GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Wani irin harbawa zuƙatansu suka farayi da ƙarfi-ƙarfi, suna jam junansu i ziwa jikin juna tamkar mayen ƙarfe.

A hankali Shatu taji jikinta na macewa.
Kanta ta manna a ƙirjinta kunnenta na dai-dai kan ƙahon zuciyarshi.
Lumshe idonta tayi tanajin wani irin masifeffen ƙamshi turare mai daɗin shaƙa dasa baccin daɗi cikin ƙanƙanin lokaci, koda yake baccin nata baya rasa nasaba da abinda ke wujijjigata.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, shiru yayi yanajin yadda tasa hannunta, ta zagayo ƙugunshi ta riƙe gam-gam da iya ƙarfin ta.
Sai kuma ya ɗan sunkuyo cike da mamaki yakkali fuskarta, tuni tayi bacci cikin ƴan second nin nan.

Cike da mamaki ya zubawa fuskarta kallon tuhuma.
A hankali yasa yatsunshi ya fara ɓanɓaro hannunta,
yanayi yana ja da baya-baya yana komawa cikin ɗakin.

Ita kuwa binshi take amman ba bi irin na takuba,
Cike da mamaki ya ƙara leƙa fuskarta.
Tabbas bacci tayi.
Janyeta yayi daga jikinshi kana ya saketa a hankali ta tafi zata faɗi, bai tareta ba, sai dai yasa ƙafarshi ya tare dai-dai inda yaga kanta zai bugu.
Cikin Sa’a kanta ya sauƙa kan rumfar ƙafarshi.
A hankali ya ajiye ƙafar tashi a ƙasa.
Kana ya janye ƙafarsa, kanta ya konta a ƙasa.

Cike da mamaki, ya juya ya koma can inda yake konciyar.
Bai cire al’kyabbar ba ya konta yana mgnar zuciya.
“Mutun kamar mayya, wannan baccin kuma na meye to”.

A haka shima yayi baccin da yasan in bai yishiba, zaiji ciwon kai.

Kiran sallane ya tadashi.
Tanan konce har yanzu.
Al’wala yaje yayi kana ya fito ya kimtsa ya fesa turare.
A hankali yazo kusa da ita.
Ɗan sauran ruwan dake tafin hannunshi ya yarfa mata a fuska.

A hankali ta buɗe idonta, kana ta kuma lumshesu haka tayi kusan sau uku ganin hakane a hankali yace.
“Ke kasa uwar bacci tashi kiyi salla”.
Miƙa tayi a hankali tare da cewa.
“To”. Shiru yayi yana nazarin muryarta, ba haka muryarta yakeba.
Wannan shine abinda su Ummi basu ganeba, shi gashi ya gane a take,
Su kuwa basu gane cewa muryarna ba tata bace.

Kanshi ya ɗan juya tare da cewa.
“Uhummmm”. Daga nan ya fita, ita kuma Shatu da ido ta bishi.
Yana fita ta miƙe kalle-kalle tayi a ɗakin nashi sosai har ƙarƙashin gado ta leƙe.

Tana gamawa ta shiga Bathroom nashi.

Wani irin murmushi tayi tare da cewa.
“Komai nashi mai kyau da tsabta”.

Al’wala tayi kana ta fito, a falo ta samu Ummi da Hibba da alamun a nan sukayi salla.

Sosai Ummi tayi mamakin kenan, tana ɗakin Sheykh ne, murmushin jin daɗi tayi a ranta tace.
“Ikon Allah kenan”.

Ita kuwa Shatu hijabin Hibba ta amsa tayi salla.
Suna zaune a nan ya shigo.
Wayarshi na kunne cikin nitsuwa yace.
“To Aunty Hafsat gata nan ɗazu bacci takeyi”.
Cikin murmushin tace.
“To bata”.
A hankali ya iso tsakiyar falon wayar ya miƙo mata tare da cewa.
“Aunty Hafsat ce ƙanwar Umaymah saura kiyi mata rashin ta ido”.
Ya ƙarishe mgnar a hankali yadda ita Aunty Hafsat bazata jishiba.

Ita kuwa amsa tayi tare da karawa a kunne cikin nitsuwa tace.
“Assalamu alaikum”.
Fuska a sake tace wa alaikissalam ɗiyata, ya gida ya sanyi”.
Muryar matar sak irin ta Umaymah shiyasa cikin jin daɗi tace.
“Lfy lau Alhamdulillah Aunty ya gida da aiyuka”.

“Alhamdulillah”. Tace kana ta ɗora da cewa.
“Sunana Hafsat Jalaluddin Muhammad Sultan”.
Cikin jin daɗi tace.
“Eh Aunty na sanki ai Umaymah ta gaya min sunanki ta nuna min hotonki da Aunty Rahma da Zakiya da Yezeed dama duk sauran”.
Cikin jin daɗi tace.
“Masha Allah, to ki amshi number ta data Rahma da Zakiya a wurin Hibba, ɗazuma Zakiya taita kiranki ashe kina bacci ne”.
Cikin nitsuwa tace.
“To Aunty yanzu kuwa, ngd matuƙa”.
Cikin jin daɗi Aunty Hafsat tace.
“Allah ya muku al’barka ya baku zaman lafiya.
In Sha Allah zamuzo auren Haroon zaki gammu mu ganki”.

“Amin Amin. Aunty Allah ya kaimu lokacin ya kawoku lfy”.
Tace kana sukayi sallama.

Daga nan suka shiga kitchen.
Jamil kuwa tuni yaje yayiwa wani mai musu aikin gidansu.
Yasa ya nemi irin wannan tayis ɗin. Yace gobe da safe misalin sha ɗaya zaizo ya ɗauke shi.

Washe gari da safe.
Misalin karfe tara, Sheykh ya fito cikin shiga ta al’farma, yau ba al’kyabba a jikinshi riga da wondone sai malum-malum gariya mai kyau.
Getzner ce mai masifar kyau Brownish red color mai ɗan karen kyau da sheƙi, gariyar tasha aiki mai ɗan karen kyau da zaren surfani mai sheƙin piash color.
Hular kanshi da red and piash color, takalmin shi kuwa fatar ta kifa kalar red ɗin.
Yayi kyau sosai ya kafa hular nan cas a kanshi. Kekyawan suman kanshi ya konto gefe da gefe da ƙeyarshi sai sheƙi da ƙelli yakeyi.
Sajenshi ya kwanta lib, gashin girarsa dana gemunshi ɗan cas dashi misalin kamu ɗaya, sai sheƙi suke zubawa.
Ɗan madai-daicin bakinshi mai jajayen laɓɓa sai sheƙi sukeyi.
Yar ƙaramar jakar na’urar System ya riƙe a hannunshi, sai wani ƙamshi mai daɗin ji yake fiddawa, ɗan farin siririn Glass irin na manyan Doctors ya manna a fuskarshi kana ya fito.

A falonshi ya sameta, tana jera mishi breakfast.
Ganin zai wucene ta ɗan biyoshi a hankali ya zama suna tafe a jere.
Cikin kallon suman ƙeyarshi tace.
“You are breakfast is ready”.
Bai kulata ba yaci gaba da tafiya.
Ita kuma ƙeyanshi ta mannawa harara.
A haka suka fito.
Ya sallami Ummi da Jamil da tunda suka karya bai tafiba.
Da sauri Jamil yabi bayanshi yana cewa.
“Uhum Dakta sai yaushe zaka dawo ne?”.
Juyowa yayi ya kalli Jamil sai kuma yace.
“Kanada matsala ne?”.
Da sauri ya jujjuya kanshi tare da cewa.
“No. I’m very fine”.
yayi mgnar yana jijjiga jikinsa.
Kai ya kaɗa ya juya zai fita,
Da sauri Jamil ya kuma tambayarsa.
“Dakta yaushe zai dawone”.
Cikin tsuke fuskarsa yace.
“Ban sani ba”.
Daga nan ya fita, shi kuwa Jamil tsalle yayi tare da cewa.
“Yesss, Dakta Allah ya kiyaye hanya, a wuni lfy a asibiti”.

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Yi maza to ka ɗauki shi”.
To yace kana ya miƙe ya fita.
Sanin cewa yanzu Sheykh yana sashin Hajia Mama ne.

Haka yasa ya rigashi fita.

Ummi kuwa miƙewa tayi taje ta rufe ƙofar sabida bata son wani yazo ya shigo.
Kiran Jamil tayi a waya tace in sun isoma ya kirata a wayane zata buɗe mishi.

Tana katse kiran ta juyo ta kalli Shatu dake zaune gefenta tana ce mata.
“Yauwa to Ummi muje mu fara aikin kafin ya iso mun kusa cimma aikin.”

Cikin mamaki tace.
“A a keda kikace sai an matsar da gadonshi sannan aikin tono ai bazamu iyaba. Dole sai mazan”.
Cikin muryar da har yau Ummi ta kasa banbance shi da asalin muryarta tace.
“A a ba matsala Ummi muje zamu iya”.
Ta ƙarishe mgnar tana yin gaba, ganin hakane yasa Ummi Binta a baya.
A hankali suka shiga falon.
Tana mai cewa Ummi.
“A nan ma an mishi wani aikin amman shi bai shiga jikinsa ba, sabida yanada Garkuwar addu’o’in da yakeyi yau da kullum.
Shiyasa duk sabbin sihirurruka basa shigarsa.
Sai dai waɗanda akayi mishi tun bai gama girma ba.”
To kawai Ummi ke ce mata sabida jin kamar muryarta na canza mata.

A haka ta kuma nuna mata wani wurin.

Tare da cewa.
“Uhumm Ya Jafar suke nema, su maida majanunin kan bola sai kuma sharrinsu ya zame mishi al’khairi,
Tsawon shekaru baya mgn sai ambaton Allah. Bashi ba zunibi sai tarin lada da yake samu na karatun al’ƙur’ani da ya zame mishi abokin hira.

To ita kuma me take nema a duniya da zata cutar da baiwar Allah da ahlinta duka haka.
In banda lalaci da son duniya na miji ya lalace da bin matsafa yana sawa ana sabauta ɗan uwanshi da yayanshi.”
Ita dai Ummi binta takeyi da ido da ƙafa har suka isa bedroom ɗin shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button