sallan forko na a masallacin Masarautar Joɗa, wanda haka yake nunin saura awa ɗaya lokacin salla asuba tayi.

“Ya ilahi, ya mujibadda’awati”.
Ya fara maimaitawa a zuciyarsa.

Ita kuwa Aysha har lau bacci takeyi tare da sabke ajiyoyin zuciya a jere a jere.

Tsawon mintuna talatin yayi yana addu’o’in a zuciyarsa,
Kamar a fizge yaji bakinsa ya buɗu ya furta.
“La’haulawala ƙuwta illabillah aliyul axeem”.
A bakinshi, dai-dai lokacin kuma ladanin masalacin matsarautar Joɗa yayi kiran assalatu.

Wani irin tsuma yaji jikinsa nayi, zufa mai zafi ta karyo masa.
A hankali ya muskuta, kana ya ɗan ɗago hannunsa ya ɗaurasu tsakiyar bayanta,
cikin sanyi yace.
“A’ish, Ahh’ihch”.
shiru babu, amsa. Sai shessheƙan,
jin kuzarin jikinsa kaɗan yasa a hankali ya mirgina da ita ya kwantar da ita, kana ya ɗan ja baya.
sannan ya buɗe borgon ya fita, ita kuma ya rufeta.

A hankali yasa hannunshin ya kunna wutan ɗakin.
Gajeren wondon sa dake gefe yasa hannunsa ya ɗauka kana ya zira a jikinsa.

Miƙewa yayi tsaye.
“Waiyyyy, daɗi Alhamdulillah”.
Yace a saman lips ɗinsa ya ƙare zancen dasa hannun ya shafa mararsa da tayi mishi sakayau ba nauyi ba tauri ba ciwo,
taku ya farayi a nitse ya shiga bathroom.
Kai tsaye wurin wonka ya shiga.
Ruwan ɗumi ya sakarwa kanshi, tare da sunkuyar da kanshi.
Cike da mamaki ya zaro kekyawan idanunsa ya zubawa ƙasan baf ɗin ido, inda yaga ruwan nabi sawunshi da kalan ja.
Da sauri yasa hannunshin ya rufe shawan.
Cike da mamaki ya sunkuyo ya kalli boxes ɗinsa,
da sauri ya sunkuyo yayi ƙasa da ita,
idonshi ya rumtse da sauri sabida ganin gaba ɗaya matse-matsin cinyoyinsa jini hakama joystick ɗinsa duk jinine a jikinta.
ga boxes ɗin ya ɓaci.
A hankali yayi ƙasa da baxes ɗin ya cireshi, gefe ya ajiyeshi.
Karon farko kenan a rayuwarsa tun bayan girmansa da zaiyi wonka tsirara haihuwar uwarsa.
Haka yasa yakejin kunyan kanshi da kanshi.
Sabulu da soso ya jawo, wonka ya farayi soso da sabulu ya murje jikinsa tsab ya solle ko ina.

Daga nan kuma yayi wonkan tsarki inda yayi suppatul kamal wato wonka tsarki mai haɗe da al’wala.
Da sauri ya fito cikin jakkuzin.
Drower’nshi dake cikin bathroom ɗin ya nufa.
cike da kunya, da sauri ya zaro towel ya ɗaura a ƙugunsa,
Sannan ya dauko baby towel ya fara tsane ruwan jikin nasa, yana gama ya ɗan shafa mai kana ya zaro farar jallabiyarsa sabuwa dal ya saka bayan yasa farar boxes da singilet.

Wata farar al’kyabba sabuwa dal itama ya zura a jikinsa kana yasa hirami.
OudKareem dake cikin drower’n ya fesa tako ina na jikinsa kana ya fito.

Yana sako ƙafarshi a bedroom ɗin ana tada iƙama,
hakane yasa da sauri yanufi hanyar fita jin jam’i zai wucesa.

Juyowa ya kumayi, wayarshi ya ɗauka ya zura a aljihu kana ya iso bakin gado, cikin ya ɗan ɗaga murya yace.
“Aish tashi lokacin salla yayi”.
A hankali ta buɗe kekywawan kwayar manyan idanunta da suka rine sukayi jazir kana suka kumbura.
A hankali ya ɗan sunkuyo kan goshinta ya manna lips ɗinshi yayi kissing nata tare da cewa.
“Gud gerl, jazakallahu khairan yah Aysha tashi kiyi wonka kiyi salla.”
Shar-shar haka yaga wasu tafasassun hawaye sun kwaranyo mata, ba tare da ta motsa ko yatsarta ba.
Da sauri ya sunkuyo kanta da kyau cikin murya mai cike da kulawa da tausayawa yace.
“Sannu Aish kiyi haƙuri kinji kibar, tashi kiyi wonka kiyi salla kinga lokaci yayi”.
Ya ƙarashe mgnar yana juya ya fita jiyo ana tada kabbara.

Kai tsaye masallacin ya nufa.

Ita kuwa Aysha da kumburarrun idanunta ta bishi da kallo duk da dishi-dishi take gane.
Cikin rauni ta saki raunataccen kuka murya na rawa take kukan tare da cewa.
“Gud gerl ko? Ta ina zan iya tashi, kamin fyaɗe kace na tashi,
rufe idanun tayi sabida duhun da taga yana meye ganinta, kana ɗakin yayi mata duhu gaba ɗaya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button