GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Sarkin fada kuwa da sauri ya fito ya umarci hadimai maza da su kawowa baƙin abin taɓawa ai kuwa nan da nan aka cika gabansu Abboi da abubuwan ci da na sha.

Cikin tarin kula Lamiɗo ya kalli Bappa tare da cewa.
“A a Malam liman tafe kuke tare da shine?”.
Cikin nitsuwa Bappa yace.
“Na’am tare muke”.
Kai Lamiɗo ya jinjina tare da kallon Abboi gyara zama Abboi yayi fahimtar tambayarsa Lamiɗo yayi a hankali yace.
“Ai mutumin ƙasar mu ne zamane da wani babban dalili ya dawo dashi nan ƙasar ku”.
Cikin gamsuwa Lamiɗo yace.
“Makiyayinka ne shi?”.
Cikin mutuntaka da kunya Abboi yayi shiru dan shi Bappa yafi ƙarfin makiyayinsa a wurinsa Bappa ɗan uwane”.
Cikin yin murmushi Bappa yace.
“Eh ni ɗaya daga cikin makiyayansa ne”.
Yayi mgnar sabida fahimtar Abboi bazaice hakanba.
Sai kuma suka sake wani sabon gaisuwa.
Nan Babba ke cewa.
“Tare muke da mai ɗauki shi da kuma ƙanwata sunzo ganin jikar tamu su sun isa can”.
Cikin tarin jin daɗi Galadima yace.
“Masha Allah, Allah ya bada ladan ziyara”.
Amin Amin duk suka amsa.
Dai-dai lokacin kuma Affan yasa hannunshi ya ture sarkin ƙofa dake tareshi yana cewa.
“Lamiɗo yana ganawa da manyan baƙi”.
Cikin haki da ɗaga murya yace.
“Kai da Allah bani wuri. Abbana nake nema Abba! Lamiɗo!”.
Yayi mgnar da ƙarfi tare da kutsa kai cikin falon.
A tare suka juyo suka zuba mishi ido Abba kuwa da sauri ya miƙa tare da cewa.
“Na’am Affan meya faru?”.
Cikin haki yace.
“Abba Mamey Lamiɗo Mamey’nmu ta dawo wlh Mamey ta dawo gata can a Part ɗin Hamma Jabeer su Umaymah nata kuwa Mameynmu ta dawo a mutun ba tsuntsuwar Boleru ba”.
Kusan a tare gaba ɗayansu suka miƙe banda Lamiɗo dasu Abboi tare da cewa.
“Kai Affan nitsu ka gaya mana”.
Cikin kaɗuwa ya kamo hannun Abban nasu tare da cewa.
“Zo muje ka gani wlh Mamey na ta dawo a mutun ba tsuntsuwar Boleru ba”.
Ai kafin ma ya rufe baki Abba ya juya da sauri yabi bayan Abbanshi.

Abboi kuwa da Bappa da Arɗo Bani da Alhaji Haro kallon juna sukayi tare da yin murmushin zatonsu ya tabbata jinjinawa juna kai sukayi
Sai kuma Bappa yace.
“Ya ilahi meke faruwa?”.
Cikin yin Murmushi Lamiɗo yace.
“An tashi taron fada sai gobe”.
Nan take duk sauran suka miƙe suka fita kowa ya nufi muhalli sa cike da alhini.

Shi kuwa Lamiɗo Galadima ya kalla tare da cewa.
“Muje gidan Jabeer ɗin Kuma taso muje ƙofar surkin naku”.
Yayi mgnar da yaƙini a ransa su Bappa ne ke tafe da abinda suka daɗe suna tsumayin wato dawowar Mamey (Ummey) kenen.

Ai kuwa da sauri su Bappa suka bi bayansu.
Fadawa na musu rakiya.
Ɗan zagi na baza riga da cewa.
“Gyara kimtsi, sarki ya gaisheku”.

A haka suka nufi Part ɗin Sheykhhhh.
Kusan a tare suka isa dasu Abba dan rawan da jikinsa keyi ya hana masa yin sauri.

Lokacin ɗaya kuma duk masararutar Joɗa ta cika da lbrin dawowar Mamey kamar yadda labarin juyewarta da bacewarta ya karaɗe ko ina na Masarautar Joɗa.

Suna shiga Affan yaja hannun Abbansu har gaban Shatu da Sheykh wanda ke ruggume da Ummey har yanzu a sume.
Sun kasa taɓuka komai, duk da shi dai Sheykh ya gane a sumen take.

Cikin haki Affan yace.
“Gata Abba ka gani ga Mameynmu”.
Wani irin farin ciki ne mai masifar yawa dake shirin ɗauke masa numfashin sa ne ya sauƙo mishi, jin hakane yasa yayi sauri ya sunkuya a tsakiyar falon ya fuskanci al’ƙibla ya faɗi yayi sujjada gaban Ubangijin talikai sarki buwayi gagara misali.

Dai-dai lokacin su Lamiɗo suka shigo.
Ganin Bappa ne yasa kukan Shatu tsananta murya na rawa tace.
“Bappa Ummey na Bappa Ummey na”.
Da sauri irin na sarakuna su Lamiɗo suka ƙara so wurin.
“La ha ila ha illalalhu Muhammadu Rasulullahi Sallallahu alaihi Wasallam”.
Suka faɗa a baki a haɗe tare da zama bisa kujera.

Cikin sanyi Bappa ya kalli Shatu kana a hankali ya juyo yankallesu gaba ɗaya hawayene cikin a fuskarsu.
Ga Jamil a sume.
Galadima kuwa da Lamiɗo murmushi sukeyi tare da maimaita ƙalmar hamdala”.
Da sauri Junainah tazo ta faɗa jikin Bappa tare da sakin kuka tace.
“Bappa Ummey na ta rasu ne?”.
Da sauri ya jujjuya kanshi tare da juyowa ya kalli Khadijah ƙanwar Shatu cikin sanyi yace.
“Khadijah in akwai zam-zam a gidan kawo min in kuma babu bani ruwan sanyi”.
Da sauri Ummi ta miƙe kitchen ta nufa tana mai cewa.
“Akwai zam-zam bari in kawo”.
To kawai yace mata.
Abba kuwa a hankali ya ɗago kanshi kana ya jingina bayanshi da sawun Lamiɗo ya kife kanshi bisa guiwar Lamiɗo sai ga wani kuka mai rauni ya subce mishi.

Da sauri Bappa ya amshi goran zam-zam mai sanyin.
Matsowa yayi kusa da Shatu.
Da sauri ya buɗe goran zam-zam ɗin ya tsiyayi sassanyan ruwan a tafin hannunsa, kana ya saita fuskarta tare da cewa.
“BISMILLAHI”.
Ya watsa mata shi a fuska da ƙarfi tare da sunan Allah.
Shiru babu motsi da sauri ya sake tsiyayo wani ya watsa mata tare da bismillah.
Stiil ba motsi da ƙarfi ya kuma watsa mata a karo na uku.
Da ƙarfi taja wani irin nannauyan numfashin mai tsawo tare da cewa.
“La’ilahaillaha Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam. Astagafirullaha wa’atubu illaik”.
Kusan a tare gaba ɗayansu falon suke furta Alhamdulillah.

Cikin wani irin yanayi Jabeer, Jafar, Jalal, da Jamil wanda Bappa ya watsa mishi ruwan ya farfaɗo a firgice suka matso gabanta sukayi mata zobe.
Kana Umaymah da Mamma da Aunty Rahma suna kusa dasu.
Cikin wata iriyar murya mai raunin amo Sheykh ya kamo hannunta murya na rawa yace.
“M…mah..Mam.. Mameyyy”.
Da sauri ta ɗago jajayen idanunta da tsananin ciwon kai ya rinasu ta watsa masa su cikin nashi ba tare da ta amsaba.
Cikin rauni ya kuma cewa.
“Mamey Mamey na Jabeer ɗinki ne! Mamey kin manceni ne, gani Ga Yah Jafar ɗina ga sakalallun tagwayenki ga Affan ɗinki ɗan lelenki ga Abba na Ga ƴan uwanki Umaymahna ga Mamma na ga autar Sitti Aunty Rahma Mamey Jabeer ɗinkin ne ga Ummi amintacciyar jakadiyarki mai riƙon amana”.
Shiru sukayi baki ɗayansu suka zuba mata idanu.
Ita kuwa ido ta lumshe wasu hawaye masu ɗumi suka zubo mata cikin raunin murya tace.
“Alhamdulillah Jabeer na tunoku gaba ɗayanku”.
Wani irin farin cikin ne mai tarin yawa ya cika musu zuƙatansu baki ɗayansu.

Da sauri suka juyo suka kalli Bappa da yake cewa.
“Alhamdulillah baiwar Allah ta tuno baya ta gane ƴaƴanta da ƴan uwanta”.

Da sauri Sheykh ya juyo tare da kamo hannun Shatu wacce cikin kuka da rarrafe ta matso gaban Ummey da kyau murya na rawa hawaye na zuba tace.
“Innalillahi shike nan Ummey ta tuna baya kenan Bappa zata mantani kenan?”.
Wani numfashin Ummey taja tare da zubda hawaye.
Ita kuwa Shatu kamo hannun Junainah tayi cikin rawan murya hawaye na kwarya tace.
“Ummey ki kalleni Ummey nice Shatunki fa Ummey koda zaki tuna baya kada ki manceni Ummey kalleni fa nice Shatunki kalli Junainah’nki ƴar autarmu Ummey koda zaki manceni dan Allah kada ki mance Junainah ke kika haifeta a cikinku muka reneta bata san kowa ba sai nudake”.
Wani irin kuka ta saki mai ƙarfi tare da jawo Junainah da itama kukan takeyi juyowa tayi ta kalli Yah Sheykh cikin rawan murya tace.
“Ummey nane fa da tun inada shekaru takwas a duniya na bar gaban Dedde na da Abboi na na dawo gabanta ita ta raineni kamar Uwa itace ta haifi Junainah itace ta bamu tarbiya sanadinta muka baro ƙasar Cameroon muka dawo Nigeria muka zauna Rugar Bani wayyoooooooo Allah na Ummeyna kada ki manceni”.
Shirun da Ummey tayi yasa gaba ɗaya tausayin Shatu da Junainah yasa kowa zubda hawaye sabida fargabar kada fa ya zamo ta tuno baya can ta mance yanzu.
Kuka sukeyi baki ɗayansu hatta Afreeen dake hannun Aunty Amina kuka takeyi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button