GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

A haka dai suka shiga Masallaci.

Dole yau a gaggauce yayi Kudbar jumma’a dududu 15 minutes yayi yana kudbar kan halaccin mace ta kalli mijin da yakeson aurenta, kamar dai yadda yayi al-ƙawari a wancan satin.
Daga nan aka kabbarta sallah.

A can Rugar Bani kuwa.
A hankali Shatu ta ɗago kanta ta kalli Ba’ana jin tunda suka tsaya baice mata komaiba, ganin yadda ya zuba mata idone yasata, saurin yin ƙasa da kanta,
cikin sanyi muryar tace.
“Ya Ba’ana zamu tafi rana tanayi fa!”.
Wani dogon numfashi ya ja ya sauƙe da ƙarfi, kana a hankali ya ƙara matsowa kusa da ita da sauri tayi baya cikin tsoro, hannunshi ya ɗaga mata alamun karta gudu, kai ta jujjuya tare da ƙara matsawa cikin rawan murya tace.
“Ba kyau ina tsoro”.
Kanshi ya jingina da jikin bishiyar gamjin da suke ƙasanta, ido a rufe yace.
“Da dai inada niyar cutar dake, da bamu kawo zuwa yau ban cutar dakeba Shatu, kadafa ki mance tun kina ƴar tatsitsiyarki nake sonki kuma nake tare dake, dare da rana, kada ki mance kullum sai kinje gidanmu da dare da asuban fari kin amsowa Ummey mgninta, da har ina son cutar dake da tun wancan lokacin zan cutar dake.
To amman bani da niyar cutarki, ina sonki ne sabida Allah, da kuma gsky da zuciya ɗaya, Shatu koda zaki ƙi yarda dani a kan komai dan Allah ki yarda dani cewa ina sonki, na kuma soki a baya zan soki har gaban abadan, wlh babu ƙarya a cikin soyayyarki a zuciyata, Shatu sonki shine babban raunina a duniya.
Har yau babu wani abu dake firgitani da bani tsoro sai rasaki.
Babu wani abu na duniya daya taɓa sani zubda hawaye sai soyayyarki, dan Allah ki dena zaton dan na matso kusa dake zan cutar dake, ki amince dani in baki abinda idonki zai buɗu da gane sihiri duk ƙanƙantarshi”.
A hankali take juya mishi kai cikin sanyi tace.
“Na sani Ya Ba’ana wlh na yarda da kai akan soyayyata, na sani bazaka cutar daniba, tunda baka cutar dani a bayaba, nasan kana sona, na kuma yarda da son gsky kakemin, to amman ni bana son wadannan abubuwa asirce-asircen sabida haramun ne.
A hankali ya zame jikinshi ya zauna kan jijiyan bishiyar.
Ganin haka itama tayi sauri ta zauna bisa guiwowinta ta durƙushe a ƙasa.
Cikin mamaki tace.
“Dan Allah ya Ba’ana meyasa kwanan nan duka sai kayi ta zubda hawaye a gabana, hankalina yana tashi.”
Kanshi ya ɗan ɗaga ya kalli sama, a hankali yace.
“Shatu ina sonki zan kuma soki har iya numfashin na, bazan bari wani abu ya rabani da keba, in kuma akasamu wani ya zama ƙaddarar rabani dake, to shi kuwa tabbas zan rabashi da rayuwarshi, kiyi haƙuri in dai a kanki ne zan iya yin komai, na kuwa san duk duniya babu wanda yasan hanyar da za’abi a kamani ko aci galaba a kaina, sai ke ranki ke ɗaya tak ce kikasan duk wani sirrina ban saniba ko zaki iya min halacci ki sirranta min rayuwata”.
Da sauri tasa hannu ta share hawayenta tare da cewa.
“Ya Ba’ana ai rayuwa a hannun Allah take, wata ƙilma in rigaka mutuwa, kuma in dai nice in sha Allah bazan baiyana sirrinka dan a cutar da kaiba, ko ba komai kana soma kuma kace dan zaka nemo su ya Gaini ne kayi wannan tsarin gudun kada mugaye su cutar da kai, Ni na sani Ya Ba’ana waɗannan layun bazasu kareka ba, sabida ba hanyar Allah ka biba amman ni zanyi ta maka addu’a”.
Ido ya zuba mata a zahiri da baɗininta gsky ta faɗi dan yaga hakan cikin ƙwayar idanunta.
A hankali ya jawo tandun duma dake rataye a kafaɗunshi, cikin sanyi yace.
“Ga ruwa kisha”.
Da sauri ta jujjuya kanta tare da cewa.
“Bana jin ƙishi”.
Tura mata tandun yayi gabanta tare da cewa.
“Eh ba mgnin ƙishi bane, kishi dan kiji sanyi a zuciyarki naga kina kuka”.
Cikin share hawayenta tace.
“Ba kai bane ka sani kukan kana ta barmin amanar sirrikanka bayan kuma shi amana rikeshi nada girma da nauyi da wuya”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Zaiyi wuya ki riƙe kenan?”.
Da sauri tace.
“In sha Allah zan riƙe”.
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
“Bazaki sha bako?”.
Kanta ta gyaɗa mishi alamar eh.
Kana ta miƙa tsaye, gaba ta ɗan yi kusa da Rafi’a, tace.
“Rafi’a mu tafi”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Rafi’a ku tsaya”.
Cikin tsoronshi Rafi’a tace.
“To Ya Ba’ana”.
Da sauri ya ƙara so gabansu, tare da cewa.
“Mata ɗago hannunki mu gani kinada zobene?”.
Kai ta girgiza alamar a a babu.
kana ta ɗaga hannunta na dama,
Yatsarshi ya karkaɗa mata tare da cewa.
“Lalala ɗago hannun hagu mu gani”.
Cikin gajiya ta ɗago hannunta, fararen tausasan zara-zaran yatsunta suka zubawa ido gaba ɗayansu.

Babu zobe ko ɗaya a yatsunta,
Murmushi yayi kana yace.
“To bari in baki zoben ziyara, koda bakya tare dani, duk lokacin da na nake kusa dake kawai zakiga zoben a yatsunki”.
Da sauri ta buɗe baki da nufin cewa a a.
Kawai sai tayi shiru ganin wani irin zoben azurfa mai masifar ƙyalli da sheƙi sai ɗauke ido yakeyi.
Ta juyo zata ce mishi a a Ya cire sai kuma tayi shiru ganin ya ɓace daga gabansu.
Yatsunta tasa da nufin cire zoben da sauri ta barshi jin tamkar yatsunta zasu tsinke.
Rafi’a kam tuni tayi gaba, haka yasa itama tabi bayanta.

Suna zuwa bakin titin suka samu motar zuwa cikin Ɓadamaya.

A can cikin masarautar Joɗa kuwa,
Bayan an idar da salla, kamar kullum Lamiɗo ya gaggaisa da mutane, talakawan garinshi.
Shi kuwa Jabeer dashi da tawagarsa duk sun nufi cikin gida.
Sabida Galadima nata ce mishi su tafi cikin gida su fara shirin tafiya.

Haka yasa duk suka nufi cikin gidan masarauta.
A nan babban farfajiyar suka ɗan tsaya.
Ido Jabeer ya ɗan zubawa jerin motocin da a ƙalla sun kai ashirin da biyar zuwa talatin an bisa alamu anyi manyan baƙi ne ko kuma za’ayi fita mai mahimmanci.

Cikin suka wuce a falo suka samu Umaymah, Hajia Mama, Aunty Juwairiyya, da Ummi, duk suna zaune suna ɗan hira.
Hibba kuwa tana kitchen.

Suna isowa ta fito da sauri jin muryarsu.
A hankali ta isa gefen Jalal cikin yin ƙasa da murya tace.
“Ya Jalal kazo kaci abinci karku tafi bakaci komaiba”.
Kanshi ya ɗan gyaɗa mata,
Jamil ne ya hararesu tare da cewa.
“Allah shi ƙara, ai in dai Jalal ne kaɗan kika gani da gwatsalel, mutumin da ba’a iya masa bare a masa gwaninta”.
Haroon ne ya ɗanyi dariya tare da cewa.
“Haka suke shida Jabeer yadda suke kamanninsu iri ɗaya hakama halinsu”.
Da sauri Jamil ya zare ido tare da ɗan ja da baya yace.
“Tab a a Ni dai wlh bance hakaba”.
Jabeer kanshi Jamil ya bashi dariyar da dole ya ɗan murmusa, tuni sukuma sauran dariya sukeyi.
Ya Jafar kuwa shi ganin murmushin Jabeer shine ke sashi murmusawa.

Ita kuwa Hibba tura baki tayi ta koma gefe ta zauna alamun tayi fushi, baibi ta kantaba, sai Jamil ɗin ne ya ɗan lallasheta, haka dai sukayi ta yar raha, saida Lamiɗo ya aiko su fito kafin.
Suka miƙa duk suka fita, shi kuwa Sheykh Jabeer gefensu Hajia Mama da Umaymah ya ɗan rusuna kusa da Umaymah a hankali yace.
“To Umaymah bari inje bisa umarnku ba don raina yaso ba”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Allah ya bada Sa’a ya kaiku lfy ya kuma dawo daku lfy, Allah ya tabbatar mana da al’khairan dake cikin wannan tafiyar, al’farma Annabi da Alqur’ani”.
Amin Amin suka amsa baki ɗayansu, Hajia Mama dasu Ummi ma duk sukayi mishi addu’a, kafin ya fito.

Yauma kamar ranar mota ɗaya suka shiga da Haroon da Lamiɗo da Ya Hashim da Laminu.

Kana sauran tawagar sarki.
Daga nan suka nufi hanyar fita gari su nufi garin Shikan.
A cikin motocinsu kamar na ranan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button