GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ganin Ya Jafar ya miƙa ya juya zai fitane yasa yayi saurin.
Bin bayanshi ya rakashi kana ya dawo ya konta.

Ummi ma ta konta.

Ƙarfe ɗaya da rabi Sheykh ya tashi yayi ta nafilfilinshi tare da jere addu’o’in da neman warakar damuwar rayuwarshi data ahlinshin.

Ummi ma tuni ta tashi. Ƙarfe uku ta fito.
Falon hango haske a ɗakun Shatune ya tabbatar mata sun tashi.

Kitchen ta wuce. gas ta kunna ta ɗumama musu miyar, kana ta haɗa plate spoons and cups tazo ta jere bisa Dinning table.

Sannan ta koma kitchen ta ɗauko musu drinks and water masu sanyi tazo ta jere komai yadda ya dace.

Kana ta dawo falon ta zauna riƙe da carbinta.
Ƙarfe huɗu dai-dai su Jalal suka buga ƙofar sanin sune yasa, ta tashi ta buɗe musu.
Suna shiga ana buga bindigar sanarda mutanen masarautar Joɗa cewa lokacin sahur yayi.
Bayan mintuna talatin kuma za’a kuma sakin bindingar.

Cikin gudu Shatu ta fito falon jiki na rawa, kiciɓis tayi da Ummi da takeda niyar zuwa ta ta kirasu suzo suyi sahur.
Ruggume Ummi tayi ƙam-ƙam tare da neman inda zatasa ranta.
Allah ya sani tana tsoron ƙaran abu biyu, ƙaran aradu da walƙiya da kuma ƙaran harbin bindiga”.
Cikin mamaki Ummi tace.
“Oho Aysha duk wannan tsoron na ƙaran harbin bindiga ne, lallai kuwa in baki sababa kafin Ramadan ya ƙare zakisha wuya.”
Hibba ce ta fito tana dariya tace.
“Allah ko Ummi ana ɗaukan alhaƙin Aunty Aysha”.
Babban Falon suka nufo yayinda duk jikinta ke karkarwar.”
Dinning area Suka wuce.
Bayan duk sun zaunane Ummi tace Hibba tasa musu abinci.
Buɗe kulolin tayi.
Jolof ɗin taliya da kifi Aunty Juwairiyya tayi, sai kuma
Flaks ɗin kunun gyaɗa.
nasu kuma tuwon semo da miyar ɗanyar kuɓewan sai tea da sauran kayan sha.
Ta zubawa kowa abinda ranshi keso.
ita dai Shatu mamakin abincin Aunty Juwairiyya na yau takeyi sabida idonta bai gano mata wani mugun abu a cikiba.

Haka yasa itama shi taci. Da kunun.
duk sunyi nisa a yin sahur ɗin. Amman shi bai fitoba,
Sai ƙarfe huɗu da rabi ya fito.
A hankali ya iso Dinning area ɗin gaban washing hand Baby ya ɗan tsaya tare da wonke hannunshi.
Ita kuwa Shatu tana ganinshi ta ɗanyi gyatsa tare da cewa.
“Alhamdulillah kana ta miƙe”.
Kujerar dake gefen Jalal ya zauna,
Yana zama ita kuma ta juya ta nufi cikin falon.
Shi bai ma kalli inda takeba.
Cikin falo ta koma hannunta riƙe da cup ɗin kunun da take sha.
Cikin kula Ummi tace.
“Sai yanzu?”.
ta ƙarishe mgnar tana zuba mishi tuwon semo da miyar ɗanyar kuɓewar da yaji nama da kifi da man shanu.
gyara zamanshi yayi tare da cewa.
“A jinkirta sahur a gaggauta buɗa baki Ummi Manzon Allah yace.”
Murmushi tayi tare da cewa.
“Hakane”.
Bismillah yayi tare da gyara zaman shi, ya fara cin abincin.
yaci mai ɗan yawa dan daren jiya baici komaiba.
tea ta haɗa mishi.
Hannunshi ya wonke kana ya amshi tea ɗin ya fara sha.
Jalal, Jamil, kuwa ci sukayi sukayi haninƙan kana suka miƙe zasu tafi.
Cikin kallonsu yace.
“Kadafa kuje ku kwanta, kuyi al’wala ku wuce masallaci.”
To sukace kana suka tafi.
Shi kuwa yana gama yin sahur ɗin ya koma Side ɗinsa,
Wonka yayi tare da al’wala kana yayi shigarsa ta farar jallabiya.
Bayan sun idar da salla gari ya ɗanyi hasken ya taso ƙeyansu, suka dawo gida.

Side ɗin su suka wuce. raka Ya Jafar yayi har Side ɗinsa kafin yazo ya shiga sashinsa.
Shiru falon babu kowa, bisa alamu kuwa tuni Ummi ta kimtsa ta share da goge ko ina, ta sassake labulaye, tare da sa turaren wuta mai ƙamshi.
Kana ta kashe hasken ko ina, babu abinda ke tashi sai ƙamshi da sanyin A/C da karatun Alqur’ani mai girma da kuna.

Falonshi ya nufa yana shiga,
ya zauna a falo, Dua Azkar ya fara yi cikin zazzaƙan muryarshi.
Bayan ya isane kuma ya fara karatun al’ƙur’ani. Sai bakwai da rabi dai-dai ya shafa addu’a kana ya wuce bedroom ɗin shi.
Wutan ya kashe tare da ƙara ƙarfin gudun AC.
sannan ya nufi luntsumemen gadonshi ya kwanta bisa gefen damanshi tare dasa hannun ya jawo blanket ya rugu.
A hankali lips ɗinshi ke motsawa, alamun tasbihi yakeyi.
Cikin 13 minute bacci mai daɗin gaske ya kwasheshi”.

Haka can wurinsu Shatu ma, saida tai karatun al’ƙur’ani sosai kafin ta konta hakama Hibba.

Ummi kuwa wonka tayi tayi al’wala ganin bakwai ta wuce ne tayi walahan ta raka biyu.
Kana tayi karatu sai ƙarfe tara da rabi ta konta take kuwa bacci yayi awon gaba da ita.

Ƙarfe goma dai-dai ya tashi daga baccin da yakeyi.
Wonka yayi tare da al’wa kana ya fito ya kimtsa cikin shiga ta al’farma. Turare mai ɗan sanyi ya fesa kaɗan kana.
Ya ɗanyi tafiya kaɗan zuwa gefen Bedside drower’n dake tsakanin gini da gado, wanda akwai tazarar fili mai ɗan faɗi ana yake shimfiɗa sallayarsa wurin ya zama keɓantaccene.
Walaha, yayi raka biyu kana yayi addu’o’in yau da kullum ya shafa, miƙewa yayi ya ɗauki System ɗinshi ya riƙe a hannunshi, kana ya ɗauki woyarshi ɗaya cikin su huɗu da suke bisa Bedside ɗin.

A hankali yake taku, har ya fito tsakiyar falon. Shiru gidan tamkar babu mai rai a ciki.
A haka ya buɗe ƙofar ya fita, tare da ja musu ita ta baya.
Koda ya fito asalin farfajiyar masarautarma ko ina shiru kakeji, sai ɗan zirga-zirgan fadawa da hadimai masu tattara ɗan sharan dake ko wanne bakin part.
Suma kowa a hankali yake aiki alamun akwai bacci tare dasu.
Motarsa kirar Tolls Royce, wacce kuɗinta zai iya kai kimanin Billion 4, 959,630, naira. Baba Lado shine Drevernshi da sauri ya taso yana suka tafi.
Daga nan masallacin jumma’a na kasuwa ya wuce.
Sha ɗaya saura ya isa, inda ya samu tuni masallacin ya cika yayi maƙil da al’ummar Annabi maza yara da manya tsoffi da tattawan, yan kasuwa sun cika sunyi maƙil iso warshi kawai dama ake jira.

Motarshi na gama tsayuwa yan agaji suka rufa mishi baya, babban cikinsu ne ya buɗe mishi marfin motar tare da ɗan rusunawa yace.
“Barka da safiya Malam”.
Cikin tsananin kulawa Sheykh Jabeer ya kalli dottijon da ya kai ya haifeshi.
Hannu ya miƙa mishi tare da cewa.
“Barka dai Baba Sule Ya ibada”.
Cikin jin dadi yace.
“Alhamdulillah”.
Sai kuma ya kalli sauran wanda yawanci bazasu wuce sa’annim ƙaninshi mai binshiba Affan kenan,
Murmushi yayi tare da basu hannun yana mai tuna cewa tabbas da Affan yana ƙasar nan To bana a Ɓadamaya zaiyi azumi, kuma ya sani da yanzu suna tare anan, dan shi ba irinsu Jalal bane.
Zagayeshi sukayi suna buɗa mishi hanya yana wuce.
Ta kofar da liman ke shiga ya shiga.
sit kakeji da yake duk mazane, gashi kuma ansan ƙa’idarshi shi baya son surutu in yana tabsir.
Zama yayi tare da kallon ɗan agajin dake saƙala mishi abin ɗaga sauti mgn a jikin al’kyabbar jikinshi.
Yayinda wasu kuma suka koma bayanshi wasu suka tsaya gefenshi, yan ɗaukan awazin kuma na gidajen Radio da TV duk sun kafa na’ura su a gaban table ɗin da yake zaune.
Bayan an gama kimtsa mishi komaine, ya gyara zamanshi tare da kallon alaramma Abdulƙadir wanda shine zai jamishi baƙi.
System ɗinshi ya buɗe tare da gyara mata zama, haka shima Alaramma Abdulƙadir yayi da Qura’an ɗin gabanshi.

Gyara murya Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero yayi tare da fuskantarta taron al’ummar dake gabanshi cikin ɗan ɗaga sauti yace.
“Bismillah rahmanirrahim. Assalamu alaikum warahmatullahi wa barka tuhu.
Innal hamdalillah nahmaduhu wanasta inuhu wanastagfiru wana uzubillahi min shururi am fusina wa sai’yi ati amalina. Manyahadillahu fala mudillah, famanyuddul fala hadiyala wa asshahu’alla’ila’ha’illalahu wahdahu lasheri kallah, wa asshahadu annamuhammadan abduhu warasulu.
Ya ayu allazina amanuttaƙullaha haƙƙa tuƙatil wala ta mutunna illah wa antum muslimun ya ayu hannasu taƙu rabbakum.
Kalakum min nafsin wahida, wa kalaƙa minha zaujaha wa bassa minhuma rijalan khasiran wa nisa’ah wattaƙullah lazitasa’aluna bihi, wal’arhama innallaha kana alaikum raƙiba, ya haiyu allazina amanutaƙullah wa ƙulu ƙaulan sadidah yuslahlakum amalakum wayagfirlakum zunuba kum, waman yuɗillah wara sulahu, faƙadfaza fauzan azeema ambaduhu fa inna’asdaƙal hadisi kitabullah wa’ahsanal hadi hadiyu Muhammadin (S.A.W) wa sharal umuri muhdasatuha fa innakulla mudasatin bidi’a wa kulla bidi’atin balala wa kulla balaltun finnar.”
Nufamshi ya sauƙe mai ɗan nauyi sabida jan dogon numfashin da yayi, kana ya kalli taron al’ummar musulmi dake zaune gabanshi manya da yara, masallacin yayi maƙil har woje.
Kusan gaba ɗaya taron jamar suka haɗa baki wurin cewa.
“Wa alaikassalam warahmatullahi wa barka tuhu”.
Kanshi ya ɗan rusunar tare da ci gaba.
Gyara masaƙalin abin sautin mgnar dake wuyan al’kyabbar jikinshi yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah. Kamar yadda aka saba haɗuwa a wannan masalaci mai Al’barka bana kuma Allah ya ƙaddara dani za’ayi.
Kamar yadda aka fara a wancan shekarar, zan ɗaura a kan darasin da Malam Abubakar ya fara, duba da kasantuwar mafiya yawa yan kasuwa ne, to zamuyi maudu’in bisa haƙƙin tauye mudu, da kuma barin salla ta wuce dan gudun cinikayya ya wuce ka.”
Daga nan ya shiga cikin shirin gadan-gadan.
Yayinda gaba ɗaya mutane sukayi tsit suna jin nasiharsa da hujjoji da yake jawowa daga al’ƙur’ani zuwa ahadisai, yana shigarsu yana ratsa musu jiki, jini, da zuciya.
Musamman dama mutane nason wa’azinshi.
Haka yasa koda lokacin tashi yayi sai suka ga kamar miti biyar sukayi ba awa ɗaya ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button